Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

bayyana a bayan ƙofar. Kallo ɗaya Kuliya ya masa ya ɗauke kai, tare da ci gaba da danna laptop ɗin gabansa. “Barka da safiya..... ni na gaida ka, tun da kai ba za ka iya ba gaisheni ba” Abubakar ɗin ya faɗi yana ƙarasowa cikin office ɗin. har ya zauna a kujerar dake tsallaken teburin Kuliyan bai masa magana ba. “Me yasa yau ka makara ?” Muryar Kuliyan ta tambaya bayan wani lokaci, ba tare da ya kalli Abubakar ɗin ba. muryar tasa kamar da ga sama. Sannan amonta ya fito kamar kullum, cikin ɗaci da alamun ɓacin rai. Dan shi kullum ba'a rasa abinda yake ɓata masa rai. Abubakar ya yi murmushi, to shi ya zai yi ne?, tun da Allah ya haɗa shi zama da mutane biyu masu murɗaɗɗen hali, tsakanin Kuliya da ƙanwarsa Misha!, Ya rasa wannene ya fi wani murɗewar hali. “Ƙanwarka ce, ta yi rashin jin da ta saba a makaranta, sai da na biya ta can, sannan na ƙaraso nan” Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Shi duka-duka sau ɗaya ya taɓa ganin ƙanwar Abubakar ɗin, ba ma sosai yake iya tuna lokacin ba, dan shekarun da ɗan dama. “Dama autopsy results ɗin nan na zo karɓa, Kamis yace yana wurin ka” Ba tare da Kuliyan ya kalle shi ba, ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, sannan ya buɗe wata loka dake jikin teburin nasa, ya ɗauko file ɗin,ya miƙa masa. Abubakar ya karɓa yana miƙewa tsaye. “Na tafi...” Ko kallonsa Kuliya bai yi ba, bare ya bashi amsa, kuma shi ma yasan ba lalle ya kalle shin ba. Yasan halin Kuliyan sarai. Har faɗi yake da bakinsa cewa; idan ba Abubakar ɗin ba babu me iya zama da shi a matsayin aboki. Dan kaf duniyar nan Abubakar ɗin ne kaɗai abokinsa, ba shi da wani aboki da ya wuce shi, sai Sharon da suke ɗan jitiwa, ita ma kuma ba kullum ba. *Badawa layout, Kano....* RAJA POV. “Raja dan Allah, dan Allah!.....” Cewar wani mutumi a galaɓaice, yayin da yake durƙeshe a gaban Rajan. Kuma bai ko gama rufe bakinsa ba, Rajan ya ƙara tsinduma kansa cikin bahon dake aje a gabansa, wanda yake cike taf da ruwa. Haka mutumin ya yi ta motsi da kansa a cikin ruwan, saboda azabar da yake ji. Zaune yuke a harabar gidansa. Yayin da Rhoda da su Zuzu ke tsaye a bayansa. Waɗanan lumssassun idanun nasa na kallon mutumin da kansa ke fancal-fancal cikin ruwan sanyin. wannan innocent face ɗin nasa fayau!, banu wani abu da za ka iya tsinta a cikinta. Kai ba ka ce mamallakinta ne ke wannan aikin ba. Ƙarar ringing tone ne ya karaɗe wurin. A hankali Rhoda ta duba screen ɗin wayar 'Oga Garuje', shine abun da ta ga an rubuta, dan haka da sauri ta ƙarasa kusa da Raja. “Garuje ne ya ke kira” Bai kalleta ba, sai ma bindigarsa ƙirar pistol da ya ɗora a kan fuskar mutumin da ya tsamo kansa daga cikin ruwan. Sannan wannan kamillar muryar tasa ta furta. “Me yasa ka ci amanar mu?” A nitse muryar tasa ta fito, cikin wannan sautin nata mai nuna tsantsar innocent ɗinsa. “Dan Allah Raja....Dan Allah...” Ji kake Tas!!. Ƙarar bindiga ya karaɗe harabar gidan. Me gadin gidan ya yi saurin faɗawa ɗakinsa. Duk da yasan cewa abun ba zai komo kansa ba. Amma wai me hausawa suka ce ne?, idan ka ga gemun ɗan uwanka ya kama da wuta, to ka shafawa naka ruwa. Raja ya yi wani murmushi me kama da dariya, a sanda ya ga shigewar me