Chapter 62
Chapter 62
Habibty, dan Allah!...” Da ƙyar ta iya shanye kukan nata, saboda lallashin da Fu'ad ɗin ke mata. “Menene ma kika ce sunan makarantar?” “Brickhall School, a nan Kaura District take, kusa da game Village” “Inshaallah zan nemo miki Rabi'a, sai dai idan abun yafi ƙarfina” Da haka suka yi salama, don yau babu wayar soyyayar da aka saba, saboda yanda take cikin tashin hankali. Sallamar Babansu ta ji a tsakar gida, hakan ya sa ta fito da sauri, Ɗan Lami ya kalleta a lokacin da yake zama kan tabarmar da su Habiba suke kai, don shi ma ya samu a ɗan lasa masa abun da aka samu. “Abba sannu da zuwa” Ta faɗi cikin muryar wanda ya gama kuka. Ɗan Lami ya ɗan kalleta kaɗan, sannan ya kauda kai, don haushinta yake ji, ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba, a sanda ya ji labarin ta tura manemin aurenta wurin yayansa Habu, a inda ya ji labarin kuɗin yaron ya yi zaton wurinsa za ta turo shi, amma sai ba ta yi hakan ba, kuma haushi bai ƙara kama shi ba, sai da Kawu Habu ya ambata masa yawan kuɗaɗen da shi ma nemin auren nata ya kawo, kuma Kawu Habun ya yi mirƙi si-si ya hana shi ko asi a cikin kuɗin, yace wai da su za'a haɗa a yi wa yarinya kayan ɗaki. Da ace kuɗaɗen hannunsa suka shi, ai da ya morewa rayuwa, don ko karuwarsa Vicky ba ta isa ta ƙara rena masa hankali ba. “Abba har yanzu Rabi ba ta dawo ba” Saratun ta kuma faɗi tana durƙusawa a gabansa, sai da ya juyo ta kalli idon Habiba, sannan ya furta. “Ni na aiketa? Ita wadda ta aiketa ai ita ya kamata ta fita nemanta ba ni ba!” Habiba ta taɓe baki, a zuciyarta kuwa murmushi take, don bisa ga dukkan alamu aikin wannan malamin ne ya ci, a rannan ta saurari gaba ɗaya zancen da Rabin suka yi iya da Saratu, kuma hakan ya sa ta kira yayarta Hajiya Inno a waya, aka haɗa musu wani laƙani da zai sa duk wani ɗa na mijin da zai kalleta ya yi sha'awarta, kuma a yau ɗin nan aka tura aikin, kuma bisa ga dukkan alamu aikin ya ci, tun da ga shi ba ta dawo ba, kuma shirinta na gaba shi ne; idan Rabin ta dawo, sai ta sa Ɗan Lami ya koreta daga gidan. Jiki a saɓule Saratu ta miƙe ta koma ɗaki, ta na Allah wadarai da rayuwa irin ta gidansu. ____________________ _Suwanah!... Salmaniansa, kuna jin abun da nake ji?_ _wai Rabi ta ɓata?_ _To sai ku ta ya ta da addu'ar Allah ya bayyana mana ita_ _Game da YUSHAL (ALIYU & MISHAL) kuma, sai de na ce Allah dai-daita tsakani_ _Godiya mara adadi_ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *15* ~~~ _-*She doesn't need to be your whole world. She just wants to know that she holds a special place in it. That's all*-_ *** *** Follow my Wattpad account 👇 https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends ~~~ KULIYA POV. “Babu zafi yanzu?” Cewarsa ya na kallon Mishal, wadda idanuwanta suka yi jajir, saboda kukan da ta sha, kuma har zuwa lokacin ba ta dena hawaye ba, sai jan zuciya take. Zaune take a kan wata kujera dake cikin permacyn da ya tsaya siya mata magani, bayan da suka dawo daga asibiti. Shi kuma ya ɗan sunkuya a saitin fuskarta ya na kallonta, a hankali ta gyaɗa kanta tana jan hanci, sai shi ma ya gyaɗa nasa kan. “Then tashi mu koma gida” Ya faɗi yana