Chapter 2
Chapter 2
da suka wuce, dan tun bayan zuwanta gidan ba'a ƙara mata sabon ɗinki ba. Kuma a halin yanzu kayan sun mata kaɗan, ba wai dan ta ƙara ƙiba ba, sai dan girma da shekaru suka ƙara mata. A yanzu ba ma ta saka kayan, kayan yayarta Baby da ta rasu su takesakawa, dan a sanda Babyn ta rasu ba zata wuce shekarunta ba, duk da Babyn na fama da cutar sickler. Baby?!, sunan ya maimaita kansa a cikin ranta, a sanda ta ɗago wata doguwar riga sama, rigar ta Babyn ce, kuma ba wannan ne yasa ta tsaya ta ci gaba da kallon rigar ba, sai dan tunawa da ta yi da yanda Babyn ke matuƙar san rigar. _“Umma ki ce ta bani....” _ Muryar Rabi'an ta faɗi a wancan lokacin, mahaifiyarsu dake zaune a kan sofa tana duba wasu takardu ta juyo ta kallesu, sannan ta kalli rigar da suke kokawa a kanta. _“To wai ke Adawiyya me za ki yi da wannan rigar ?, in ce de ta miki yawa” _ Rab'ia ta turo baki gaba tana wata shagwaɓa irin tata ta autanci. _“Wallahi Umma ina san rigar” _ Baby ta fisge rigar daga hannun Rab'ia tana hararta. _“Ai ko ba zan baki ba....” _ “Yayar ummanta Adawiyyan Umma, rabu da ita, zan sai miki sabuwa, wadda ta ma fi tata kyau.....” Sai kawai ta ninke rigar ta maida ta cikin jakar, Allah ya sani sam bata san tuno LABARINTA na baya, dan hakan sam bai da amfani a ganinta, saboda wannan wata rayuwace da ta shuɗe a baya, sannan rayuwace wadda ta tafi da abubuwa da dama. Ciki kuwa harda ita kanta, saboda gani take kamar wannan ba waccan Rabi'ar data sani ba ce, wannan wata baiwa ce dake aikatau a gidan mahaifinta, ba kamar waccan Rabi'ar ba, me rayuwa cikin gata da kulawa, autar ummanta, ƙanwar yayarta, jika mafi soyuwa a wurin kakkaninta. Wata doguwar riga wadda Saratu ta bata kunce ta ɗauko, ta haɗa da hijabin Baby, sannan ta zuge jakar tana miƙewa. Bayan da ta aje hijabin a kan jakar, hannunta kuma tiƙe da rigar da ta ɗauko ɗin. “Rabi dan Allah yaushe za ki min ƙunshin ?” Saratu ta tambaya tana aje rigar da ta gama gogewa. Rabi ta ɗan dakata da tafiyar da take, sannan ta juyo ta kalli Saratun dake kallonta ita ma. “Saura kwana nawa ne sallar ?” Saratu ta amsa mata da “Ehhh to!, gaskiya ba na ce ba, amma jiya na ji Umma (wato Habiba, dan haka suke kiranta) na faɗin saura kwana huɗu ne ko uku?...” “Gobe za ayi hutu a makarantar yarana nan, sai na miki goben, nima ina so ki min kalaba” Ta ƙarashe tana ɗan dukan kanta da ke ɗauke da manyan kalaba guda huɗu, dan bata kitso, kuma ba komai ya ja hakan ba sai santsi da tsayin da gashin nata ke da shi. tun mahaifiyarta na da rai bata kitso, sai dai Ummar tasu ta kaisu wurin gyaran kai. Amma yanzu fa ?, gashin nata ma ya fara raguwa saboda rashin gyara, kalabar da Saratun ke mata ita kaɗai kan nata ke samu. Saratu ta gyaɗa kanta sannan ta ce. “Allah kai mu goben” Har Rabi zata fita da ga ɗakin sai ta juyo. “Wani kala zan miki ?” “Ɗan gama nake so” Da ga haka bata ƙara cewa komai ba ta gyaɗa kanta, sannan ta fita da ga ɗakin, wanka ta je ta yi, ta fito bayan da ta gama wankan, saboda yanzu ana cikin azumi shi yasa ayyukanta suka ragu a gidan. Dan idan baki buɗe ne, sai ta kai niƙan alkamar da Habiba ke yin finkason safe, idan kuwa a