Chapter 109
Chapter 109
a ɗazun da ta yi magana murmuyarta ya fito a raunane. “To ba girma nake ba!” “Iyeee, lalle girma, su Mishallyn Aliyu an fara girma” Sai ta yi dariya tana rufe fuskarta da tafukan hannunta. Shi ma sai ya yi dariyar. A lokacin kuma aka turo ƙofar ɗakin. Anna ta shigo, hakan ya sa su duka suka kalleta. ZAID POV. Yana fita da Rabi'a ba su tsaya a ko ina ba sai wani ɗaki dake kusa da wanda aka kwantar da Aliyu, kasancewar ɗakin babu kowa. Suna shiga ɗakin, ya tura ƙofar ɗakin ya rufe, sannan ya jingina bayansa a jikin ƙofar. Yana miƙawa Rabi dake tsaye hannunsa, kamawa ta yi, shi kuma ya jata ta faɗo kan jikinsa, ya saka hanyyensa duka biyu ya rungumeta. Ita ta ɗago daga jikin nasa tana faɗin. “Ka ji yanda kayan jikinka suke warin gumi?” Jikin nasa ya shinshina yana faɗin. “To ya zan yi da rayuwa, larura ta sa na koma ƙazami, kwana ɗaya ban yi wanka ba fa, ga mu yau a na biyu...” Ta ɗan yi dariya tana mayar masa da chain ɗin wuyansa ƙasan rigar jikinsa. “Rhoda tace na faɗa maka, ita ta wuce gida, za ta je ta shirya, wai ku haɗu a kotu” “Uffff! Kin ga Wallahi shaf na manta!” Ya faɗi yana dafe kansa. “Abubuwan nawa ne da yawa, kinga kuma ko su kawu Abdullahi ban kira ba, dan kin san ya kamata na sanar da su halin da ake ciki” Ta gyaɗa kai. “Haka ne... Abun da ya fi kawai yanzu ka koma gida ka je ka yi wanka, ka sauya kaya, sai ka wuce kotun... Kuma ga abinci nan ma na kawo maka” Kansa ya girgiza. “Ba na jin zan iya tafiya na bar Aliyu shi kaɗai” “Wa ya faɗa maka cewar Aliyu shi kaɗai ne, akwai ni, ga kuma Mishal” “Idan kuma wata buƙata ta taso wadda dole sai kun buƙace ni fa?” “Da yardar Allah har ka dawo babu wata matsala da za ta faru” “Kin tabbata?” Ta gyaɗa masa kai. Sai da ya ƙara janta jikinsa ya rungume, sannan suka fita a tare. Ganin wata mata da ban a ɗakin zaune kusa da Aliyu ya basu mamaki. “Ƙaraso Zaid. Wanan ita ce Anna!” Cewar Aliyun yana nuna masa matar dake sharar ƙwalla. Anna ta juyo tana kallon me kama da ɗanta. “Zo nan, ai kai ma ɗana ne” Anna ta faɗi tana miƙa masa hannu. Zaid ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Suka sakata a tsakiya, idan ta juya ta kalli Zaid, sai ta juya ta kalli Aliyu, kafin idonta ya sauƙa a kan Rabi dake tsaye kusa da Mishal. “Wannan ita ce matar taka kai ma?” Zaid ya gyaɗa mata kai. Zaid ya ɗan jima a ɗakin, kafin ya musu sallama, bayan ya faɗa musu uzurin da zai je. Har yabkama hanyar barin ɗakin,maganar Aliyu ta dakatar da shi. “A dawo lafiya Zaid” Sai da ya juyo ya kalleshi, kafin ya gyaɗa kansa yana fita. Rabi ta bi bayansa suka fita tare har zuwa jikin motarsa. Shiga ya yi, kana ya buɗe ɗayar ƙofar dake side ɗin da Rabi ke tsaye, ya mata alama da ta shigo, shiga ta yi ta zauna. “Ban sani ba ko zan jima ban dawo ba, saboda ana gama shari'ar, za mu wuce na kai Rhoda karɓar musulunci” Sai ta gyaɗa kanta tana ci gaba da kallonsa. “Me kike so na kawo miki yau?” “Ba na buƙatar komai, kawai kai nake so?” Sai ya ɗage mata gira ɗaya yana faɗin. “Ni da kai na?” Ta yi dariya tana gyaɗa masa kai. “In dai ni ne kin samu 'yan matana, and zan kawo miki kifi, ko shi