Chapter 106
Chapter 106
amma har zuwa yanzu bai farfaɗo ba. Ita kanta ba ta san in da kanta yake ba, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kawai tana nan ne, amma hankalinta ba ya tare da ita. Tun a ɗazu da safe da suka gama zirga-zirga. Zaid yace mata ta zauna,shi zai tsaya a kan komai. Kuma tun lokacin take zaune a nan ɗin. Babu yanda Zaid ɗin be yi da ita ba kan ta ci abinci, amma fur haka taƙi. Ko sallah ma ba ta jin ta yi. Gani take kamar Aliyu tafiya zai yi ya barta, kamar shi ma zai bi Abbanta, Mamanta da yayanta. Wata ƙila ita ba ta da sa'ar zama da kowa a rayuwa, haka Allah ya tsara tata rayuwar, ba tare da yin zama me ɗorewa da makusantanta ba, wata ƙila haka za ta ƙarar da rayuwarta cikin kaɗaici. A hankali Zaid da ya dawo daga masallaici ya zauna ɗan nesa da ita. Kallonta kawai yake yana san sanin me ya kamata ya yi?. Ga ɗan uwansa a cikin wani hali na mutuwa ko rayuwa, ga kuma matarsa da ke cikin tashin hankalin rasa mijinta, shi kansa idan za'a rarrasheshi so yake, dan ba ya so Aliyu ya sake tafiya ya barshi, ji yake kamar ya saka igiya ya ɗauresu da juna, gudun kada wani abun ya kuma zuwa ya gifta a tskaninsu. Sai de kuma a matsayinsa na namiji, kuma babba, dole ne ya haɗiye nasa tashin hankalin, ya san hanyar da zai bi dan ganin ya kwantar da hankalin matar ƙaninsa. Bakinsa ya buɗe zai yi magana, idonsa ya sauƙa a kan Rabi'a da Rhoda da suka shigo corridor ɗin ɗakunan. A hankali Rabi ta yi a jiyar zuciya bayan ganin mijinta cikin ƙoshin lafiya, sai de hankalin nata be gama kwanciya ba sai da ta tafi da gudu ta yi wurin da yake, miƙewa tsaye ya yi yana kallonsu. Rabi ta manta da Rhoda dake bayanta, da kuma Mishal ɗin da hamkalinta bai ma kai kanta ba. Ta yi saurin rungume mijinta tana shafa bayansa. Shi ma riƙeta ya yi da kyau a jikinsa, yana jin kamar ya fashe mata da kuka. A hankali ta sake shi tana ci gaba da duba jikinsa. “Me ya faru?...” Ta tambaya tana yawatawa da idonta a kewayen wurin da suke, bata rufe bakinta ba idonta ya sauƙa a kan Mishal dake zaune a kan kujera, ta sunkuyar da kanta ƙasa, gashin kan nata a yamutse, ga jinin da ya fara bushewa a gefen fuskarta. A kiɗime ta zauna kusa da ita tana rungumota jikinta. Mishal na jin kanta ya sauƙa a kafaɗar Rabi ta saki kukan da yake cin ruhinta tun safe. Kukan da Mishal ɗin ke yi ne ya ƙara karya zuciyar Rabi. Mishal na rungume a jikinta ta juyo da kanta ta kalli Zaid dake tsaye yana ƙoƙarin hana hawayensa zuba. “Raj! Me yake faruwa wai?” Zaid ya ɗan kawar da fuska yana ɗaga kafaɗarsa. “Aliyu ne ba shi da lafiya” Sunansa kawai da ta kira ne ya ƙara karya zuciyar Mishal, ta ƙarawa kukanta ƙarfi tana ƙanƙame Rabi a jikinta. Da Zaid ya ga ba zai iya ɗauka ba, sai ya yi wa Rhoda alama da ta biyoshi, ya kama hanyar barin corridorn. Duk yadda Rabi ta so Mishal ta kwantar da hankalinta ya gagara. Kukan ma da ƙyar ta sakata ta dena shi. Sai hawayen da take gogewa. Sai wajajen ƙarfe takwas Zaid da Rhoda suka dawo. Zaid ɗin ya umarci Rhoda da ta ɗauki Rabi da Mishal ta kaisu gidansa, kuma ita ma kar ta tafi, ta zauna ta kwana tare da su. Kamar wata gawa