Skip to content

Chapter 59

Chapter 59

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

kalama da rabonsa da ya furtasu ga kowa tun bayan ranar da ya taso daga asibiti, bayan nan kuma ba zai iya tuna rabonsa da furtasu ba. Cike da mamaki Mishal ta cire hannunta a baki ta juyo ta kalleshi, ba ta san shi sosai ba, amma tana da tabbacin ba saba faɗar kalaman ya yi ba, yadda suka fito daga kan harshensa ne ya sa ta tabbatar da hakan, sai kuma inkiyarta da ya kira, da idan zai ma ta magana sai dai ya ce Hafsat, amma yau Mishal yace, ga kuma kunnuwansa da ya riƙe. Sai ya zamemata kamar wani maraya “Raina ne a ɓace, ni kuma ba na san a min magana idan raina ya ɓaci” Kuliya ya faɗi yana ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, Mishal ta juyar da kanta gefe, ta na ci gaba da kallon farin wata, kafin muryarta ta fito. “Hargagi da ɗaga murya ba ya saka mutum ya huce haushi, sannan ba ya maganin ɓacin rai” Kuliya ya ci gaba da kallonta ya na mamakin hankalin da ya ga ta yi a yau, kamar ba wannan mashiririciyar ba. “Me zan yi dan raina ya huce?” Mishal ta juyo ta kalleshi, jin yanda amon muryarsa ya fito a sanyaye. Ba tare da tace masa komai ba, ta miƙe ta zagaya ta bayansa, shi ya ɗauka ma cikin ɗakin za ta koma, be za ta ba ya ji sauƙar hannayenta a kan kafaɗunsa duka biyu, dai-dai doron wuyansa, hakan ya sa ya lumshe idonsa a hankali, don sauƙar hannun nata a kan jikinsa ya sauƙar masa da wani yanayi mara fasaltuwa. A hankali Mishal ta shiga matsa gurin tana masa tausa, idonsa a lumshe ya ɗaga kannsa sama, hakan ya sa kansa ya karu da jikinta, ita ma idon nata ta lumshe, dan ta ji sak wannan yanayin da ta taɓa ji a sanda ya rungumeta. Ci gaba ta yi da masa tausar, kafin muryarta ta fito a hankali, kuma har lokacin idonta a lumshe yake, kamar yanda nasa suke a lumshe. “A duk sanda za ka yi fushi. To wannan kake buƙata!” Kafaɗar tasa ya motsa, hakan yasa ta buɗe idonta. “Shin za ki kasance tare da ni a duk sanda zan yi gushi?” Wani abu me kama da farin ciki ya motsa a ƙirjin Mishal. Hakan ya sa ta kuma lumshe idonta tana danna masa kafaɗar. “Insha-Allah” Allah ne kaɗai ya san yanda abun da take masa yake sanyaya zuciyarsa, ya ji duk wata damuwa da ɓacin ransa sun bi iska. A hankali ya buɗe idonsa, sannan ya janye kansa daga jikinta, hakan yasa ita ma ta buɗe idonta, sai ta ga ya na janyowa littafinta. A kan idonta ya buɗe littafin, sannan ya tsaya nazartar problem ɗin, kafin ya shiga mata solving. Cikin abun da bai fi minti uku ba, ya gama mata, kuma har lokacin tana masa tausar. “Nagode” Ta faɗi a saitin kunnensa, ya ɗaga hannunsa na dama ya ɗora a kan nata dake kan kafaɗarsa. Hakan ya sa Mishal jin wani abu me kama da shock ɗin wutar nepa ya ratsa fatar hannunta. “You are welcome!” *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja* *10:00 PM* RAJA POV. “Zaid” Rhoda ta kira sunansa, hakan ya sa ya ɗaga haɓarsa daga hannunsa da ya yi tagumi, ya juyo ya kalleta, zaune yake a kan kujerar dake ɗakinsa, gaba ɗaya tunani ya hana shi sukuni, ya kasa gane abun da ya kamata ya yi. Kallon Rhodan ya yi na 'yan wasu sakkani, sanye take da pyjamas iri na jikinsa, hannunta a dama riƙe da trayn abinci. Sai