Chapter 69
Chapter 69
hagu, yayin da Jagwado ya zauna a ƙasa ya na kallonsa, kai kace me shirin ɗaukan karatu ne, kansa ya juyo ya kallesu gaba ɗaya, sannan ya ɗauke kai ya ci gaba da kallon bishiyoyin. “Ka da ka damu Raj. Ka gane ko?. Rhoda ta ce eh... Za ta gano maka 'yar shilarka. Dan haka kawai ka share” Kalon Alandin dake wannan batun kawai ya yi, ya kuma ɗauke kai, shi da za su tashi su bar shi shi ɗaya ma da abun zai fi masa sauƙi, dan duniyar ma kanta ji yake kamar babu kowa sai shi kaɗai, kamar a duniyar babu wanda ya kai shi kaɗaici, kamar ma kwanakin ba sa sauri, gani yake kamar a jiya ne Rabi ta ganshi ya na harbin wannan mutumin. “Zaid!” Juyowa ya yi ya kalli Rhoda da ta kira sunansa. “Na ƙara tsananta bincike, ka roƙi Allah ya temakemu mu samota” A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya, kafin a hankali wani damshi ya sauƙo daga idonsa har zuwa ƙasan kuncinsa, wani abu ruwa, wani abu da ba zai iya tuna rabon da su fito daga idonsa ba, amma yau sai ga su a idonsa, yau shi ne yake hawaye saboda wani ɗan adam da ba Rhoda ba, a da ya ɗauka cewa duniyarsa ta mutu gaba ɗaya, bayan Rhoda ba shi da wani abun damuwa, ba shi da wani wanda yake damuwa da shi bayan ita, ba shi da wanda zai bawa kula sai ita, amma yau a kan Rabi sai ga shi ya na hawaye, hawayen da yake san ya yi su tsawon lokaci, amma ya na dannewa. Gaba ɗayansu suka ci gaba da kallonsa cike da tausayawa, don har wata rama ya yi, ga ɗan duhu da faratrsa ta yi, tsabar tashin hankali, saboda shi gani yake koma miye ya samu Rabi'a shi ne sila. Rhoda ta dafa shi, kuma kafin ta faɗi abun da ke bakinta ya kwanta a jikinta ya na rungumarta, tare da sakin kuka a hankali, kuka yake sosai, amma kuma ba sauti, sai jijjigar da jikinsa ke yi tare da na Rhoda da ya runguma. Rhoda da jikinta ya yi sanyi, ta shafa kansa ita ma hawayen na sauƙo mata, tun suna yara sun riga da sun saba da ko kuka tare suke yi, hakan ya sa za ta taya shi jimamin halin da yake ciki. Su Alandi ma gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyi ƙalau, kamar wanda suka kwana a cikin fridge. “Rhoda ki temaka ki nemota.... Rhoda ba zan iya ɗaukar wannan ciwon ba, ba zan iya ba!” Cikin muryar kuka ya yi furicin kuma a lokaci guda ya na sakin Rhodan, Rhoda ta shafa sumar kansa ta na girgiza masa kai. “Na maka alƙawarin samo maka ita, ko ina ta shiga a garin Abuja, ka yarda da ƙanwarka ko?” Ya gyaɗa mata kai. “To ƙanwarka ba za ta barka ka faɗi ƙasa ba. Zan tabbatar da na nemo maka ita a ko ina take kuwa” Ƙara rungumarta ya yi ya na sakin wani kukan. “Rhoda Ina san Ammata, ina santa... Ina santa..... I na... I na.... Santa!” Rhoda ta shafa bayansa tana gyaɗa masa kai. “Na sani, na san ka na santa, kuma za ka aureta, da yardar yesu zaka aureta!” *No.181, Guzape, Abuja* *10:04pm* KULIYA POV. A hankali hannunsa ya tura ƙofar shiga falon gidan zuwa ciki, sai da ƙofar ta buɗe gaba ɗaya, sannan ya saka ƙafafunsa ciki, shiga ya yi ya na baza idanuwansa a falon a yunkurinsa na neman ta inda zai hangota, idan ma ta na falon kenan. A kan kujera 3 seeter ya hangota, ta yi rashe-rashe ta na bacci, ganinta kawai da ya yi a