Chapter 4
Chapter 4
green color eyes ɗinta. “A wani class kike ?” Yanzu ma bata amsa shi ba, hakan yasa Abdul tunanin ko de bata jin hausa,sai de kuma farin fatarta baya kama da na larabawa, farace, fara kuma sosai, sai dai ba irin farin fatar larabawa da turawa ba. Kyan fuskarta, idanuwanta da kuma gashin kanta sune suke kama da na larabawan, idan zai iya sakata a jerin mutanen nigeria, sai dai a danganta ta da jinin shuwa arab. Mishal ta zuƙi taliyar indomien da ke bakinta,sannan ta ci gaba da kallonsa. “Can't you speak hausa ?” “Me kake buƙata ?” Ta tambaya da hausa tana kallonsa. “Ashe dai kina ji....” “Na ce me kake buƙata ?” Abdul ya ɗan shafa kansa sannan ya ce. “Idan ba zaki damu ba, shin zamu iya yin soyyaya” Sai ta yi murmushi, wanda ya bayyana ƙarafunan braces ɗin dake saman haƙwaranta, wanda Abdul ya ɗauke shi a matsayin amasar tambayarsa, sai shi ma ya yi murmushin. Mishal ta rufe flask ɗinta a karo na biyu, sannan ta miƙe ta zagayo ta ɓarin da Abdul yake. “Miƙe pls” Yana murmushi ya miƙe tsaye. Tashi ɗaya Abdul ya ga yanayin fuskarta ya sauya zuwa fushi mabayyani. Sannan ba ta yi wata-wata ba, ta ɗaga hannunta na dama ta ɗauke shi da maruka uku kyawawa. * Tsaye suke a office ɗin principal ita da Abdul ɗin da ta fasawa baki da marin da ta masa, bayan shi Abdul ɗin ya kawo ƙararta office ɗin principal ɗin. Principal ɗin nasu ya kalleta da kyau, bayan da Abdul ya gana tsara masa aabin da ya faru, kuma ko musu ba ta yi ba, ta amsa lefinta, shi a rayuwarsa bai taɓa ganin yarinya irin wannan Hafsat ɗin ba. Kullum cikin kawo ƙararta ake, ba ga malamai ba, ba ga ɗalibai ba, kuma shi yarasa yanda zai yi da yarinyar. Shi dai ba zai iya korarta daga makarantar ba, saboda tana da ƙoƙari, tana ɗaya daga cikin ɗaliban da suke alfahari da su a makarantar. “Hafsat, me yasa kika mare shi?” Mishal ta wani juya idonta a cikin office ɗin, sannan ta ɗan sosa hannunta. “Zuwa ya yi yace wai yana so na...” “Kuma da ga cewa yana sanki sai ki mareshi ?” “Ai dokar makaranta ya karya, shi yasa na mareshi, ya godewa Allah ma da ban karya masa hannu ba” Principal ya ci gaba da kallon yarinyar, ba wai da wasa take faɗar hakan ba, a bakin gaskiyarta take faɗin zata karya shin, dan ta karya ɗalibai biyu a makarantar, kuma tun daga junior ta fara makarantar, sannan tun da ga lokacin kullum sai an kawo ƙararta. Wani lokacin ma a ajinsu na koyon kung fu take dukan 'ya'yan mutane, hakan yasa shi da kansa yace ta fita da ga anjin koyon kung fu ɗin, amma yarinyar fir taƙi, kuma taƙi ɗaukar ko wani sport sai kung fu ɗin. “Ga wannan takardar, ki kaiwa yayanki” Hannu ta kai ta karɓi takardar, sannan ta sa kai ta fice, ba wannan ne karo na farko da suka taɓa bata takardar suka ce ta kai masa ba, dan idan da sabo ma yayan nata ya saba zuwa makarantar a kan matsalarta. A kusa da staffroom ɗin malamai mata ta ga wannan yarinyar....wannan yarinyar da ke tsananin bata tausayi. Sai kawai ta tsaya da tafiyar da take, ta nufi wurin yarinyar, dan tana so tai mata magana. “Sanu da aiki!” Yarinyar da ke sharar ta yi saurin ɗagowa ta kalleta, ita ma yarinyar ta gane Mishal ɗin, tana yawan ganinta a makarantar. “Menene sunan ki” Mishal ta tambaya fuskarta ɗauke da murmushi. Sai da yarinyar ta haɗiye wani abu, sannan ta amsa mata da. “Rabi'a” Mishal