Chapter 53
Chapter 53
layin ya yi shiru, kasancewar babu kai kawon mutane, tun bayan da ya ganta yau, ya lura da wani irin farin ciki kwance a fuskarta. “Akwai wani abu na mussaman ne?” Ya yi tambayar da ba tare da ya kalli fuskarta ba, ita ma kuma ba tare da ta kalle shi ba, ta sunkuyar da kanta tana murmushi. “Bayan shuɗewar tsawon lokaci, yau na buga ball, shi yasa nake cikin farin ciki...” Ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, ya juyo ya kalleta, Kyakkyawan murmushinta shi ne yake ƙara bayyana masa kammaninta da Mommansa, zuwa yanzu yasan da cewa akwai sabo tsakaninsa da ita, kuma a yanzun ne ya kamata a ce ya tambayeta wani abu game da kanta. “Ammata a gidan ku da wa kike kama?” Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta yi murmushi. “Kana san sanin dangantakar ka da ni?” Cak, Raja ya tsaya, hakan ya sa ita ma Rabin tsayawa tana kallonsa. “Na san kana tunanin na haɗa alaƙa da kai. Ban sani ba ko kai ɗin jinina ne, amma dai a cikin familynmu babu wanda ya ɓata, da ace akwai wani wanda na san ya taɓa ɓata, ko ya bar gida, da sai na ce wata ƙila kai ne, ko kuma ka fito daga wajensa ne!” Ta zaɓi da ya ɓoye masa ne don har zuwa yanzu ba ta gama sanin waye shi ba, ta na buƙatar fara sanin waye shi, kafin ta bayyana masa cewar ta san shi da ɗan uwansa 'ya'yan abokiyar tagwaitakar Ummanta ne!. “Da Ummana nake kama, dan haka ko da zan yi zaton cewa kai ɗan uwanmu ne. Zan ce ka fito daga tsatson Umma ne!” Da ƙyar Raja ya haɗiye yawu, jin cewa Rabi'a ba 'yar uwarsa ba ce kamar yanda ta faɗa, sai dai kuma shi ya jita ne kawai, amma ya riga da yasan cewa ita 'yar uwarsa ce, alaƙar tsakaninsu ce bai sani ba, amma tabbas ita 'yar uwarsa ce!. KULIYA POV. A hankali ya turo ƙofar ɗakinta, a lokacin kusan ƙarfe goma na dare, wai a hakan ma ya dawo da wuri, don ya na so ya sameta ido biyu, amma cikin rashin sa'a sai ya tarar ta yi bacci kamar kullum, a jiya ya nema mata drivern da zai riƙa kaita makaranta yana dawo da ita, kuma kamar yanda ta buƙata ya sai mata kayan abinci da kuma kayan girki, don ita kaɗai za ta girka kayanta, shi ba zai iya cin jagwalgalen da za ta girka ba, yanzu haka shigowa ya yi don ya sanar mata da an kawo kayan girkin. Sai ya samu kansa da ƙare mata kallo daga nan inda yake, yanayin kwanciyarta kaɗai zai sa ka gane cewa mummunar kwanciya gareta, kanta a wani gefe da ban, haka ƙafafunta ma sun yi wata duniyar, blanket ɗin da ta rufe jikinta da shi ya yaye daga jikinta, ya yi wani wurin. A zuciyarsa ya yi murmushi ya na shigowa cikin ɗakin, tsayawa ya yi a jikin gadon yana kallonta, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, kafin ya kai hannunsa ya na gyara mata kwanciyar, har ya ɗora kanta a kan pillow ba ta farka ba, ya gyara mata ƙafafuwan na ta duk shiru kake ji, kamar wata gawa, ya janyo blanket ɗin ya rufa mata, sannan ya mata addu'ar da yake da tabbacin ba yinta take ba, ya miƙe ya na kashe wutar ɗakin, sannan ya fita. Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka, ya sauya kayansa, a sanda ya fito daga closet ɗinsa ya iske Ayra zaune a kan gadonsa, ya kamota ya ajete a inda ya saba kwantar da ita, shi kuma ya shiga ƙarasa aikin da bai samu ya ƙarasa a office ba. Allah ya sani a kwanakin nan ayyuka sun sha masa kai, ko lokacin kansa ba ya iya samu, don a yanzu haka ma ko abincin dare be samu ya ci ba, amma babu yanda zai yi, yana bawa aikinsa muhimmanci fiye da komai. RABI'A POV. Yini ta yi tana bawa Anti Saratu da Zara labarin ball ɗin da ta buga, haka ta kwana da wannan farin cikin fal ranta, da ga ta yi juyi za ta tuna da yanda ta buga wasa me kyau, sai wani kalar farin ciki wanda ba ta san daga inda yake ba ya lilliɓeta har ka. Washe gari weekend, don haka gidan kawai ta gyara, sannan ta shiga kiciniyar haɗa kayan suyar funkaso, kuma har washe garin wannan farin cikin bai bar ranta ba. RAJA POV. “Su kenan?” Ya tambaya a dake, yayinda yake kallon mutumin da ya kawo musu makaman da suka yi oder, mutumin ya zuƙi karan sigarin dake hannunsa sannan ya furzar yana gyaɗa kansa. “Su kenan” Sai shi ma Rajan ya gyaɗa kansa, ya na ɗaga kafaɗarsa. “Na fahimta” sannan ya waiga yana bawa su Zuzu umarni da su kwashi makaman su zuba a booth ɗin motarsu, har ya juya zai koma cikin motarsu mutumin ya katse shi ta hanyar faɗin. “Ɗan uwa wannan cikar fa?, Idan ba damuwa ina buƙata!...” Mutmin ya ƙarashe yana wa Rhoda wani irin shegen kallo, babu shiri Raja ya juyo ya na watsa masa wani masiffafen kallo, idanuwansa da suke a lumshe da sune ya buɗesu tar a kan mutumin, kuma ba jimawa da buɗesun, farin cikinsu ya rikiɗa zuwa ja, jijuyoyin kansa suka fito raɗa-raɗa, yau shi akewa magana kan ya bada ƙanwarsa a matsayin karuwa?, me wannan mutumin ya ɗauki kansa ne. A fusace ya yi kan mutumin, shi kuma ya riga da ya tsorata har ya shiga ƙoƙarin guduwa, Raja ya ci kwalar rigarsa da hannunsa na dama, sannan ya shiga naushin fuskarsa da hannunsa na hagu. Cikin su Zuzu da Jagwado da Rhoda babu wanda ya yi yunƙurin dakatar da shi, dukansa yake yana ƙarawa, kunnuwansa sun toshe, babu abun da yake ji sai maganar mutumin da ya yi a ɗazu, sai da ya farfasa masa fuska tukkuna Alandi ya ga kamar kashe mutumin Raja ke ƙoƙarin yi, don haka ya ƙarasa kusa da shi ya riƙe shi, amma bisa ga mamakin Alandin sai Raja ya ha kaɗashi shi baya. Hakan ya ankarar da Rhoda cewar Rajan ba a hayyacinsa yake ba, saboda haka ita ta ƙarasa kusa da shi ta dafa kafaɗarsa ta dama. “Zaid is okay!” Cak, hannun da Raja ya ɗaga don dukan mutumin ya tsaya a iska, ban da hucin ɓacin rai babu abun da yake, har wani datse haƙwara yake, gaba ɗaya ilahirin jikinsa sai rawa yake. Yakan shekara ransa bai ɓaci ba, amma idan ransa ya ɓaci abubuwa da dama za su ɓaci, sakin kwalar mutumin ya yi, hakan yasa ya zube a ƙasa ragwajab!, hannunsa na hagun da ya ɗaga ya daki iska da shi. Har lokacin idanuwansa a buɗe suke gaba ɗaya, sai huci yake, kamar wani wanda ya yi wasan tsere, juyawa Rhoda baya ya yi yana rufe fuskarsa, duk da iskar dake kai kawo a wurin shi gumi yake, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana ɗaga kansa sama. Kamar wanda aka tsikara kuma sai ya zabura ya faɗa cikin mota yana kwantar da kansa a kan dash-bot. Sai sauƙe ajiyar zuciya yake, a hankali kuma girman idanuwansa suka shiga raguwa. *No.181, Guzape, Abuja...* *80:40 AM* MISHAL POV.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112