Chapter 94
Chapter 94
tata!. Ɗan Lami ne ya fito daga ɗakinsa yana kallonsu su duka. Kansa ya girgiza cike da nadama, a sanda ya kalli Mama, ya tabbatar da koma miye ya samu 'ya'yansa shi ma akwai nasa sa hannun a ciki, shi ma ya bada gudunmawa ta musamman a lalacewar tarbiyyar yaran gidansa. A matsayinsa na uba, kamata ya yi a ce yana saka ido akan ko wace harka dake kai kawo a cikin gidansa, ya kamata ace shi ne tsaye a kan ko wata harka ta gidan, sannan nauyin ci, sha da suturarsu duka ya rataya a wuyansa ne, amma sai ya yi burus da su, ya kama wata hanya da ba ta haifar masa da ɗa ne ido ba. Zuwa yanzu ya yi nadamar abubuwa da dama da ya aikata a rayuwarsa, kuma hakan ya biyo baya ne, sakamakon nasihar da wannan matashin me kama da matarsa da kuma 'yarsa ya masa. Sosai matashin ya ja hankalinsa kan abubuwan da yake basu da kyau, kamata ya yi ace ya kama sana'a yana kula da gidansa da kansa, ba wai tsinduma cikin harkar caca da bin matan banza ba. Kuma matashin be sallame shi ba sai da ya danƙa masa jari me tsoka, ya shawarce shi da ya kama sana'a, sannan abun da yake ƙoƙarin yi kenan, don hatta da wannan ɗawainiyar asibitin na Mama shi ne a kai. Ya kuma hana habiba saida wannan finiason da take, duka nauyin gidan ya dawo kansa. “Sannu kin ji Mama!” Ya faɗi yana jan kujera tare da zama, shi ma kai ta gyaɗa tana kallonsa. Kamar daga sama suka ji sallamar wata murya me kama da ta Rabi'a. Cikin sauri su duka suka kalli ƙofar soron gidan. Ilai kuwa, Rabin suka gani ta shigo cikin gidan. Farin cikin ganin Rabi ya sa Saratu miƙewa da gudu ta yi kanta suka rungume juna. Tun daga Habiba, Mama, Ɗan Lami har da Zainab kallon sabuwar Rabin suke, ba wai ƙiba ta yi ba, don idan aka dangana da jikinta na da sai de ace ta rame, amma ta yi wani irin fari, ta ƙara haske, yanayin fatarta kawai zai sheda maka da irin sauyin rayuwar da ta samu. “Ina sirikin nawa?” Rabi ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta. “Yana waje” “To shigo mana, bari shi ma na masa iso” Sai a lokacin idon Rabi ya sauƙa a kansu sauran mutanen dake tsakar gidan, fuskar Ɗan Lami da ta kalla ce ta tuno mata da kashedinsa gareta, na kar ta ƙara dawowa gidansa, hakan ya sa fara'ar fuskarta ta ɗauke ɗip, sannan ta juya da sauri za ta bar gidan. “Tsaya Rabi'a” Tsayawar ta yi, saboda jin amon muryar mahaifinta, an ya kiwa yau ba mafarki take ido biyu ba?, to in ba haka ba, ita de tun tasowarta da mahaifinta, ba za ta iya cewa ga rana ɗaya da ta ji ya yi magana cikin nutsuwa kamar haka ba, an ya ma kuwa shi ne?. A hankali ta juyo ta kallesu, zuwa lokacin su duka sun miƙe tsaye, sai a yanzu ma ta lura da Mama wadda ke zaune a kan tabarma, ita sam ba ya ma ganeta ba, yanzu wannan Mama ce ta zama haka?, oh!, rayuwa kenan. Sai kuma Habiba, wadda ta rame, ga kuma tabbuna a jikinta ta ko ta ina. “Ki dawo Rabi, nan ɗin gidankimu ne” Zaune take a gefen Anti Saratu, yayin da Mama da Zainab ke zaune a kan tabarma, Habiba na kan kujera, haka ma Ɗan Lami, daga can gefe kan wata sabuwar sallaya kuma Zaid ne zaune, ya sunkuyar da kansa ƙasa. Ɗan Lami kallonsa kawai yake yana ƙarawa, ashe de wannan matashin sirikinsa ne?, ashe shi ne yake auren 'yarsa Rabi?!, Ashe