Skip to content

Chapter 95

Chapter 95

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

kuma ina sansa, dan haka ba zan bari ina ji ina gani ki raba ni da shi ba” Nan take wasu ƙofafi suka buɗe a ƙirjin Mishal, kishi ya soma kamata, wani abu me kama da wuta ya shiga ruruwa a cikin ranta. “Mijina kike so?” Ta tambaya ta na nuna kanta. Cike da gadara Siyama tace. “Ƙwarai kuwa, mijinki nake so, kuma tun kafin ya sanki nake sansa. Dan haka na zo ɗaukar mataki” Ta ƙarashe tana fitar da wuƙa daga jakarta, Mishal ta zabura ta finciko wayar tvnsu, ta hau dukan Karima da Siyama, abun su kansu ba ƙaramin mamaki ya basu ba, dan ba su taɓa zaton ƙaramar yarinya kamarta za ta iya aikata hakan ba. Dukansu take kamar wadda Allah ya aikota, su kuma banda kururuwa da ihu babu abun da suke. Jin sautin dirin motar Kuliya ne ya sa Mishal yada wayar, ta leƙa ta wundo ta ga tabbas shi ne, ta dawo da baya, ta buga kanta a jikin bango, tare da fasa ƙara, wanda ta karaɗe gidan baki ɗaya. *You are not hard to love; You've just run into a few who didn't know how to...* *** *No.86, Garki 2, Abuja...* RABI'A POV. Kwance take cikin style ɗin motsa jiki na plank, tana kan tabarmar motsa jiki ne, a cikin gym ɗin gidan. A rannan da Zaid ya kaiya ganin likita ya shawarceta da yawaita motsa jiki, kuma hakan ne ya sa Zaid ɗin kawo mata mashinan motsa jiki. Sanye take da wani baƙin leggings, sai wata yar siririyar tanktop da ta saka. Daga gefenta kuma ruwan da ta tanada ne dan sha a sa'ilin da ta gaji. Ba ta yi tsammani ba kawai ta ga ya shigo, hakan ya sa ta kusa tuntsirawa daga yanda take, ba shiri ta tashi daga kwanciyat plank ɗin ta zauna a kan tabarmar tana kallonsa. Sweat pants da wata singlet ne a jikinsa, hannunsa na hagu riƙe da mug. “Kai kuma me ka shigo yi a nan?” Kamar wani me neman wanda zai ba shi amsa haka ya juya ya kalli bayansa sannan ya juyo ya kalleta. “Motsa jiki mana” ya amsa matavikin ɗage gira, na shi bai ga lefin abun da ya yi ba. “Motsa jiki?” “Ƙwarai.... Ko da an ƙa'ide cewar maza ba sa yi, mata ne kawai ke yi” Rabi'a ta girgiza kanta, dan ta ga alamar ba motsa jikin ya zo ba, neman magana ne kawai irin nasa. Dan haka ta juya abunta tana sauya salon motsa jikin nata zuwa cat cow pose. A duk sanda za ta sunkuya cikin motsa jikin sai ta kalli Zaid dake bayanta. Zaid ya yi murmushi ya na aje mug ɗin hannunsa a kan wata chest drawer, sannan ya tsaya yana kallon kansa ta cikin mirrors ɗin dake zagaye da gym ɗin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana wani jujjuyawa. Kafin ya ɗaga hannayensa ya na auna girman muscle ɗinsa. Duk abun da yake Rabi na leƙensa ta ƙasan ƙafafunta. Kamar da aka ce ya kalleta ta cikin mirrorn, karaf suka haɗa ido, da sauri Rabi ta waske ta ci gaba da cat cow pose ɗinta. Zaid ya kuma yin wani murmushin yana kama rigarsa ta ƙasa, sannan a hankali ya cireta. Tsabar gulma Rabi ba ta san sanda ta dungura ta ka ba, saboda wasu tabbubbuna da ta ga a bayansa, ga kuma tsayawar da ya yi babu riga a jikinsa, wani abu da sam bata so, shi kuma ga shi kamar wanda aka yiwa asirin rashin zama da riga, kwata-kwata bay a san zama da riga a jikinsa