Skip to content

Chapter 91

Chapter 91

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

wani ɓangare na Zaid, wani ɓangare na gaskiyar sa da take tutiyar ta sani, wani ɓangarensa da ɗai-ɗaiku ne cikin mutane kawai suka sani. “...Lion, umarni ya zo daga sama, duk yanda za ka yi ka yi don ka kawo ƙarshen wannan aikin, oga yace ba zai iya jira sama da haka ba, saboda haka sai ka san yadda za ka yi dan ka miƙo duka hujjojjin da ka haɗa!...” *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.* ZAID POV. Zaune yake a kan kujera ya na facing Rhoda, wadda ke daddana system ɗin dake kan cinyarta, hankalinsa rabi na kanta rabi kuma na ga wayar da yake ta jira, dan kuwa a jiya ya aikawa da office ɗinsu saƙon yana san magana da ogansu, ya san da cewa a yau ɗinnan za su kira, amma kuma ba zai iya jure zaman gidan suna cikin wannan halin shi da Adawiyya ba, ba zai iya zama a gidan ta na gudunsa ba, gwara ya ba ta space, ko ta samu damar sararawa a gidan, ina yado bayan ya koma sai ya amsa kiran. “Dude!... Zo ka gani!” Cewar Rhoda, mamaki mamaye da fuskarta, idonta kyar a kan system ɗin gabanta. Da sauri Raja ya miƙe ya dawo gefenta ya na kallon system ɗin. A jiya suka samo putage na CCTV camera ɗin dake layin da aka cillar da Adawiyya bayan da aka haike mata, ba ƙaramar wahala suka sha ba kafin suka samu putage ɗin, sannan kuma suna da tabbacin putage din shi ne zai kaisu ga karshen binciken da suka fara. A tare suka juyo suna kallon juna shi da Rhoda, bayan da vedion ya kai ƙarshe. “Usman?!” Rhoda ta tambaya tana dubansa. Nan take idon Raja ya kaɗa ya yi ja, babu abun da Rhoda ke iya hangowa sai wutar masifa da tashin hankalin dake ci a cikinsu. “Ba zan barsu ba!...” Ya faɗi ya na miƙewa, da sauri Rhoda ta kamo hannunsa tana maida shi inda ya miƙe. Kai ta shiga girgiza masa alamin a'a. “Zuwa yanzu case ɗin ya zama biyu Zaid... Ka fara miƙa hujjojji game da Alhaji Bala tukunna, idan an bamu izinin kamu, sai mu haɗa mu kamasu su duka!” Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga ya na cije leɓensa na ƙasa. “Kin tabbatar da haka ya kamata a yi?” Rhoda ta gyaɗa masa kai cike da tabbatarwa. *Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.* Habiba ce zaune a tsakar gida ta na dunduma jikinta da ruwan ɗumi, kwana uku kenan da aka sakota daga hannun 'yan sanda, kuma dukan da ta ci a hannunsa ne har yanzu be bar jikinta ba, dan ta doku ba ƙarya. Ita ta yi ma mamaki da suka sakota da wuri haka, duk da shi Ɗan Lami ma ko kwana be yi a wurinsu ba. Sallamar Saratu ta ji daga bakin ƙofa, hakan ya sa ta juya ta na kallonta. “Sannu Umma... jikin ne?” Habiba ta gyaɗa kai tana matsa ƙafarta. “Amarsu kenan, daga ina kike ne?” Habiban ta tambaya kamar ba ita ba, a sanda Saratun ta karɓi ƙyallen hannunta ta shiga dunduma mata jikin nata. Saratu ta yi murmushi. “Gidan su Farida na je, zuwa gobe za mu fara rabon cingam” Habiba ta gyaɗa kanta, zuwa yanzu ta fara shiga hankalinta, ta fara gane gaskiya da akasinta, a jiya Saratu ke faɗa mata cewar wai Rabi ta yi aure, kuma wannan me kamar tata ne ya aureta, sai kuma ganin nutsuwar da Ɗan Lami ya fara yi, ita ma ta sa ta shiga taitayinta, ta gane cewa Allah ɗaya ne, dan