Chapter 34
Chapter 34
za mu iya rabuwa da juna ba, gwara kawai mu haƙura...” Cewar Aliyu. Bai ko rufe bakinsa ba Zaid ya ɗora da: “A'a Malam Ila, ba za ayi haka ba, ku ɗauki Aliyun kawai, ni na haƙura!” * Tsaye suke a harabar gidan marayun, yayin da Malam Ila ke kallonsu yana sharar ƙwalla, Aliyu kuma na kuka, Zaid na bashi baki. “Hey! Don't cry, na ce maka zan riƙa zuwa ina dubaka...” Shi dai Aliyu hankalinsa bai kwanta ba, dan ba ya jin zai iya zama a wurin nan. A kan idonsa Malam Ila da Zaid suka fice daga wurin. Ashe ƙarshen ganawarsu kenan, ahse ba za su ƙara ganawa ba sai bayan wasu shekaru masu tarin yawa. Dan a cikin kwana uku kawai ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku. Malam Ila da Zaid na fita, Malam Ilan ya kalli Zaid. “To Zaidu, tun da ka zaɓi ka koma gidanku ka ci gaba da zama, sai ka koma can ɗin, amma duk safiya, rana kuma dare, ka riƙa zuwa kana karɓar abinci a wurina” “Na gode Malam Ila, Allah ya saka da alkairi” “Kai ai ba komai, ku yaran kirki ne, 'ya'yan mace ta gari, Allah ya maka albarka” *Present day...* *Room No.45, National Hospital, Abuja.* KULIYA POV. Daga kan gadon marasa lafiya, Abubakar ne kwance, yayin da na'urar oxygen ke maƙale a kan fuskarsa, kasancewar ba ya iya numfashi me kyau. Daga gefen gadon kuma, Kuliya ne tsaye, riƙe da hannunsa, hawaye ya ke sharewa akai-akai. Idan zai iya tunawa, rabonsa da kuka tun ranar da ya bar garin kano, ranar da ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku. Amma a yau sai ga shi ya na kukan tsoron rasa amininsa, babban abokinsa, wanda idan ka ɗauke Anna, kaf duniya babu me iya jurar halinsa in ba shi ba, kuma ba ma haka ba, a yau ɗinan Aabubakar ya sadaukar da rayuwarsa don ceton tasa rayuwar. Shi ɗin da bai aje kowa ba bayan Annan, shi kuma da yake da mata, yara har da ƙanwa da kuma 'yan uwa, ya iya sadaukar da rayuwarsa don kawai ya ceceshi. Daga gefe kuma Symon da hannunsa ke ɗaure da bandage ne, sakamakon raunin da ya samu a artabun da suka yi da 'yan ta'addar nan, sai Sharon wadda ke hawaye, sai kuma Kamis, Sani da Mubarak sun yi jigum-jigum cike da jimamin abun da ya samesu, don gaba ki ɗayansu abun ya shafa. Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, kawun Abubakar wato Alhaji Musa ya shigo, tun bayan da aka gamawa Abubakar ɗin tiyata yace su kira masa shi, su kansa ba su san dalilin hakan ba. Jin sautin muryarsa ne yasa Abubakar buɗe ido a wahalce, sannan ya kalli kawunsu wanda gaba ɗayansa yake a ruɗe. “Abubakar?! Me ya sameka haka?” Da ƙyar Kamis ya iya masa bayanin abun da ya faru. Kawu Musa ya zauna a kusa da Abubakar ta ɓangaren dama, yayin da Kuliya ke riƙe da hannunsa ta ɓangaren hagu. Da ƙyar Abubakar ya kai hannunsa kan abun oxygen ɗin yana ƙoƙarin cire shi daga kan hancinsa. Ganin hakan yasa Kuliya saurin kai hannunsa kan na Abubakar domin hanashi yin abun da yake ƙoƙarin yi. Cike da dauriya Abubakar ɗin ya girgiza masa kai. Hakan yasa jiki a sanyaye Kuliyan ya janye hannunsa daga kan na Abubakar ɗin, har ya samu ya cire abun, sannan ya kalli Kawu Musa. ”Kawu... Za... ka... iya... Tuna... Wassiyar Ummuna... Ta ƙarshe ?” A rarrabe maganara take fita, haka kuma a wahalce, cikin wani sauti mara amo. Hawaye na yi wa Kamu musa zuba ya gyaɗa kansa, don bi da bi maganganun matar wan