Chapter 111
Chapter 111
shirin saka masa kuka, sai ya yi dariya yana ƙara kwantar da ita. “Ki yi haƙuri. Gaskiya ni me sa'a ne Ammata, a karon farko?” Kanta ta ƙara cusawa a ƙirjinsa dan tsabar kunya. “Diary baka da kunya” Muryarta ta fito daga ƙasan ƙirjinsa. Ya yi dariya. “Wallahi ji na nake kamar wani sabon mutum, ji nake kamar yau aka haifo ni, duka burikana ɗaya bayan ɗaya suna cika...” Ya faɗi a setin kunnenta. Sai ta ƙara narkewa a jikinsa tana lumshe ido. dan wani bacci da take ji na shirin kamata. KULIYA POV. Kwance yake a kan gadon marasa lafiya na asibti, yayin da Mishal ke kwance a gefensa, kallon fuskarta kawai yake, yana tuna yadda ta yi mirƙisisi kan ita ba za ta tafi gida ba, don ita tare da shi za ta kwana. Baccinta take hankali kwance, kamar tsimma a cikin randa. Juyawa ya yi yana kallon window, saboda wata iska me daɗi dake shigowa ta windown. A yanzu komai na rayuwarsa ya hau seti, ba ya jin akwai wani buri nasa da rage bai cika ba, komai ya setu, komai ya hau kan hanya, ya samu dangi, ɗan uwa, uwa, mata ga shi har da suruka, shi ko me zai yi in ba godewa Allahnsa ba. Da ga nan kuma sai ya shiga tsara abubuwan da zai yi idan ya bar asibtin, dan ba zai yi shiru a kan abun da aka masa ba, kuma ya san ko suwa suka masa hakan, dan case ɗinsu shi ne aiki na ƙarshe da ya yi. *** Haka Aliyu ya ci gaba da samun kulawar likitoci a asibitin, har zuwa lokacin da ya samu sauƙi, a cikin jinyar da ya yi, 'yan uwansu na haɗejia duka sun zo sun duba shi, ba ƙaramin daɗi suka ji ba a sanda suka ganshi, kuma shi ma ya ji daɗin ganinsu sosai. Bayan ya warke ne suka ɗunguma zuwa Hadejia su duka, domin bikin Rhoda, wadda ta zaɓi sunan Rauda a yanzu, dan bayan ta karɓi musulunci aka tambayeta sunan da take so a sa mata, sai tace Zaid ya zaɓa mata, shi da kansa yace ta karɓi sunan Rauda, dan yana kama da sunanta na da, kuma ma'anar sunan ma me kyau ce. Haka aka sha bikin amarya Rauda da angonta Zakar. Wanda suka ci gaba da zama a haɗejia, kasancewar shi Zakar ɗin a nan haɗejian yake aiki. *BAYAN SHEKARU BIYAR...* *No.275, Asokoro, Abuja...* Anna ce zaune a kan kujerar daning, su na magana da Aliyu dake zaune a kan kujerar dake facing ɗinta. Mishal ce ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da tray, wanda ta ciko shi da wasu warmers, ga tulelen cikinta tana turashi gaba. “Sannu Hafsat. Kai Aliyu ka tashi ka temaka mata mana” cewar Anna. Kuliya ya miƙe tsaye yana nufarta, trayn hannun nata ya karɓa, sannan ya ƙaraso ya aje shi a kan danning, ya koma inda Mishal take, ya kamo hannunta, tana takawa a hankali har suka iso danning ɗin, ya zaunar da ita a kusa da Anna ya na jera mata sannu, ita kuma ban da gyaɗa musu kai babu abun da take. “Sai da na ce miki ki bar girkin nan, amma kika ƙi” Anna ta faɗi tana dubanta, ita dai ba ta iya cewa komai, don tun bayan samun cikin nata ta koma muiskila, sam ba ta son yawan magana. Ƙofar falon aka turo, Zaid da ya je ɗaukan Rabi'a a NFF (Nigerian Football Federation) centre ya shigo, sannan ita ma Rabin ta shigo tana biye da shi, sanye take da wata kimonoh, wadda ta saka jersyn Super Falcons a ƙasanta. Kasancewar yanzu