e kuma shi ne jinin Rabi 'yar uwar Maryam, me sunan Rabi 'yarsa?. Allah kenan. Rabi ta share wata ƙwallar da ta silalo daga idonta, wai yau ita ce Abbansu da Habiba suke neman yafiyarta, ita kuwa me za ta iya cewa?. Ba ta da wani abun cewa face ta godewa Allah. “Na yafe muku Abba, muma Allah ya yafe mana” Ta furta muryarta a raunane. Habiba ma ta share hawaye tana saka mata albarka, Mama ma kallonta kawai take, tana san tace ita ma Rabin ta yafe mata, amma babu hali. *06:50 PM.* Sai a lokacin suka samu damar dawowa gida, Rabi ce a kan gaba, yayin da shi kuma Zaid ke biye da ita, ita ta buɗe ƙofar falon ta shiga, sannan shi ma ya shigo, tsayawa ya yi kukkuna fitilun falon dan babu haske sosai. Kuma fitilun ne suka haska masa ita tar, tsaye a tsakiyar falon tana dubansa, idanuwanta sun cika da ƙwalla. A hankali ya aje jakar kayanta data karɓo a gidansu. Kafin ya ƙara wani yinƙiro, Rabi'a ta tako ta rungime shi tana sakin kuka. “Na gode Raj, Na gode da duk wani abu da ka san ka taɓa min” Zaid ya yi murmushi yana shafa kanta. “Ammatan Raja babu komai fa, babban surprise na tafe nan da next week nan” Ba komai ta fahimta a kalaman nasa ba, amma ko ba komai sun mata daɗin sauraro, dan haka ta ƙara narkewa a jikinsa tana kukanta. *No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja.* MISHAL POV. Zaune take a falon Annan suna hira. Yau tun safe Kuliya ya kawota, tare da faɗa mata cewar bayan sallahr magrib zai dawo ya ɗauketa. Tana cikin farin ciki yau, dan sai da ya biya da ita gidan yayanta, suka gana da Daala da kuma su Baba Lami, duk da ba su tarar da matar gidan ba, a cewar Baba Lami wai ta fita unguwa ne. Da sallama aka turo ƙofar falon, hakan ya sa ita da Anna kallon ƙofar. Siyama ce ta shigo tana ɗan murmushi, sai de kuma cikin sakan ɗaya wannan murmushin ya ɓace daga fuskarta, sakamakon arba da Mishal da ta yi, saboda ba ta manta karonsa ba. “Ah-ah, Siyam, ƙaraso mana” Siyama ta haɗiyi miyau tana ƙarasowa cikin falon, gaba ɗaya yanayinta kaɗai zai fallasa sirrin zuciyarta. A ɗarare ta zauna kusa da Annan tana satar kallon Mishal wadda ke jifanta da murmushin ƙeta. “A... Anna ina yini” “Ke! Lafiyarki kuwa?” Siyama ta yi saurin girgiza kanta, sai kuma ta gyaɗa shi. Har wata zufa take don tashin hankali. “A'a Siyama, wannan yanayin naki ba lafiya ba, bari na samo miki wani abun sha” Annan ta faɗi tana miƙewa, tare da nufar hanyar kitchen, da sauri Siyama ta bi bayanta, don zama da Mishal inuwa ɗaya ba nata ba ne, Mishal ta wuce tunaninta, saboda haka gwara ta bar mata falon, kafin ta laƙa mata sharri kan tana shaƙar iskar da ta furzar. Mishal ta ƙara bajewa a kan kujera tana murmushi, saboda ta tuna abun da ya faru tsakaninta da su last time!. *** “Me kuke nema?” Muryar Mishal ta tambaya a waccan ranar, lokacin da Siyama da Karima suka shigo gidanta. “Rayuwarki muke nema!” Karima ta amsa mata a hassale tana shigowa cikin falon, duk da Mishal ta tsorota amma ba ta bayyana tsoronta ba, sai ta ɓoye kayanta a cikinta. “Me ya sa kuke neman rayuwata?” Ta tambaya tana sakin tsintaiyar hannunta. “Saboda kin shiga tsakanina da Kuliya, kin raba ni da Kuliya.Ni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112