nasa ta dawo masa, a sanda take kwance a aibiti cikin halin ciwon naƙuda, rai a hannun Allah, kamar dai yanda ke faruwa ɗanta a yaunzu. Hawaye ya gangaro daga idon Abubakar, da ƙyar ya iya haɗiye wani abu sannan yace. “Dukkan wasiyyunta na cika su, na reni Mishal da kaina... Na bata kyakkyawar rayuwa... Na... Na bata farin ciki... Abu ɗaya ne ya rage...” Ya ƙarshe yana ritse idonsa, yayin da Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cike da tausayawa. Kawu musa ya gayɗa kansa. “Na mata alƙawarin in dai Allah ya yarda zan aurar da Mishal ga miji na gari, sannan kafin... kafin na bar duniya, zan barta a hannu na gari...” Kawu musa ya girgiza kai cike da sallalami. “Ka dena faɗin haka Abubakar, Insha-Allah za ka miƙe a kan ƙafafunka...” Abubakar ya yi wani murmushi me ciwo. “Ba na tunanin haka Kawu Musa... Ba... Ba na jin zan ta... Tashi, don haka nake so a ɗau rawa Mishal aure yanzu-yanzun nan!...” Wani irin dokawa zuciyar Kuliya ta yi a cikin kunnuwansa. Ya ji wata ƙara a ƙirjinsa kamar ta fashewar glass, kamar glass ɗin windown da aka jefa da dutsi. Wai me ma yake ji ne ?, kawai dan an ce za ayi wa wata yarinya aure ?, sai gabansa ya yi irin wannan dukan ?, wai shikan wata jaraba ce ke damunsa kan wannan yarinyar ?. Kafin ya gama shawara da zuciyarsa, Kawu Musa yace. “Waye mijin ?” Abubakar ya ƙara matse hannun Kuliya dake cikin nasa, sannan ya juyo ya kalli Kuliyan. “Al... Aliyu Zaid... Bichi... Ku... Kuliya!, Babban abokina... Na san kaf duniya, babu wanda... Zai... Zai iya riƙe Mishal in... Ba shi ba... Don haka shi ne mijin nata!...” Sakan ɗaya... Biyu... Uku. RAJA POV. A karo na uku ya ƙara jan akwatin dake hannun mutumin da suka zo karɓar kaya a wurinsa, kuma shi ma mutumin kamar ɗazu yaƙi ya saki akwatin. Raja ya ɗaga kansa sama, sannan ya sauƙe. “Ka cika gardama, ni kuma ba na san gardama, ka fahimta ?” “Kuɗin da kuka bamu bai cika ba, don haka sai kun ciko za mu baku kaya” Mutumin ya faɗi yana kallon idon Raja. A hankali Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya gyaɗa kansa, tare da sakarwa mutumin akwatin. “Na fahimta” Ya faɗi yana neman bindigarsa a aljihun wandonsa na baya, kuma yana kamo bindigar, ya fiddo da ita, sannan ya saitata a kan mutumin, bai yi wata-wata ba, ya matsa kunamar. Ƙaran harbin bindigar ya karaɗe wurin. Mutum ukun da suka zo tare da wanda aka harba suka yi ƙoƙarin guduwa, amma sai Rhoda da Zuzu dake tare da Raja suka buɗe musu wuta. A nitse Raja ya sukunya saitin gawar mutumin dake yashe a ƙasa, ya kai hannunsa sannan ya finciki akwatin. “Kun yi wa kanku, babu kuɗi, sannan babu kaya... Ko dan ga ta rai ma ai kun yi!” Daga haka ya miƙe ya juya, Rhoda da Zuzu na take masa baya. *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.* _“Kamar yanda na maka bayani tun daga farko... Ina son na fito takarar sanata ne... Don haka ina buƙatar wasu 'yan kuɗaɗe masu yawa... Wanda zan yi amfani da su wurin yin campaign, kasan yanda mutanen Nigeria suke!, Kaji ne, sai da tsaba, idan ba su ganka da wani abun duniya ba, ba za su ko kalleka ba, bare su zaɓeka... Don haka na ce ka dawo kusa da ni.... Don ku min aikin da ya fi wanda kuke yimin shi a garin kano!...”_ Tar muryar Alhaji Bala ke fitowa daga cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112