yanzu ya tuna masa da safiyar yau, a lokacinda ya tsinci kansa cikin duniyarta, yanda ya sumbaceta a yau da safe ba ƙaramin saka shi cikin nishaɗi ya yi ba. Sai tunanin abun da ya katse masa nishaɗin safiyar ya dawo masa. Wannan maganar ta Ibrahim ce ta sa ya saki bakinta a hankali, sai dai kuma bai raba fuskarsa da tata ba, ya na kallon murfin idonta da ta lumshe, a hankali ya janye hannunsa dake kan ƙugunta ya kama fuskarta, sannan ya sumbaci gaban goshinta, kuma sumbatar ce ta sa ta buɗe idonta. “Ki je Ibrahim ya na jiranki” Ya furta mata a hankali, kuma ita ma sai ta gyaɗa masa kai kawai, ta na fita daga hannayensa, ta ɗauki lunchbox ɗinta za ta fiti ya kamo hannunta, sannan ya rungumeta sosai a jikinsa, yana jin yanda jikinta ya yi karkarwa a lokacin. Kafin ya saketa ya bata damar tafiya. Mamaki ne ya kama shi ganin maganin mura da na zazzaɓin da ya aiko mata ɗazu, hannunsa ya kai ya ɗaki kwalar maganin muran dake kan coffee table, idanuwansa a waje yake kallonta daga kwancen da take, ganin abun da ke cikin kwalbar saura rabi. Kenan duka ita ta shanye?, tab, ai dole ta yi bacci, rabin kwalba fa?, dariya ta kama shi, hannunsa ya kai ya ɗan taɓa fuskarta, amma kamar wanda ya taɓa gawa. Hannunsa ya kai ya kamota ya na zaunar da ita, hakan ya sa ta buɗe idonta a wahalce, ta kuma lumshe idon sannan ta buɗe. “K... kai... ka...” Abun da take faɗi kenan, Kuliya bai san sanda ya fashe da dariya ba, maye take tuburan a fili, yau in ba shirme irin na Mishal ba, kusan rabin kwalba fa ta sha?, gaba ɗaya ta kasa zama gu ɗaya, sai layi take tana daga zaunen, ga idonta da take buɗewa ya na lumshewa da kansa. “Tashi mu je na kaiki ɗaki...” Ya faɗi ya na gimtse dariyarsa, a lokaci guda kuma ya na kama kafaɗunta, amma sai ta sa ragowar ƙarfinta ta ture shi. “Kai... Ka... Ka rabu da ni... Ba... Ba ka san... S... San wa.. cece Mi... Mishal ba ko?...” Sai ta nuna kanta da ɗan yatsa. “Ni ce... Ce Hafsat... Haf... Hafsatun Aliyuu... hhhhhh!” Sai ta ƙarashe da dariya, ta guntule dariyar tana nuna shi. “Kai kuma... Wa... Waye kai?” Kuliya na murmushi yace. “Aliyun Hafsat” Sai ta ƙyasta hannunta. “Ka... ka ga mun yi ma... Match kenan... Amma me... Ne kake a nan?” Zama ya yi a kujerar yayin da take kallonsa da lumsassun idanuwanta. “Wata na zo nema...” Bai ko ƙarashe ba ta fashe da dariya. “Haka... Haka wani ma yace min a... A... A makarantarmu, wai... Wai shi ya na neman wani, amma kuma ni na san ni yake nema... Ni fa Cele... Cele ce a makarantar nan... Ko... Kowa ni yake san gani... Kai ma ka na san gani na ko ?” Ya gyaɗa mata kai, sai ita ma ta gyaɗa nata kan. “Amma kai... Be kamata ka... Ka ce kana so na ba” Kuliya na ɗora hannunsa na dama a kan bakinsa yace. “Amma me ya sa?” “Saboda ni matar aure ce, mijina sunansa Kuliya... Kuliya... Yaro idan ka shiga hannun Kuliya ko, hmmmm” Ya ƙara fashewa da wata dariyar. “Me ya sa kake.... Kake dariya irin haka?” “Ba dariya nake ba.... Kuka ne” Sai kuma ita ma ta fashe da kuka harda hawaye. “Yau ma yayata ba ta zo makaranta ba, ya... Yayata ta de... Dena sona, ba ta so... Sona... Kuliya ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112