week end ne ita ce ma da kanta take suyar finkason. Kuma ta hanyar kuɗin da take samu a finkason, da albashi da ake bawa Rabin a wurin aikinta, Habiban ke iya kula da gidan, dan komai na gidan ita ce ke yi. Bayan ta shiga ɗakin, mai kawai ta shafa, sannan ta ɗauki hijabin da ta fitar ta saka, ta yiwa Saratu sallama, ta fita. “.....Kin ji matsalata da ke, dan Allah Habiba yanzu idan baki rufa min asiri ba waye zai rufa min?....” Rabi ta ja ta tsaya a sanda ta ɗora idonta a kan mahaifinsu tsaye yana ƙanƙan da kansa a gaban Habiba,wadda ta wani ɗaga kai sama tana shirin zazzago buhun masifa. “Wallahi Ɗan Lami baka isa ba, a kan me zan ɗauki kuɗi na baka?, bacin na san caca za ka je ka yi da su......” Rabi bata tsaya ta gama jin abinda take faɗi ba ta sa kai ta fita. Kuma abinda Habiban ta faɗi gaskiya ne, dan baban nasu babu wani aiki da yake face cacar, duk kuɗin da zai samu a caca suke ƙarewa. Sai da ta ɗan tsaya a ƙofar gidansu, ta ɗan ɗaga kai saka, da ga nan inda take tana iya hango dutsen zuma rock, dubanta ya kai kan tarin bolar dake tsallaken ƙofar gidansu. Bolar har tsiri take dan tsabar yawanta, da sauri ta ɗauke kanta da ga barin duban bolar, dan Allah ya sani idan ma takalleta zuciyarta har wani tashi take, dan ta tsani ƙazanta a rayuwarta. Haka ta ci gaba da tafiya a cikin ƙazamin layin nasu, wanda kwatanni da datti suka masa ƙawa. Akasarin mazauna unguwar ta Madalla masu magana da harshen gwari da baagi ne, sannan akwai hausawa sai nufawa, da wasu sauran yarukan, sannan a cikinsu akwai musulmai da cristian. “.....Rabi!” Ta juyo saboda jin an kiran sunanta, gamin wanda ke kiran nata yasa ta yi murmushi tana juyowa gaba ɗaya, Zara ce, mutum ɗaya da za ta iya ɗagawa ta kira da ƙawarta. “Aikin za'a je?” “Eh mana, keda kika sani” Suka ɗan yi dariya. “Kunu kika siyo ?” Rabi ta tambaya yayin da idonta ya sauƙa kan jug ɗin dake hannun Zaran. “Eh wallahi, bari na wuce, kafin Umma ta soma faɗan na daɗe....” Kuma daga haka suka yi sallama, bakin titi ta fita, a titin ma sai da ta yi wata doguwar tafiya a ƙafa, kafin ta iso Ɗan kogi motor park. Inda ta saba hawa mota, ta biya kuɗin da ta saba biya a kullum, wanda Habiba ke bata dan yin kuɗin motar, saboda da ga gidan nasu zuwa makarantar da take aikin akwai nisa. Tafiyar kusan minti 40 ce. Sun yi doguwar tafiya a motar, kafin suka isa Joy Emodi CI inda za'a sauƙeta, daga nan ta soma tafiya a ƙafa, wadda ta ɗauketa tsawon lokaci, kafin ta iso makarantar da take zuwa aikin shara. *Brickhall School, Kaura district, Abuja* A hankali wata farar mota ƙirar Corolla hybrid ta yi parking a harabar makarantar. ko minti ɗaya ba ta yi da parking ba, ƙofar gidan baya na motar ta buɗe. Wata matashiya ta fito,sanye cikin wata baƙar pleate skirt, da kaɗan skirt ɗin ta sauƙo gwiwarta, sai farar oxford shirt, wadda ta ɗora maroon suit a kai, daga gefenta suit ɗin na dama an manna symbol ɗin makarantar, wuyanta saƙale da tie, kanta babu ko ɗankwali, sai gashin kanta wanda ya ji gyara, an ɗaureshi cikin pony rail, jelar sai reto take a bayanta. Bayanta goye da backpack ɗinta me kyau, ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112