Skip to content

Chapter 56

Chapter 56

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

sani ba, ko wani kallo za ta masa bayan wannan abun da ya faru?, Oho. Rhoda dake cikin farin ciki da ɓacin rai a lokaci guda ta dafa kafaɗarsa. Ta na cikin farin ciki jin yau Raja ya rabu da Uchechi, ya kuma bayyana sirrin zuciyarsa kan abun da yake ji game da Rabi'a, ranta kuma ya ɓaci ne saboda nasa ran ya ɓaci. A hankali ya sauƙe hannunsa daga kan fuskarsa, sannan ya juya bayansa da sauri, ya kalli Rabi dake a sanƙare a wurin, kamar wata mutum-mutumi, kamar wadda aka manne mata ƙafafunta da glue me ƙarfi, kuma kamar wadda ta cillar da hankalinta a hanya, haka take jin kanta, duniyar ta mata shiru, babu abun da take ji sai muryar Raja cikin faɗin “She is my wife to be!”, anya kuwa tana cikin hayyacinta?, kamar fa ta haukace ma, yau in ba wadda ta yi hauka ba, waye yake jin abunbda babu shi a zahiri, ko kuma dai iskokai ne suka shiga jikin Rajan?, Oho, a'a abun zai fi kyau ace jikinta suka shiga ba nasa ba. Kanta ta ɗaga ta kalli fuskarsa, jin yana kiran sunanta. Kallonta kawai yake, ya kasa cewa komai, don ya ma rasa abun da zai faɗa mata, sai kawai ya juya ya tsayar mata da mota, sannan ya kamo hannunta ya sakata a cikin motar, don ya ga kamar bata cikin hayyacinta. A kan idonsa motar da ya sakata ta bar wurin, sannan ya dafe kansa cikin neman sauƙi, a bisa tsautsayi idonsa ya sauƙa kan wata rumfar me ƙosai, wutar da ya yi arba da ita tana ci a cikin murhunta ta tuno masa ƙiyayyarsa da wuta. *2008.* *Gidan Maman Rhoda, Kano...* *08:30 PM.* “Zaid miƙo min kwanon can!” Cewar Maman Rhoda tana nunawa Zaid kwanon dake ɗauke da farfesun kifi, Zaid ya ɗauki kwanon sannan ya miƙa mata, zaune suke a kan carpet ɗin dake falo, Rhoda na daga gefen Zaid, yayin da Maman Rhodan ke facing ɗinsu, girkin ranar da suka yi ne zube a gabansu, yayin da suna shirin cin abincin dare. “Mom ni kifin nake so kawai” Cewar Rhoda tana shagwaɓe fuska, Maman Rhoda ta wurga mata harara. “An ƙi a baki kifin, da ci kike ?, Kifi na Zaid ne kawai” Zaid ya kunshe dauriyarsa ya na shafa kanta, kasancewar ta jingina da shi, Maman Rhoda ta zubewa Zaid gaba ɗaya kifin, sannan ta bawa Rhoda tata shinkafar babu kifi sai miyar kawai. Rhoda ta turo baki tana ture abincin, sannan ta miƙe ta bar falon da hawaye. Nan da nan Zaid ya shiga damuwa, don Allah ya sani ba ya son ɓacin ran 'yar ƙanwar tasa, don haka ya miƙe, hannunsa riƙe da kwanon abincin nasa. “Zaid ina za ka?” Ba tare da ya juyo ba ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama sannan yace. “Abincin zan je mu ci” “Da ka rabu da ita kawai” “Ba zan iya cin abincin ba tare da ita ba!” Ya amsa mata a lokacin da ya ke ƙarsa fita daga cikin falon, Maman Rhoda ta girgiza kanta tana murmushi, soyyayar Zaid da Rhoda sai kallo, ko ka shiga tsakaninsu kai ne za ka ji kunya. “I'm sorry Cuzie” Zaid ya faɗi a karo na biyu ya na kallon Rhoda, wadda ta cunkune tana wani kawar da kai, wai ita a dole an ɓata mata rai, tana zaune a bakin gadonta, yayin da Zaid ɗin ke zaune kusa da ita. Ya na murmushi ya aje kwanon abincin a kan cinyarsa yana buɗe kifin, ya guntsuro tsoka ya haɗa da lomar shinkafar, sannan ya kai mata saitin