Skip to content

Chapter 18

Chapter 18

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

hankali. Amma sam hankalin nata bai kwanta ba. A duk sanda za ta ga yarinyar kusa da Raja wani irin baƙin ciki ne ke cika zuciyarta. Har addu'a take kan ubangijinta ya bata damar da za ta raba yarinyar nan da haukar dake kanta, don idan aka bata dama, tsaf za ta rabata da wannan rawar kan da take. “Babe Please ka rabu da waɗanan gajojin, kullum idan zan zo sai sun hana ni ganinka” Cewar Uchechin, yayin da suka shiga cikin gidan, har suka zauna a kan kujerar falo, sai wani mammane masa take. Shi kuma ya ci gaba da kallonta da waɗanan lumsassun idanuwansa nasa. Amma bai ce mata komai ba. “Babe magana fa nake” Ta faɗi tana ƙara maƙalƙale shi. Hannunsa na dama ya saka ya tallafo fuskarta. “Gobe zan wuce Abuja” Wannan innocent muryar tasa ta faɗi, yayin da yake kallon idanunta. Shi kansa ya sani abun da yake ba dai-dai ba ne, yasan cewa hatta da taɓa jikinta da yake haramun ne, tunda ba maharramarsa ba ce. Sai dai yana iyaka bakin ƙoƙarinsa ganin basu wuce hakan ba, bayan taɓe-taɓen juna basa ƙetare iyaka. Duk kuwa da yanda Uchechin ke nuna masa cewar hakanfa ba komai ba ne, sai dai shi yasan cewa hakan komai ne. Dan kuwa ba zai taɓa yafewa kansa ba idan har ya aikata abinda take so ɗin, sai dai kuma yana san Uchechi, shi yasa ya kasa rabuwa da ita. Duk da yanda take nuna masa zalamarta a fili. “Shi kenan, ni ma akwai abinda nake yanzu, idan na gama zan biyoka Abujan...” “Sure?” Ta gyaɗa masa kai. Kafin ta ci gaba da tattaɓa sassan jikinsa, ganin kamar suna shirin yin nisa ne yasa shi saurin raba jikinsa da nata. Ya miƙe tsaye yana riƙe kansa. Da sauri Uchechi ta miƙe tana rungumarsa ta baya. “Please Babe, yau kawai, just once....” “Uchechi, get out!” Ya faɗi a ruɗe. “Babe...” “I say get the hell out of here!.....” Ya maimaita mata wannan karon cikin ɗaga murya, kamar ba shi ba, don abu ne mayuwaci ransa ya ɓaci. Nan take Uchechi ta fara hawaye, ta rasa me za ta masa ya fara santa, a ganinta kamar santa ne ba ya yi, dole ne ta koma wurin yayarta Chisoma, dan su san ta yanda zasu ɓullowa lamarin. Jakarta kawai ta ɗauka sannan ta fita. Tana fita Raja ya koma da baya yana kwanciya a kan kujerar. “Astangafurullah, Astangafurullah...” Ya shiga faɗi a hankali. Ya rasa wannan wata iriyar masifa ce haka, daga can ƙasan ruhinsa ba ya san hakan, amma kuma wani abu a cikin kansa na faɗa masa cewar ya aikata. “Rho, ki share mana...” Cewar Zuzu, yana ci gaba da lallashin Rhoda da ta ƙuntume fuska. Ganin fitowar Uchechi da gudu daga cikin gidan yasa suka miƙe da sauri. Dan suna cikin wata rumfa ne dake harabar gidan. Har wata ajiyar zuciya ta yi, tana bawa zuciyarta da kanta haƙuri. “Geti losh!” Cewar Alandi, a ƙoƙarinsa na ganin ya kwaciɓa turanci. Dariya ta kama Rjida, ta juyo ta kalleshi. “Ba geti losh ba, get loss!” Ya sosa kai ya na ɗaga hannu kamar me kai wa duka. “Sai ni Wallahi!... Hhhhh hajiya Rhoda ai kece ba ki gaɗa dai-dai ba, ki bar gani na a hakan nan, masters gareni a fannin kai sara suka!” Rhoda ta kwashe da dariya, ranta fes. *No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja* KULIYA POV. Zaune yake a ɗakin Anna, tun bayan da aka