miƙewa, tare da miƙa mata hannunsa, ta kalli hannun nasa, sannan ta kalli fuskarsa, ba ta taɓa zaton cewa son Kuliya take ba sai yau! Yau ɗin da kishi ya rufe mata ido har ta aikata abun da ba ta taɓa zaton za ta iya ba. Sai ta yi ƙoƙari ture wannan tunani, ta ɗago da nata hannun, ta ɗora a kan nasa, a hankali shi kuma ya naɗe natan cikin nasa. Mishal ta lumshe idonta, ta buɗe, saboda wani ɗumi da ya ratsata, ɗumin hannunsa ne ya ratsa har tata fatar, a hankali Kuliya ya ɗagota daga zaunen da take, sannan ya riƙe hannunta da kyau ya na jawota jikinsa, hakan ya sa Mishal riƙewa wata iska a maƙoshinta, ta juyo ta kalleshi, a sanda shi ma yake kallonta. Idanuwansa kaɗai sun isa su bayyanar da gajiyar da yake ɗauke da ita, kuma bayan gajiyar ma da alamun yunwa. Ta haɗiye yawu, a lokacin da suka fara tafiya a tare, don rabin jikinta yana jikinsa. Ko da suka shiga mota ma ba gida suka wuce kai tsaye ba, sai da ya tsaya a wani super market ya sai mata chocolate. “Na gode!” Ta faɗi cikin muryarta da ta gaji da kuka, a karo na farko tun bayan sanin Kuliya da ta yi, ta ga ya yi wani abu me kama da murmushi, dan wannan ba murmushi ba ne, kuma dai kamar murmushin. Ita ta na mamakin halinsa, ɗan uwansa sam ba haka yake ba, su na tafiya a mota, Kuliya ya jefo mata tambayar da ke ci masa rai tun bayan ganinta tare da wannan me kama da shi ɗin. “Hafsat! Wacece wannan wadda na ganku tare da ita?” Mishal ta yi murmushi tana ɓare ledar chocolate ɗinta. “Yayata ce, Anti Adawiyya!” Ƙiiiii!, kake ji ƙaran sautin birkin da Kuliya ya taka, gabansa na wani irin matsanincin bugu ya juyo ya kalleta, ita ma ta ɗa firgita, dan ta kai chocolate ɗin bakinta kenan ya taka birkin, hakan ya sa chocolate ɗin ta gogi gefen bakinta, duk da halin ruɗu da Kuliya ke ciki sai da ya yi dariya a ransa, ganin yanda chocolate ɗin ta gogu a gefen bakinta, abin dariya!. “A ina kika santa?” “Aikin shara take a school ɗinmu” Kuliya ya juya ya kalli gefen titi, kamar me neman wani abu. “Shin kin san wani abu game da ita?” Mishal ta girgiza kanta. “Ni kaina a sanda na fara ganinka sai da na yi mamakin kamar da kuke da ita, amma a sanda ta bani labarinta sam ban ji wani abu da ya danganceka a ciki ba” Kuliya ya dafe kansa. “Kin san gidansu?” Ya tambaya ba tare da ya ɗago kansa ba, ita ma sai ta girgiza kanta. “Ko unguwarsu ban sani ba” Ba zai iyu ba, babu ta yanda za ayi a ce suna kama irin haka ba tare da wani dalili ba, gaskiya ne yarinyar tana kama da shi, zai iya yiwuwa ta zama ɗaya daga cikin ahalinsa, ya kamata ace ya yi wani abu a kai. “Kuma akwai!...” “Ya isa Hafsat, kaina ba zai iya ɗaukan wani batun ba, please!” Ya yi saurin katseta, ya na yiwa motar key, Mishal ta taɓe bakinta cikin halin ko in kula, da ma so take ta faɗamasa cewar akwai wani me kama da shi again, amma tun da ya dakatar da ita ai shikenan, shi ya jiyo. Kuliya na tuƙa motar ya na hasaso yadda za ta kaya tsakaninsa da su Karima, don basu ci bilis ba, sai ya ɗauki mataki a kansu. *Chikakore, Kubwa, Abuja." *05:30 AM.* Gate ɗin ɗaya daga cikin maka-makan gidajen dake layin ne ya buɗe, me gidan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112