Skip to content

Chapter 40

Chapter 40

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

ɗin, duk da fuskarta a rufe take da gyale. Har suka ƙaraso inda yake ya na kallonsu, ɗaya daga cikin sojojin ne yace ya buɗe musu booth, bai musa ba ya buɗe, suka saka akwatunan a ciki. Dai-dai da lokacin da mata nan biyu suka saka Mushal a cikin motar tasa a seat ɗin gaba. Ɗaya daga cikin matan ce ya fusaknci cewa babbace, don ga shekarunta nan sun bayyana hakan, kuma sai yake ga kamar ma yasan fuskarta. Gaishe da ita ya yi cike da girmamawa. “Kai ne Aliyu right? ” Sai ya gyaɗa mata kai idonsa a ƙasa. “Ba ka gane ni ba ko?” Sai ya gyaɗa kansa yana ɗaga kafaɗa, don ya kasa ganotan. “Mun taɓa haɗuwa sau ɗaya, General Adamu Nimra Arab” Take fuskarta a ranar da suka fara haɗuwa ta dawo masa, tabbas ita ce, ita ce matar da ta babshi award a wani taron karramawa da ya taɓa zuwa. “Ni uwa ce, kuma yaya a wurin Mishal, ba sai na zauna na maka dogon bayani ba, nasan ka mallaki hankalin kanka, ka kuma san hakkin mata a kan mijinta, na kuma san da ka san hakkin Maraya, don haka sai ka kiyaye!” Maganganun nata ba su da yawa, amma baƙaramin taɓa shi suka yi ba, shi kuwa ya san maraici, ai yana jin babu wanda zai bada labarin maraici sama da shi... RAJA POV. Zane yake a kan kujerar dake facing Alhaji Bala, wanda ya buɗe akwatin dake cike da hodar ibilis, wadda su Rajan suka ƙwato masa a hannun waɗanda sukai haɗa kasuwanci da su. da ma haka Alhaji Bala ya saba saka su aiwatarwa tun suna garin kano. Sai ya yi yarjejeniya da dilolin cocaine, kan yana so a kawo masa zai biya kuɗin, sai kuma ya tura 'yan daba karɓar kayan, idan waɗanda aka aiko da kayan ba su yi gardamar hana kayan ba, 'yan dabar Alhaji Bala za su karɓi kayan salin alin, idan kuma waɗanda aka aiko da kayan sun yi gardama, 'yan dabar Alhaji Bala za su kashesu su ƙwaci kayan. Fuskar Alhaji Balan, ɗauke take da wani irin yanayi, wanda yake cakuɗee da farin ciki da kuma mamaki, tun da ya fara safarar hodar ibilis, bai taɓa yin wadda ta kai wannan yawa ba. Kuma masu kayan suna da matuƙar haɗari, bai ɗauka cewar su Rajan za su iya ƙwato kayan cikin sauƙi kamar haka ba, wannan aikin da suka masa yasa ya ƙara basu matsayi me girma a cikin zuciyarsa, tare da ɗaura niyyar ɗorasu a kan sauran harkokinsa, zai buɗe musu cikinsa, ya faɗa musu sauran ayyukansa da ya saba yi, don su taya shi ya tara kuɗin da yake buƙata, wajen yin campaign ɗin takararsa. “Da kyau Zaki, aikinki na kyau! Na ji daɗin wannan aikin, Dan haka zan ƙara baku wani aikin!” Kusan a tare Raja da Rhoda suka kalli juna, a cikin idon Raja roda ta hango 'Ba na faɗa miki ba?', ita ma ta idon nata ta mayar masa da 'Na gani'. Sai kuma suka juya dubansu kan Alhaji Bala dake ta washe baki. Raja ya ɗaga kafaɗa yana faɗin. “Wani aiki ne wannan ?” “Safarar makamai!” RABI'A POV. Zaune suke ita da Zara a tsakar gida, yayin da Habiba da Mama ke ɗaki suna ƙus-ƙus ɗin da suka san na miye, wai yau suke faɗin Maman za ta yi tafiyar, kuma tun safe suke ta shirye-shirye. Anti Saratu kuma na banɗaki tana wanka, Fatima da Mahmud kuma basa ma gidan. Fitowar Mama da Habiban ce tasa su dakatawa da hirar da suke, a tare