sauƙo a idi ya yi wa gidan dirar mikiya, a ganinsa nan ne kawai zai iya zuwa ba tare da ya yi tunanin aiki ba. Sai dai a yau gidan nata cike yake da mutane, wanda suke zuwa mata barka da sallah, shi kuma na ɗaya da ga cikin ɗabi'arsa, ba ya san zama a cikin mutane. Shi yasa ya dawo ɗakin nata ya zauna, yana karatun wasiƙar jaki. Ƙofar ɗakin aka turo haɗi da sallama. Jin muryar da ba ta Annaa ba yasa bai ko kalli inda ƙofar take ba, ya ci gaba da kallon inda yake kalla wato jikin taga, har yarinyar da Annan ta aiko kawo masa abincin ta aje a kan side drawer. “Me ki ka kawo ?” Kamar daga sama yarinyar ta ji muryarsa ta furta, wannan masifaffiyar muryar tasa, me sa cikin mutum murɗawa lokaci guda. Kuma nan take ita ɗin ma jikinta ya shiga rawa, saboda tsabar abar tsoro. “A... Anna, ce... ta... tace na kawo... maka abinci...” “Fita da shi!” “Amma ta...” “Ki fita da shi na ce, bana buƙata!” Cike da bala'i ya katseta, kuma har zuwa lokacin bai kalleta ba. Sum-sum ta ɗauki kayan abincin ta fita da su. “Gaskiya Anti Karima ba zan iya ba, na gaji da masifar bawan Allahn nan, shi kullum kamar bai san mutane ba, shekara nawa na shafe a gidan nan?, amma ko sunana ma bana jin ya sani...” Yarinyar ta faɗi rai a ɓace, yayin da ta iske yayarta a kitchen. Wadda take kitsa mata yanda za ta shawo kan Kuliya da ya daɗe a cikin ranta, tun sanda ta zo gidan Annan ta shafe shekaru kusan shida ta faɗa sansa, amma shi ko kallonta ma ba ta jin ya taɓa yi. “Ke dai Wallahi an yi wawuya, yanzu kina ga na miji irin wannan, za ki na wani cewa kin gaji?... ta ya zabki gaji ?... Namiji irin Kuliya ko yankar naman jikinki yake haƙuri za ki yi ki ci gaba da binsa...” Yanrinyar mai suna Siyama ta juyar da kanta gefe, har ga Allah ita ta gaji, tun shekaru uku baya take ta fama, amma ya kasa ganewa. Abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, ya kukan uwa mara amfani. “Ke ba ki ga irin yanda yake hidima da Anna ba ?, to ita da take marainiyarsa kenan, ke kuma idan ki ka zama matarsa ai sai yanda ki ka yi da shi kansa ma ba dukiyarsa ba!” Antin ta kuma faɗi, murya ƙasa-ƙasa. “Ke dai kawai ki ci gaba da dagewa, na tabbatar da za ki same shi... Kuma batun rashin sabo za ku saba, ba ki ji sunan sa ba ne ?, Kuliya manta sabo, ko ya san sabon ma mantawa da shi yake. Bare kuma ke da kunnenki ki ka ji Anna ta ce bai taɓa yin budurwa ba!” Kuliya dake zaune a ɗakin Anna yana kallo da kuma sauraren abun da suke ta cikin wayarsa, wani abu ne me kama da murmushi ya yi playing a cikin ransa. Amma ba za ka gane hakan ba idan ka kalli fuskarsa. Don tana nan cikin yanayinsa na shanu, babu fara'a bare annuri, fuska kamar kunun da ya so gardama. Wato shi za'a yi wa haka ?, bari su saka ido su gani, ko ƙoƙarin Siyaman zai yi aiki. *Unguwar Shuwarin, Maiduguri...* “Wallahi Kalisa nake faɗa miki... Kwata-kwata ba na samun kansa, amma tun da na yi amfani da maganin da Fati ta bani, sai na ga ya yi aiki, amma kuma bai jima ba ya wargaje... Ni na rasa yanda zan yi” Muryar Hajjara ta faɗi cikin damuwa, yayin da take bayyanawa ƙawarta Kalisa sirrin cikinta. Zaune suke a ɗakin gidan Kalisan, don bayan an sauƙo daga idi ta silale ta

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112