haka Rabi ta miƙar da Mishal ta shiga janta zuwa waje, dan bata ma san inda take saka ƙafarta ba, duk inda aka jata bi take kawai. Rhoda da Mishal suka shiga mota, yayin da Rabi da Zaid suka tsaya daga can nesa da su. Rabi ta goge ƙwallar idonta ta tausayin mijinta da kuma ƙanwarta, ta kai hannunta ta dafa kafaɗar Zaid ɗin ta dama. “Ka ci abinci?” Kansa ya juyo ya kalli fuskarta ta cikin hasken fitilun dake wadace a harabar asibitin. Nan take idon nasa ya cika da ƙwalla. Sai ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya na barin hawayen fita daga inda ya tsaresu tsawon ranar. “Ban ci ba” Ya amsa mata a raunane. Rabi ta ci gaba da kallonsa, tana jin ina ma tana da damar da za ta buɗe zuciyarsa, ta cire wannan damuwar da yake ciki. Ƙwalla ta kuma gogewa tana faɗin. “Na ga ko wanka ma ba ka yi ba. Amma ya kamata ace ka ci abincin” Sai ya ɗago da lumsassun idanuwansa ya ɗorasu a kanta yana ɗage kafaɗarsa ta dama. “Adawiyya ta ya kike tunan zan iya cin abinci a irin wanna yanayin da nake ciki, ni yunwar ma kanta ba na ji. Kaina ne kawai ke min ciwo, ji nake kamar zai tarwatse!” Sai ta ɗan yi tattage tana riƙe kan nasa. “Ka ga ba?. Yunwar ce ta saka mata ciwon kan, ka daure ka taɓa wani abun, sai ka sha magani, Aliyu ba zai ji daɗi ba idan har ya ji cewar baka ci abinci ba!” Kiran sunan Aliyin ya sa wata ƙwalla ta ƙara sauƙowa daga idonsa. Rabi ta saka hannyenta ta share masa duka ƙwallar. “Na san kana da dauriya da kuma juriya, ka ƙara kan wadda kake da ita, Allah zai tashi kafaɗun Aliyu!...” Da sauri ya saka hannyensa biyu ya kewaye waist ɗinta yana janta jikinsa tare da fashewa da kuka mara sauti. Ita ma Rabin kukan take. Tana shafa ƙeyarsa. Sun jima a haka kafin Zaid ɗin ya saketa ya na share ƙwalla. “Ki san yanda za ki kwantarwa da...” Sai kuma ya yi shiru, dan sunan nata ya kwanta masa. Rabi ta kai hannunta na hagu ta kama chain ɗin wuyansa, sannan ta yi amfani da hannunta na hagu ta kama wuyan rigarsa tana janyo shi gaba, kafin ta saka sarƙar a cikin rigar tasa tana faɗin. “Mishal?” “Eh Mishal... Ko sallah ba na jin ta yi, dan Allah ki kula” Kanta ta gyaɗa tana sharar tata ƙwallar. “Na je na an min gwaji, kuma na ci, dan har training mun fara!” Bai iya ce mata komai ba, sai kansa da ya gyaɗa, daga haka suka yi sallama, shi ya koma zuwa cikin asibitin. Ita kuma ta nufi motar Rhoda. Ko da suka isa gidan, wanka tasa Mishal ta yi, kafin ta bata wasu kayan cikin kayanta tace mata tasa. Sawar ta yi, sannan Rabi tace mata ta yi sallah tana zuwa. Sallar ta fara kafin Rabin ta dawo. A falo ta iske Rjoda kwance a kan kujera tana waya da Zakar, yayin da take sanar masa halin da suke ciki a yau. Ba ta ce mata komai ba ta wuce kitchen. Ta shiga kiciniyar girka musu abinci. Kasancewar babu wani isasshen lokaci, ya sa ta yi gaggauwar girka musu jallof ɗin taliya. Duka ta jiye musu it a tray, sannan ta fito da ita ta aje a falo, zuwa lokacin Rhodan ta gama wayar tana zaune tana danna wayar tata. “Bari na kira Mishal...” Ta faɗi tana nufar ɗakinta. Ko da ta shiga sai ta iske Mishal ɗin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112