Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

a cikin jikinsa, da yanda damuwa a kulawa suka bayyana ƙarara a cikin muryarsa, abun ya burgeta ya kuma bata mamaki, ba ta taɓa ɗaukan cewa Kuliya na ɗaya daga cikin irin waɗanan mutanen ba. Kuliya ya juyo ya kalli side ɗinta a hankali, akwai wani abu da yake buƙata a tare da ita, ba komai ba ne face son sanin alaƙarta da wannan me kama da shi ɗin, ya na son ya san inda ta san yarinyar, amma idan ya tambayeta kai tsaye ba lalle ta ba shi amasa ba, ya zama dole ya yi taka tsan-tsan wurin samun bayanen da yake buƙata a wurinta. “Wani irin ciwo ne ke damunki?” Tambayar ta fito daga bakinsa, bayan ta ratsa ta tsakanin mayaƙan dake san hanata fita daga bakin nasa. A hankali Mishal ta juyo da dubanta gare shi, kafin ta juya ta ci gaba da kallon windown, sannan muryarta ta fito a hankali cikin shirun motar. “Hysteria!... na gamu da ita ne sakamako wani bad memory da na taɓa samu” Sai ya yi shiru ya na san ganr inda kalaman nata suka dosa, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, yayin da yake juya kan motar zuwa wata kwana. “Wani bad memory kika samu haka?” A wannan karon shi kansa sai da ya jinjinawa kansa na iya jefo mata tambayar, don shi ba ya surutai barkatai irin haka, idan ka ga hirsara da mutum na tsayi to a kan aikinsa ne, bayan nan kuma ba ya wata doguwar hira da kowa sai da Anna, ita ma sai su shafe tsawon wattani ba'a samu hakan ba. “Wani cousin brotherna ne, ya... Yi attempting min... Fyaɗe!...” Duk da ita yarinya ce ta san cewa sam kalmar 'Fyaɗen' ba ta da daɗin saurare, musamman ma ace miji za'a faɗawa faruwarsa a kan matarsa, abun akwai ƙona rai. Kuma sai da ta lura kamar kan motar na shirin ƙwacewa daga haannunsa, kafin ya seta kan motar da ƙyar, ya juyo ya kalleta na wasu 'yan sakkani, amma kuma ya kasa cewa komai. “A lokacin mun je hutu Maiduguri hutun Sallah... Sai ɗaya daga cikin cousins ɗina ya aike ni ɗakinsa, kasancewar tare suke kwana da shi Yazid ɗin ya sa a sanda na shiga ɗakin na gashin kwance a kan gado... Ban masa magana ba, dan da ma can Allah bai haɗa jinina da nasa ba, na nufi lokar Mu'ammar, wato shi wanda ya aikeni ɗin... Ban za ta ba na ji ya tura ƙofar ɗakin... Na tsorata amma ban nuna masa tsoron ba, na dake har na ɗauki abun da na zo dominsa, a sanda na juya sai na iske shi tsaye a jikin ƙofar... Ban ƙara masa kalo na biyu ba na nufi ƙofar dan na fita, ina zuwa kusa da shi ya kamo tsintsiyar hannun, ya finciko ni da ƙarfi zuwa baya... Ba shiri na faɗa kan gadonsa, ni kuma sai na shiga ƙoƙarin tashi, a lokacin ne ya daka min wata tsawa da har na koma ga Ubangijina ba zan manta da ita ba. A kan idona ya shiga cire kayan jikinsa. Ba ni da tsoro amma na tsorata a lokacin, ban ankara ba har ya iyo kaina ya danne ni, kuma cikin ikon Allah sai aka bankaɗo ƙofar daga waje. Aki Abubakar da Aki Arman suka shigo ɗakin, ganin na jima ban dawo ba ya sa suka biyo baya na. Ko a sanda aka fita da ni daga ɗakin ba na hayyacina. Tun daga lokacin na gamu da Hysterianan!” A lokacin da ta kai ƙarshen maganar hawaye har ya wanke mata fuska,duk da ita ba ta gama mallakar hankalin