in dai yana gida. “Wai dan Allah Raj me ya sa ba ka da kunya ne?” Rabi ta tambaya tana rufe idonta da hannunta, yayin da ta yi zaman cin tuwo bayan da ta dungura. Zaid ya juyo ya kalleta. “Me kuma na yi?” “Dan Allah ka sa rigarka?” Ta faɗi tana ƙara rufe idon nata. Dariya ya yi mara sauti ya na cillar da rigar gefe, sannan a hankali cikin takun sanɗa ya isa inda take ya zauna a gabanta, har gwiwowunsu na gogar na juna. “To na meda, buɗe ido naki” “Ka ta babbatar?” Yana ƙunshe dariya yace. “Dubu bisa ɗari” Kamar me tsoron ganin aljanu haka ta sauƙe hannunta, ai kuwa ta yi kyakkyawan gani, dan shi ɗin ne zaune a gabanta, babu riga a jikinsa, ga wannan chain ɗin sarƙar da ta saba gani a wuyansa ya kwanta a ƙirjinsa, waɗanan tabbubbuna na jikinsa suka mata maraba lale!. Zabura ta yi za ta miƙe, kuma kafin ta miƙe ɗin ya sa hannunsa ya janyota, bata faɗa ko ina ba sai kansa, hannayenta naɗe a ƙirjinsa, yayin da shi kuma ya saka hannunsa ɗaya ta bayansa. Ta zazzaro idanunwata tana kallonsa, kamar wadda aka tunawa yadda jikinsa yake a lokacin ta yi saurin kulle idonta. Zaid ya yi dariya, a wannan karon me sauti ya yi, sannan ya mannata da jikinsa yana rungumewa, har zuwa lokacin idonta a rufe. “To wai miye na jin kunyar?. Na ga kin...” Be ƙarashe ba saboda dukan da Rabi ta kaiwa bakinsa, dan ta san me yake shirin faɗa, shi ya sa a ko da yaushe take faɗin ba shi da kunya, bakin nasa ya dafe yana mata dariya. Da sauri ta miƙe daga kansa ta fita da gudu ta bar masa gym ɗin. Dan da ma kawai ta ɗan shigo dan ta motsa jikin nata ko kaɗan ne, saboda yau za'a ɗaura auren Anti Saratu, kasancewar babu wani shagali ya sa bata shirya da wuri ba, don Abbansu yace daga zarar an ɗaura za a kaita ɗakinta, babu wata bidi'a da za ayi. Zaid na dariya ya miƙe zai bi bayanta, wayar dake cikin aljihunsa ce ta yi ƙara, hakan ya sa ya fasa binta ya zaro wayar ya ɗaga kira da sauri, ganin lambar abokan aikinsa, kuma wakilan da ya naɗa dan kamo Alhaji Bala da usman, dan tun daren jiya aka basu izinin kamu. “Sir, mun kamosu, yanzu haka mun wuce headquarter da su!” Abun da na cikin wayar ya fara faɗi kenan, hakan ya sa Zaid ya ɗaga kansa sama yana lasar lips ɗinsa. “Na gane, anjima zan samu na leƙo” “Ok sir” Daga haka ya sauƙe wayar, shi kenan, duk wannan shekarun da ya kwashe cikin wannan aikin sun zo ƙarshe, assignment ya ƙare, komai ma ya ƙare, yanzu lokaci ne na fara sabuwar rayuwa tare da Adawiyyansa, lokaci ne da Rhoda za ta sake sabuwar rayuwa, lokaci ne da shi kansa zai huta, dan kuwa ba zai karɓi wani sabon aiki kwana kusa ba, zai ɗauki hutu ne dan ya kula da Ammatansa, zai ba ta lokacinsa duka, zai kuma zauna da ita na tsawon lokuta. Zuwa yanzu abun da ya rage a aikin nasu kaɗan ne, abun da ya rage bai fi saura ba, dan tun da har an kama Alhaji Bala to an tsallake babban tudun, saura da me kuma?; Alhaji Bala ya amsa lefinsa, sannan ya bayyana sunayen abokan harƙallarsa da kansa, duk kuwa da su ma kansu sun san wasu daga ciki. Usman da abokansa kuma shi ya san yanda zai yi da su, dan kuwa ɗaya bayan ɗaya ya sa aka kamo su, kuma shi ya

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112