suka kallesu. “Allah ya tsare Mamana, Allah kare min ke gabanki da bayanki, Allah ya kauda idon maƙiya a kanki!...” Haka Habiba ke ta faɗi har Maman ta sa kai za ta fita. A lokacin Saratu ta fito daga banɗaki, kallonsa kawai ta yi, ta kama hanyar ɗaki cike da takaici. Daga Mama har Habiba bin bayanta suka yi da harara. Har waje Habiba ta bi Mama tana ta mata addu'a. Kuma kafin ta dawo ne Anti Saratu dake ɗaki ta ƙwallawa Rabi kira. “Gani Anti Saratu!...” Rabin ta faɗi a sanda ta shiga ɗakin , ta iske Anti Saratu zaune a bakin gado tana shafa mai. “Awara za ki siyomin” “To kawo... Ki ban ɗari biyar a cikin kuɗina sai na ƙaro mana da kifi” “To” Anti Saratu ta amsa tana miƙewa, tare da nufar jakarta inda take aje kuɗi, kuɗin ta shiga lalubowa, kuma kafin ta gama lalubo kuɗin, wani yaro ya rangaɗa sallama daga bakin ƙofa, Zara dake tsakar gida ce ta amsa masa, abinda ya fito daga bakin yaron ne ya sanya duniyar Anti Saratu da ta Rabi girgiza, don abu ne da ba su taɓa zato na, wani abu da kaf tsawon zaman Rabi a gidan ba ta taɓa gani ko jinsa ba. “Wai saratu ta zo in ji Fu'ad!” Abun kamar mafarki, abun kamar wasa, wai yau wani ne ke sallama da Anti Saratu, wani abu sabo, wani abu da bai taɓa faruwa a tarihinta ba, ko da wasa ba ta taɓa yin saurayi ba, tun tasowarta babu wanda ya taɓa cewa yana sonta da soyyaya. Ko dan Allah maji roƙon bayinsa ne, kuma ma an ce wai haƙuri me tadda rabo. *No.181, Guzape, Abuja...* MISHAL POV. Zaune take a bakin gadon da a yanzu yake amsa sunan nata. Ita fa har yanzu ba ta ganewa komai, ta kasa ganewa halin da take ciki, gani take kamar mafarki ne, kamar ba gaskiya ba ne, babu abun da ta yi kewa a gidansu sai Daala da kuma su Mama Ladi. A karo na barkatai ta ƙara kallon ɗakin, sannan ta ja guntun tsaki a ƙasan numfashinta, miƙewa tsaye ta yi a hankali, ita ba ta saba zaman ɗaki ba, dan haka ba za ta iya zama gu ɗaya ba. Shi ma wanda ke amsa suna mijin nata bayan ya kawota gidan ya ajiye , ba ta ƙara ganinsa ba, ga shi har kusan ƙarfe tara na dare. A ƙofar ɗakin nata ta tsaya, tana kallon corridorn dake ɗauke da ƙofofo uku, wanda take da tabbacin ɗakuna ne. Ba ta damu da buɗe ko da ƙofa ɗaya ba, ta ci gaba da takawa zuwa cikin falon, kasancewar gidan bungalow ne. A falo ta ci birki, ta shiga kalle-kalle, har idonta ya sauƙa a kan wata farar kyakkyawar mage, kwance a kan sofa. Ba ta san sanda murmushi ya suɓuce mata. Da sauri ta yi wurin magen ta na ɗaukarta, hakan ya sa magen ta farka, sosa jikin magen ta shiga yi ta na mata wasa kamar wadda ta samu ƙarimin yaro. Jin ana buɗe ƙofar shigowa falon ya sa ta ɗora magen a kanta ta kalli ƙofar, dai-dai da shigowar Kuliya, sanye cikin baƙaƙen ƙananun kaya. Kamar yanda take kallonsa haka shi ma yake kallonta. Sanye take cikin wani short trouser, wanda bai rufe gwiwarta ba, sai wata half vase da bata rufe duka cikinta ba, ta ɗora falmaran ɗin wandon a saman half vase ɗin, wadda take da ɗan tsa yi, ƙafafunta sanye cikin wasu pink fluffy sliders, gashin kanta fake cikin ponytail. Zuciyar Kuliya ta yi tsalle daga ma'ajiyarta, wani abu me kama da garwashi ya shiga bi ta kan

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112