ba, amma tasan ciwon kanta, mace ta zauna ta na baka labarin yanda aka haike mata ba ƙaramin abun baƙinciki ba ne. Kuma ita kanta ba ta ce ga dalilin da yasa take ba shi labarin ba, wata ƙila don zuciyarta na faɗa mata cewar a yanzu shi ne gatanta, ba ta da wani gata nan duniya bayan shi, tun da ba ta da uwa, ba uba, ba ɗan uwa. Tun da ta fara bawa Kuliya labarin wani abu me kama da mashin ɗin yankan katako yake dagargaza zuciyarsa, ji yake ina ma ya na da damar da zai iya ganin bayan wannan mutumin, ko a baki ya tsani kalmar, bare kuma a ce matarsa aka yi kokarin aikatawa hakan. “Wani hukunci aka ɗauka a kansa?” Ya zaɓi da ya tambayeta ko zai ji salama game da yanda zuciyarsa ke masa zugi, ji yake kamar ya kurma ihu, ko raɗaɗin tsagewar zuciyar tasa zai ragu. Mishal ta share hawayenta da gefen gyalenta. “Cewa suka yi ai abun na gida ne, dan haka sai dai ayi haƙuri. Wani abun takaicin ma shi ne; kakarmu Jadda ita ce tace babu wani wanda ya isa ya taɓa mata jika, kamar ni ɗin ba 'ya ba ce, ko wata ƙila dan ba ni da iyaye a raye ne, kullum ba ta da abun faɗi da ya wuce tana sanmu, amma ni sam ba na ganin son!...” Ta ƙarshe tana sakin kuka me sauti a hankali. Ashe kallon kitse Kuliya yakewa rogo, wasu abubuwan idan ta yi sai ka ce 'yar shekara 10 ce, amma idan ta yi wani abun kuma sai ka zaci ta kai 20, wani lokacin yarinta ce fal a zancenta, wani lokacin kuma sai ta yi maganar hankali, kamar ba daga bakinta take fita ba, hannunsa yasa a cikin aljihunsa, ya zaro mata hanki, sannan ya miƙa mata. Mishal ta karɓa tana share hawayenta. “Wannan na ɗaya daga cikin matsalolin societynmu. Sai ki ga mutum ya aikata laifi, amma a ƙi ɗaukar mataki a kai, saboda ana ganin me laifin na gida ne, idan aka ɗaga maganar zumunci zai iya rabuwa. Wannan zai bawa me laifin damar ci gaba da aikata laifukansa yana fakewa da kasancewarsa na gida. Haka abun zai ci gaba da ƙaruwa kamar wutar daji” Cewar Kuliya. Mishal ta juyo ta kalleshi, ita kam yau ya na bata mamaki, bata taɓa ɗaukar cewar yana magana cikin sanyi irin haka ba, kuma ta ɗauka cewar maganganunsa basu da tsayi kamar yanda ta saba jinsu daga bakinsa, amma yau da banbanci. * “Maraba Lale!” Cewar Anna a sanda suka iso gidanta, tsaye take daga cikin falonta tana ta zabga murmushi, ta kasa gaskata abun da idonta ke gane mata, wai yau ita ce take ganin matar Aliyunta?. Suna ƙarasa shigowa cikin falon ta kama haannun Mishal ta zaunar da ita a kam kujera, sannan suka gaisa, fara'ar matar ya sa Mishal sakewa da ita. “Ni ce surukar ki 'yata, fatan ba za ki riƙa min ɗanyen tuwo ba” Anna ta faɗi tana dariya, hakan ya sa Mishal ma yin dariya, banda Kuliya da ya haɗa girar sama da ta ƙasa, kamar baƙin hadarin dake shirin zubar da ruwa, don shi bai ga wani abun dariya a maganar ba. “Kenan ke ce mamarsa?” Ta tamabaya tana kallon Kuliya. Anna ta gyaɗa mata kai. “Ni ce nan mamarsa” Mishal na murmushi ta ci gaba da ƙarewa fuskar Anna kallo, wai ko za ta tsinto wani abu guda da ya haɗa kamarta da ta Kuliyan. amma har ta gama yawo da idonta a kan fuskar Annan ba ta gani ba. “Sunana Anna.

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112