ɗin ma ba kya so?” Ta girgiza kanta. “Ina so” Zaid ya ɗaga kafaɗa cikin faɗin “To sai na dawo?” “Ummm” “Kuma tafiya za ki yi ba tare da kin...” Tureshi ta yi tana dariya. “Zaid hoo, baka jin magana Wallahi!” “To ni ki min” Juyowa ta yi tana kama fuskarsa, kafin a hankali ta yi kissing ɗinsa. “Shikenan?” Ta faɗi tana ja baya. Fita ta yi daga motar, tana rufo masa ƙofar. “A je a yi wanka, a ƙazan-ƙazan” Ta faɗi tana leƙo da kanta. “Lalle kin ci tuwo a kaina Adawiyya, amma zan rama” Ta bar wurin tana dariya. Ya tayar da motar yana ƙara sinsinar jikinsa. “Wanka daɗi, wani bai san daɗin wanka ba” Ya yi waƙar yana juya kan motar. *Believe in your dreams...* Anna da Rabi ne suke tafe, bayan da suka dawo daga wani shago da suka je dan siyan ruwa, duk yanda Rabin ta so Anna ta zauna kan ita za ta je, fir Anma ta ƙi yarda, tace sai de su je tare. Dan ita tausayin Rabin take. A kallon farko da ta mata ta gane cewar tana ɗauke da ciki!, shi ya sa take tunanin kamar ba za ta iya ɗaukan ruwan ba. Amma sai ga shi bayam da suka siyo ruwan ma ba ta bar Annan ta ɗauka ba. Ba tare da Rabi ta ankara ba, ta ji juwa ta ɗebeta, ta yi baya luuu za ya faɗi, ledar robobin ruwan dake hannunta ta faɗi ƙasa. Anna ce ta yi saurin kamota. “Sannu!... Kin ga ko?, shi ya sa na ce ki bari na ɗauka, macen dake cikin hali irin naki ba'a barinta ta ɗauki abu me nauyi!” Cikin rashin fahimta Rabi'a tace. “Babu komai fa Anna, wallahi ƙalau nake” Anna ta ɗauki ledar tana dariya. “Haba 'yanan, ai mace me ciki ba a rabata da laulayi!...” Wani shaftareren yanki na zuciyar Rabi'a ne ya yanke ya faɗo ƙasa, wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan bomb ya fashe a ƙirjinta, ta sandare a wurin, ta kasa motsa ko da ƙafarta, sai idanuwanta da ta zaro suna duban Anna. Ciki fa?, wai ita ?, ita Rabi'a take da ciki?. Ganin haka ya sa Anna fahimtar cewa ba ta ma san cewa tana da cikin ba. ”Baki sani ba kenan?” Kamar wata sokuwa haka ta gyaɗa kanta. * Zaune take a kan ɗaya daga cikin kujerun dake wani corridor, har zuwa yanzu ta kasa yarda da abun da ta ji, wai ita ce take da ciki, to garin yaya, daga sau ɗay!... Kunyar kanta da ta kamata ce ta sa ta kasa ƙarasawa. Ta yi jigum-jigum, tana jiran fitowar result ɗin gwajin da aka mata. Wata nurse ce ta fito daga ɗakin da take fuskanta, ta shiga kiran sunayen mutanen dake zaune a wurin, da haka har aka iso kanta, ta karɓi nata result ɗin tana komawa baya, tare da zama a inda ta tashi. Hannunta har rawa yake wurin buɗe takardar. Tar manyan rubutun da takardar ke ƙunshe da su ke sanar mata cewar tana ɗauke da ciki na sati huɗu. Kanta ta sunkuyar ƙasa tana shafa cikinta. A lokacin kuma ƙwalla ta zubo mata. Yanzu kenan ciki gareta?, cikin ma kuma ba na kowa ba sai na Zaid!. ZAID POV. Bayan hujjojji da aka gabatar a gaban kotu, kotu ta yankewa Alhj Bala hukuncin ɗaurin rai da rai, sauran abokan harƙallarsa kuma, ciki har da Garuje, an yanke musu hukuncin dai-dai da nasa, Usman da sauran abokansa kuma, an yanke musu shekare ashirin-ashirin a gidan kaso. Kuma da haka shari'ar ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112