kuwa ga shi dai duk wannan abubuwan da ta yi ta yi, ba su hana Rabi auruwa ba, kuma duk wannan makirce-makircen da ta yi ta yi, ba su hana ikon Allah faruwa ba. Wata sallamar suka ji cikin wata murya me kama da ta Mama, cikin sauri kuma a tare suka kalli ƙofar gidan. Sannan cikin daƙiƙa ɗaya suka miƙe a zabure. Kallonta suke suna san su gane wacece. “Ni ce Umma, ni ce Mamanki!...” Cikin kuka Mama take faɗin hakan, tare da sakin jakar hannunta, hannu na karkarwa Habiba ta nuna Maman dake tsaye a gabanta. “Ma... mama... Mama!” Tsaye take a gabansu, jikinta ɗauke da cikin da ya fara fitowa, ga wasu ƙuraje da suka bai-baye mata jiki, ta wani kalar rame ta ƙwanjare, ta yi baƙi ƙirin da ita. Allah kenan, za ka yi ta saɓa masa ya na ara maka dama, rana ɗaya kuma idon ya tashi kamaka, sai ka gwammaci ba a hallici me kamarka a duniyar nan ba. Domin kuwa shi ya fi kowa iya kamu. *Don't be afraid to lose people. Be afraid of losing yourself by trying to please anyone around you* *** *No.86, Garki 2, Abuja...* RAJA POV. A hankali ya turo ƙofar shiga falo, bakinsa ɗauke da sallama. Cak ya tsaya, sakamakon ganin Rabi tsaye a tsakiyar falon, hannayenta harɗe a ƙirjinta, ta kafe shi da wani irin kallon tuhuma, duk wata ƙwarin gwiwa da ya zo da ita dan ya mata wasu tambayoyi game da abun da ya faru da ita sai ya ji ya gushe, kallon da take masa yana ƙarasawa ya ji ya muzanta, don ita ba ta kallonsa a matsayinsa miji gareta ko yaya, kallo take masa a matsayin ɗan daba, kuma makashi. Wani yawu ya haɗiya, sannan ba tare da yace mata komai ba ya ɗauke idonsa a kanta ya shiga ƙoƙarin nufar ɗakinsa. Sai de me?, tsulum ya ganta tsaye a gabansa, ta na ci gaba da kallonsa cike da tuhuma. “Waye kai?” Tambayar ta doka wata ƙatuwar ganga me amon gaske a cikin kan Zaid, ya kafeta da idonsa, amma ya kasa ce mata komai. “Zaid! Waye kai?” Yawu ya haɗiya ya na faɗin. “I'm a goon!” Kanta ta girgiza tana sauƙe hannayenta daga ƙirjinta. “I mean real you... Waye kai!” Ta kuma maimaita masa tambayar, hakan ya saka zuciyar Zaid cikin kokwanto, to me take nufi da waye shi?, ko de ta gano wani abu a kansa ne?, ina ba zata gano komai ba. Dan haka ya haɗiye yawu yana faɗin. “I am a killer and drug trafficker. I'm goon” Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa, sosai rungumar ta ba shi mamaki, idonsa ya lumshe sannan ya buɗe, kusan shuɗewar muntuna biyar, kafin ta sake shi tana kallon fuskarsa. “Akwai wani rubutu da na taɓa karantawa. A rubutun an ce, idan har ka rungumi mutum na tsawon muntun biyar, to za ka fara yarda da duk abun da zai ce, amma har yanzu ni ban yarda da kai ba. I will ask you for the very last time... Who are you Zaid” Raja ga haɗiye wani kakkauran miyau me ɗaci, sannan ya lumshe idonsa ya buɗesu a kanta, kana ya amsa mata da: “Zaid Aliyu... Department of state service (DSS) officer!” *No.181, Guzape, Abuja...* MISHAL POV. “Yaushe za mu je gidan Anna?” Ta tambaya ta na saka kayan Kuliya da ta wanke yau da safe a cikin loka. Kuliya dake zaune a bakin gado yan danna waya ya kalleta. “Me ya faru?” Ya tambaya. Mishal ta girgiza kai ta na saka wata rigar cikin lokar.

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112