haka suna training a kan gasar WACON (Women's African Cup of Nation) da za'a buga nan da sati me zuwa. Dan zuwa yanzu Rabi ta zama ɗaya daga cikin 'yan ƙwallon da ake ji da su a Nigeria, a taƙaicen-taƙaicewa ma a halun yanzu ita ce kw riƙe da wannan kambun na (Best African Women player). Duk yanda ƙungiyoyi da dama suke son siyanta ta ƙi, don ta ce ba za ta taɓa barin ƙasarta ta koma wata ƙasar ba, saboda mijinta da kuma ɗanta. “Maman Junior har an dawo?” Cewar Kuliya dake zubawa Mishal ruwa a cup. “Wallahi na dawo Papi. Wai Mishal ke kika yi girkin nan?” Rabin ta ƙarashe tana kallon kayan abincin dake zube a kan danning. “Sai da na hanata, amma haka ta sulale ta shiga kitchen ɗin ba tare da na sani ba” Cewar Anna, Mishal ta karɓi ruwan da Kuliya ke miƙa mata ba tare da ta ce musu komai ba. “Ina Junior?” Rabi ta tambaya, sakamakon rashin ganinsa a wurin. “Junior! Junior!...” Haka ta shuga ƙwala masa kira tana baza idonta, don ganin ta inda zai ɓillo. Can sai ga wani kyakkyawan yaro dake tsantsar kama da Kuliya ya sauƙo daga kan stairs hannunsa riƙe da Ipad. Rabi ta bishi da kallo tana jinjina kai, wato yana jinta, amsawar ce ba zai iya ba, ita har mamakin lamarin Junior take, ko da ɗiso babu abun da ya baro a hallayar Kuliya. “Papi na faɗi!” Cewar Junior ɗin yana miƙawa Kuliya Ipad ɗin hannunsa. Kuliya ya karɓa ya na kallon yaron. Aliyu Zaid Aliyu kenan, a.k.a Junior, a.k.a Kuliya, a.k.a AZA, duka sunansa ne, ɗan auta a wurin kawunsa, kakarsa, mamansa, dadynsa, papinsa da kuma Nininsa. Zaid ya ja kujera ya zauna yana faɗin. “Wata ran sai na fasa ipad ɗin nan, in yabso na ga ta tsiyar... In ba wulaƙanci irin na Junior ba, ya za ayi mamansa ta dawo daga training, ta kirashi amma ya wuce wurin Aliyu yana faɗin wai ya faɗi a game?” Kuliya ya kalli Zaid yana zaunar da Junior a kan cinyarsa. “Ka fasa, ni kuma sai na sai masa sabuwa, ina ruwanka da sha'aninmu?, mu babu ruwanmu da kowa ba ehe” “Junior Mama fa?” Rabi ta faɗi tana kallonsa. Juyowa ya yi ya kalleta da gray eyes ɗinsa da shi kaɗai ne abu ɗaya da ya gado a wurin Zaid, amma hatta da buɗar idonsa irin ta Kuliya ce. Sai kuma ya sauƙo daga kan cinyar Kuliya, ya tako zuwa wurin Rabi, ya ɗan mata wani gutun murmushi yana rungume ƙafafunta. “Tafi ka bani wuri ba na so” “Haka fa ni ma suka haɗe mun kai shi da Papi last week, wai dan suna kallon Film ɗin 'Tara Dunken' na zo na sauya, shi kenan suka dena min magan, sai jiya suka kulani” Cewar Mishal tana aje cup ɗin hannunta. “Ai ke na sati ɗaya suka miki ma, ni da suka fi sati biyu ba sa kulani fa in ce me?” Cewar Anna cikin taɓe baki. “Sorry Mama” Cewar Junior kamar wanda aka yiwa dole. Rabi ta dunguri kansa tana faɗin. “Ka dena wannan miskilancin naka, idan ka ce irin halin Papi za ka ɗauko wahala za ka sha, don ma de shi Papi an yi nasarar samun Nini ta seta masa hanya, kai ko sai de ka ci jibga, don dukanka zan fara...” Shi dai bai ce mata komai ba, sai ƙasan kimonohnta da ya riƙe. “Nini? Ashe ke kika seta ni?” Kuliya ya tambaya yana kallon Mishal, ita ko tai masa banza, don ta san idan ta biyashi yanzu sai su zo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112