bakinta, kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta buɗe bakin ya saka mata. “Story time!...” Sai ta juyo tana kallonsa da kyau, ta harɗe ƙafafunta a kan gadon, tana buɗe duka kunnuwanta dan ta ji labarin da zai bata. Ta san labaran Zaid, babu na yarwa. “Wani Gayene ya zo Wajen Budurwarsa. Saiya Kira Yaro Yace mai; Kai je Gidannan Kace Sani Striker Na Kiran Hassana. Yaro Ya Antaya,yace wai Ana kiran Hassana. Babanta Yace waye Ke Kiranta? Yaro Yace Sani Striker. Sai Babanta Yace; Je Kace Isah Defender Yace Bata Zuwa” (Labaran musha dariya). Yana ba ta labarin yana kai mata lomar abincin haɗi da kifin, yana kaiwa ƙarshen labarin Rhoda ta tintsire da dariya. Abincin ya ci gaba da bata ya na bata wasu labaran, sai da ta ga ta kusa cinyewa, sannan ta karbi kwanon, ita ma ta shiga ba shi a baki. Kamar daga sama suka ji an banko ƙofar falonsu, hakan yasa ba shiri suka miƙe suka bazama zuwa cikin falon. Abun da suka gani ya bala'in gigita duniyar ko wannensu. Maman Rhoda ce yashe a ƙasa, Bala ya danne mata kai, ga sauran yaransa su Garuje tsaye a bayansa. Bala wani me kuɗi ne a unguwar kusa da ta su Maman Rhoda, ya na bawa mutane bashin kuɗi, musamman ma mata, sannan ya kan ƙawarawa mutane da kuɗin ruwa me yawa, idan kika ka sa biyan bashin kuma sai ya nemi ya fanshe a kanki, ga shi da tara yara 'yan daba, kasancewarsa ɗan uwan sanata ya sa ake ɗaga masa ƙafa ya na cin karansa babu babbaka. Lokacin da Maman Rhoda za ta biyawa Zaid kuɗin makaranta gaba ɗaya har zuwa lokacin da zai gama, kuɗaɗen hannunta ba su da yawa, hakan ya sa ta karɓi bashi a hannun Bala, suka yi da shi kan za ta riƙa biyansa da kaɗan-kaɗan. Kwana nan kuma sai ya bijiro mata da maganar ta ba shi kanta kawai, ita kuma sai ta nuna ƙin amincewarta, harda marinsa a yammacin jiya. Shi ne kuma yau ya iyo musu dirar mikiya a wannan daren. A cikin wannan daren Bala ya yiwa Maman Rhoda fyaɗe a kan idon Zaid da Rhoda, waɗanda ke riƙe a hannun yaransa su Garuje, sai da Zaid ɗin ma ya yi ƙoƙarin kaiwa Balan farmaki amma Garuje ya riƙe shi tare da buga kansa a jikin bango, hakan ya haddasa masa jiri da fashewar goshi. * Sosai Maman Rhoda take kuka, Zaid da Rhoda rungume a jikinta, yayin da suke tsaye a harabar police station, bayan da ta kawo ƙara kan zalincin da aka mata, faɗar sunan wanda take ƙara ya sa 'yan sandan korarta har da haɗa mata da duka. Babban tashin ha kalinta shi ne yanda Rhoda da Zaid ke cikin damuwa, ba za ta iya ɗaukan baƙin ciki irin wannan ba, hakan yasa ta fita wajen police station ɗin, ta siyo fetir da ashana, ta ture Zaid da Rhoda gefe, sannan a kan idon Zaid da Rhoda da kuma sauran jama'ar station ɗin. Maman Rhoda ta ɗaga jarkar fetir ɗin nan ta tittila a jikinta, sannan ta kunnawa kanta wuta, Rhoda na kuka tana fisge hannunta daga ruƙon da Zaid ya mata, yayin da wannan wutar ke ci a kan idon Zaid, komai na cikin kansa ya taɓu, tsoron wuta ya kama shi, ya zamana ba shi da wata abokiyar gaba kamar wuta. Don a lokacin suma ya yi, 'yan san dake da imani a wurin ne suka temaka musu, ita kam Maman Rhoda babu abun da ya yi saura a gawarta, ta ƙone ƙurmus, Zaid kuma ya suma, Rhoda kuma sai kuka

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112