gadin nasa. Kafin ya saki gawar mutumin nan da ya harba a ka. Jini har ya ɓata masa hannu. Ba tare da nuna damuwa ko wani tashin hankali ba, ya sunkuya ya wanke hannunsa cikin ruwan bahon nan. Kuma har zuwa lokacin wayar tasa na riging a karo na barkatai. “Ina ji” Nutsatsiyar muryarsa ta faɗi,bayan ya amsa wayar, cikin wannan kamala da kamewar tasa, kai ba ka ce shi ne ya kashe rai yanzu ba. “Raja!, Oga ne da kansa ya yi waya, ya ce ya na buƙatar ka je ka same shi a Abuja....” Raja zai iya rantsewa kan zuciyarsa sai da ta buga sau biyu a lokaci guda. Kenan tsawon shekarun da ya kwashe yana wannan aikin sun kusa ƙarewa?. Shekaru sama da uku ma rayuwarsa ya kwashe yana bautar da bai san ranar ƙarewarta ba. Sai a yau ne komai ya ke gaɓa. Komai ya ɗauko hanyar ƙarewa. Ya kawo inda ya ke matuƙar burin kaiwa. Sai dai a yanayin fuskarsa ba za ka tsinci hakan ba, dan miƙewa tsaye kawai ya yi, sannan ya juya yana kallon su Rhoda. Da waɗanan lumsassun idanuwan nasa, ƙwayar idon wadda ta kasan ce gray color tana kallon yanda su Zuzu ke magana ƙasa-ƙasa. Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce. “Yaushe kenan ?” “Ko zuwa nan da sati ɗaya ne, dan da alama ka koma can da zama, ka ga kenan sai an nema muku gidan da zaku zauna, da dai sauran su...” “Na fahimta!” Kuma da ga haka ya tsinke wayar. “Alandi, Zuzu, ku fita da gawar nan da ga gidan....” “An gama Oga Raja!” Suka faɗi suna yin wurin da gawar ke yashe. Sannan shi kuma ya yi hanyar shiga cikin gidan, da hannu ya yiwa Rhoda alamu da ta biyo shi. “Rhoda, mun kai ga gaci....” Wannan salihar muryar ta faɗi a sanda suke zaune a falon gidan. ”Me ya faru?” Rhoda ta tambaya. “Alhaji Bala ne da kansa ya ce na je na same shi a Abuja” Cike da mamaki, murna da kuma farin ciki take kallonsa. “Kenan mun kusa zuwa ƙarshe?” Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce. “Kusan zan iya cewa hakan” “Kai amma fa na yi farin ciki...” Ta faɗi da iyakar gaskiyarta, dan ta yi farin cikin, tana ganin kamar komai ya kusa ƙarewa, kamar an gama komai, kamar wannan wahalar da suka sha tsawon shekaru ta ƙare. Kuma ba ita kaɗai ke wannan tunanin ba, shi ma kansa Rajan haka yake tunanin sun kammalla komai, komai ya zo gangara, gangarar da zata gangaro da ƙarshen wahalar da suka sha tsawon shekaru..... Sai dai abinda bai sani ba shi ne; yanzu ne ma komai ya fara, a yanzu LABARIN zai soma, sai a yanzu ne babin ƙaddarar tasa zai buɗe. Wani sabon babi fil!, wanda babu ɗigo ko ɗaya a ciki, sai na wanda ubangiji zai hukunta. Saboda wata ƙaddara da ke shirin faruwa 'yan kwanaki masu zuwa. Ƙaddarar da zata tarwatsa komai, ta kuma gyara wasu lamuran. A dai-dai lokacin ƙofar falon ta buɗe, Jagwado ne ya shigo, dan da ma banda shi aka tafi yasar da gawar. Lighter ce riƙe a hannunsa yana ƙyasta ta, yayin da sigari ke maƙale a bakin. A sa'ar da Raja ya ɗora idonsa a kan wutar, a lokacin ne kuma wannan tsoron ya shige shi, tsoron wuta da Allah ya saka masa tun bayan abinda ya faru da shi. Baya san ganin wuta sam, domin wuta na ɗaya daga cikin abin da ta zama silar rabuwarsa da mutane uku da suka fi soyiwa a ransa. Da farko ta raba shi da mahaifiyarsa, sai kuma ta zo ta raba shi

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112