ta gyaɗa kanta. “Me yasa kike aikin shara a nan?...” Rabi ta gyara ruƙon tsintsiyar dake hannunta, to me yasa take mata waɗanan tambayoyin ?, amma kuma abun yaso ya bata mamaki, dan gaba ɗaya ɗaliban makarantar babu wanda ma yake kallonta da kima ko mutunci, kallon banza suke mata, ga wahalar da suke bata, wasu ma har tsokanarta suke. “Am....Imm...ummm” Ta kafa inda-inda, dan bata santa ba, batama san me za ta ce mata ba. “Is it personal issue?” Kuma tun kafin Mishal ɗin ta yi tunanin cewa ba lalle ace tana jin turanci ba Rabi ta amsa mata da sauri. “Yeah, it's personal” Mamaki ya kama Mishal, duk da dama yarinyar bata mata kama da irin villegers ɗin nan ba, ta fi kama da waɗanda ke cikin ƙuncin rayuwa, duk da ba a walaƙance take ba, amma kana ganinta zaka ga hakan, sai dai kuma yanayinta na wayyayun 'yan mata ne. Sai kawai ta gyaɗa kanta. “Gobe za ayi hutu, inaso ki min siffa, kin iya ?” Girar Rabi ta haɗe wuri guda alamun kokwanto. “Menene siffa ?” Mishal ta ɗan daki gaban goshinta. “Lalle nake nufi, kin iya?” Sai Rabi ta yi murmushi, a shekaru zata iya girmewa yarinyar, amma da alama yarinyar tana da kirki. “Na iya, kina so na miki ne?” Da sauri Mishal ta gyaɗa mata kai, kuma da gaske tana buƙatar amata siffar, dan sallar azumin ba a Abuja zasu yi ba, a mahaifarsu zasu yi, wato Maiduguri. “Wanne kike so, ɗan gam ko ɗan zane ?” “Ni dai baƙa nake so, kuma a hannu za ki min” Sai Rabi ta gyaɗa kanta. “A ina zan miki ?” Mishal ta juya tana kallon inda suke, to a ina da suka haɗu ?, a makaranta suka haɗu, to a ina zata mata da ya wuce makarantar ?. “A nan mana” Rabi ta zaro ido tana jinjina yarintar yarinyar. “Makaranta ce fa” “To sai me?, kin ga kawai zan sa a siyo min lallen, gobe zaki min, sunana Mishal” Rabi ta kuma gyaɗa kanta....kafin wata murya ta yi magan da ga ƙofar staffroom ɗin malamai mata. “Ke!, da kika tara wannan sharar a nan ub*nki ne zai kwashe!” Rabi ta zabura za ta koma ta ci gaba da sharar da take. “Kawai sai ki zagi ub*nta, me ta miki ?” Muryar Mishal ta katse mata hanzari, da sauri Rabi ta juyo ta kalli Mishal ɗin, wadda ta wani haɗe rai, tana kallon malamar. “Ke ba na ciki da rashin kunya, ki bar ganin sauran malamai su na ƙyaleki, wallahi ni ub*nki zan ci....” “Ahir ɗinki Abu, ub*ana ya fi ƙarfinki, wallahi ki fita sabgata, in ba haka ba yanzu zan nuna miki kalar nawa rashin hankalin, kuma ki musa ki gani” Mishal ta katseta tun kafin ta rufe bakinta, kuma cike da rashin kunya take maganar, tana yi tana nuna malamar da ɗan yatsa. “Bamu taɓa haɗuwa da ke ba ne, dan kina malamar art ba shi zai hana na bi ta kan mutuncinki da kika zubar na wuce ba, dan haka ki kula, kuma sharar ba zata kwashe ba, ki yi abinda kike ganin zaki iya....” TALLAH! Salma's Graphics: •Muna haɗa book cover. •Banner •poster •Certificate Kuma duka a kan ₦ 300 kacal. Domin neman ƙarin bayani: 08130172702. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #Taurariwriters °°°°°°°°°°°°°°°° *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *02* ~~~ *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja* *06:00pm* Me gidan Abubakar Muhammad Auwal, tare da matarsa Hajjara, sai yaransu guda biyu, Hammad wanda ya ci sunan kakansa da kuma fahima, 'yar jaririyar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112