kuma ya juya ya ci gaba da kalon ƙofar bathroom, kamar me jiran fitowar wani daga ciki. Rhoda ta girgiza kanta ta tako har gabansa, zama ta yi a kusa da shi, sannan ta aje taryn hannunta a kan coffee table, ta dafa kafarsa ta dama tana kallon gefen fuskarsa. “Me cece damuwar?” Hannunsa ya sa ya shafa gaba ɗayan fuskarsa, sannan ya sosa kansa. “Wani tunani kike ga Ammata za ta yi a kaina?” Rhoda ta yi murmushi. “Dude! Babu macen da ta isa ta ce bata sanka, baka da wani aibu, look at your self Bro, you are dazzling, smart, athletic, stylish, chaming and elegant!” “Ummm!, Yaushe ƙanwata ta girma haka?” Ya tamabaya yana wani murmushi ɗan guntun murmushi, Rhoda ta yi murmushi tana kwantar da kanta a kafaɗarsa. Sun ɗan ɗau lokaci a haka, kafin ta ɗago da kanta ta na ɗaukar trayn dake ɗauke da abinci. “Yanzu dai ka ci abinci” Ita da kanta ta shiga bashi a baki yana ci, don zuwan nata ya sauƙa-ƙa masa ruhi, saɓanin da da komai ya jagule masa. Maganarta ta ba shi ƙwarin gwiwa sosai, kuma ya ji cewar tabbas, babu abin da zai hana rabi'a ta so shi. *Brickhall school, Kaura District, Abuja* RABI'A POV. “...Seesee!” Mishal ta kirata, ganin gaba ɗaya hankalinta ba ya kanta, tun ɗazu take ta famar mata hira, amma ba ta amsa mata, hakan ne ya ankarar da ita cewar Adawiyyan ba ta cikin hayyacinta. Firgi-git Rabi ta kalleta. “Ummm” Ta amsa tana kallon Mishal ɗin, Mishal ta kalleta cikin nazari. “Ba ki da lafiya ne?” Rabi'a ta girgiza kanta. “Lafiya ta ƙalau.Tun rannan na ce miki ki riƙa ɗaura ɗankwali ko hula. Me ya sa bakya sakawa?” Ta faɗi cikin son bagarar da wancan zancen, don Mishal ba za ta iya mata maganin damuwar da take ciki ba, ga shi yau monday, tarradaddinta shi ne yanda za ayi ta haɗu da Raja, ta na son ganinsa, amma kuma wani ɓangare na zuciyarta ba ya maraba da hakan. Da yake ita ma Mishal ɗin wasu lokutan ba wayo ta ci ka ba, sai ta shafa kanta, ta na sinne kan cikin alamun rashin gaskiya, saboda tun rannan Anti Adawiyyan ta ce mata ta riƙa saka hula ko ɗankwali, don a yanzu ta zama matar aure, kuma sai ba ta yi hakan ba. “Na zo da hular fa. Ba ri na saka” Ta faɗi ta na jan jakarta, tare da buɗeta, wata baƙar hular sanyi ta fitar daga cikin jakar, sannan ta saka a kanta. “Ko ke fa, ai kin fi kyau a haka” Mishal ta ɗan yi murmushi. “Kowa a class ɗinmu ya na ta magana a kan ball ɗin da kuka yi rannan, yaushe za ku sake?” Rabi ta ɗan yi murmushi, don ta ɗan fara samun sauƙi a ranta. “Duk sanda kuka saka rana, amma ban da yau” Daga haka suka shiga hirar ball, kafin ɗaya daga cikin masu aikin shara a makarantar ta zo kiran Rabi'a, kan ta zo za ta yi aiki a ɓangaren kwanan ɗalibai. Wai hausawa suka ce rashin sani ya fi dare duhu, domin da ace ta san abun da zai iya faruwa a wannan tafiyar tata, da ba ta fara ba, domin babbar ƙaddarar rayuwata ta faru ne ta sanadiyyar wannan aikin da aka sakata a wannan lokacin. Haka suka yi sallama, Rabi ta tafi ɓangaren kwanan ɗaliban ta fara aikin sharar, aikin yau har ya fi na kullum, don ba ita ta gama ba sai wajejen ƙarfe 5, kuma bayan ta gama da can ta dawo ɓangaren ajujuwa, zuwa lokacin an jima da tashi, haka ta bi aji bayan

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112