Skip to content

Chapter 55

Chapter 55

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

lambar wani masanin kan na'ura me ƙwaƙwalwa dan ya binciko mata lambar Kuliya. Jim kaɗan sai ga saƙo ya shigo wayarta, kuma ba jira ta aika masa kira. Daga can DSS Headquarter, Kuliya dake tsaye a ɗakin horo ya na hora wani me laifi ya ji kamar wayarsa na vibrating, hakan ya sa ya saki wayoyin lantarki dake hannunsa ya juya ya fice daga ɗakin, don ya samu ya amsa wayar, abakin ƙofar ɗakin ya iske Sharon, don haka ya yi mata alama da ita ta shiga ta ci gaba. Ganin baƙuwar lamba ya sa shi ɗan jinkirtawa kafin ya ɗaga, kuma kamar ma ba zai ɗaga ɗin ba, sai da kiran ya shigo a karo na uku sannan ya ɗaga. Tun daga jin muryarta ya ganeta, hakan yasa suka gaisa a mutunce, kafin dalilin kiran ya taso. “Magana ce a kan Mishal, ɗazu kakarta Jadda ta kirani. Wai ta na so ta san inda aka kai mata jikarta. Na san ko ni ban faɗa mata ba, za ta iya nemo address ɗin gidanka, Jadda bata san zaman lafiya, don haka ko da wasa kada ka bari ta ɗauki Mishal daga cikin gidanka. Saboda ko a sanda tana ƙarama Abubakar be bata renonta ba, bare yanzu da ta girma, zamanta a wurin Jadda ba ƙaramar matsala ba ce!” Kuliya ya ɗan yi jimm, to a kan me ma zai bari wata Jadda ta ɗauketa?, ai a yanzu ba ya jin ko ita kanta Nimran za ta iya raba shi da Mishal, Mishal amanarsa ce, babu yanda za ayi ya bar wani abun cutarwa ya sameta, zai yi duk iya iyawarsa don ganin be bari an cutar da ita ba. Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya amsa mata da. “Insha-Allah” Daga haka ya mata godiya ya sauƙe wayar. *Joy Emodi CI St.* RABI'A POV. Tafe suke ita da Raja a kan titin, hira yake mata jifa-jifa, sama-sama take ba shi amsa, don yau gaba ɗaya tunaninta ba ya jikinta, tunaninta ya lula kan maganarsu da Yaya ta jiya. _“Rabi'a da ace kina sona, da za ki bi abun da na faɗa. Saboda Allah ya za'ayi ki riƙa kula wani da sunan me kamarki, kika sani ma ko ɗan satar mutane ne, ni dai gaskiya ki dena kula shi. Dan har ga Allah ba na so!...”_ Kalamansa gareta kenan a jiya da daddare da ya zo fira, ita ba ta ɓoye masa komai game da Raja, duk ranar da suka haɗu da shi sai ta faɗa masa sun haɗu da wannan me kamarta tata, abun da ko Anti Saratu ba ta faɗawa ba, shi ne; Raja na kama da ita, kawai ta faɗa mata cewar suna mutunci da shi. “Ammata?” Ya kira sunanta a lokacin da suka fita kan babban titi, juyowa ta yi ta kalleshi, a zahirin gaskiya ba za ta iya dena kula Raja ba, don tana da tabbacin shi ɗan uwanta ne, alaƙar jinin da suka haɗa ce ta sa ba za ta iya haƙura da shi ba, don a yanda take ji za ta iya rabuwa da Yaya a kan Raja, kuma akwai wani abu a kan Rajan dake motsi a ƙasan zuciyarta, duk da ta na amfani da duka ƙarfinta wurin danne shi, don bisa ga dukkan alamu hakan ba me iyuwa ba ne. Ko kafin Raja ya kuma faɗin wani abu, wata motar taxi da ta tsaya a bakin titin ta ɗau hankalinsa, hakan ya sa ya ci gaba da kallon motar har zuwa lokacin da aka buɗe gidan baya na motar, Uchechi ta fito, fuskarta ɗauke da wani abu me kama da fushi da kuma ɓacin rai. Hakan yasa fuskar Raja rikeɗewa zuwa mamaki, yaushe ta zo?, wa ya bata address ɗin inda yake?. Ganin yanda Raja yake kallon bayanta ya sa Rabi'a juyawa, kuma tana juyawar idonta ya sauƙa a kan wata budurwa dake tsaye kisabda wata motar taxi. Kallo ɗaya za ka mata kattabatar da cewa ita Cristian ce, saboda yanayin shigarta. Amma kuma ita Raja yake kallo ?, ko me?. To mi ye haɗinsa da ita?. Kuma ga shi ma ta ahiga tunkarosu. Ba ta ankara ba ta ji hannun Raja cikin nata, sanna a hankali ya ja ta ya mayar da ita zuwa bayansa, dai-dai da isowar Uchechi gabansa, kuma tana zuwa ta ɗaga hannunta sama ta shararawa Raja mari. Har saida ya karkatar da fuskarsa, Rabi ta tsorata sosai, ido waje take kallon gefen fuskar tasa. Zuwa lokacin har Uchechi ta fara hawaye, ta nuna Raja da ɗan yatsa ta na faɗin. “Macuci. Ma ci yi amana, da ma ashe yaudarata kake?. Saboda wannan 'yar talakawan kake yaudarata?” A hankali Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya juyo ya zuba lumsassun idanuwansa a kan Uchechi. Kafin ya furta abun da ya wargazo da duniyar Rabi da kuma Uchechin zuwa ƙasa. “Uchechi! She is my wife to be. So show some respect!” Bakin Rabi ya faɗo a har ƙasa, kallon bayan Raja kawai take tana ƙarawa, ai ba ta ganin fuskarsa, wata ƙila ma daga wani wurin maganar ta fito, ba daga bakinsa ba, inaa, wai Raja?, kai! Wallahi da sake, ba shi ya faɗi wannan zancen ba. Uchechi ta fashe da matsanincin kuka tana cin kwalar Raja, dai-dai da isowar su Rhoda da suke binsu a baya ita da Alandi, dom cewa suka yi bari su je gulma, sai kuma Allah ya sa suka ci karo da wannan faɗan. “Ke sakar shi!...” Rhoda ta faɗi tana yin kan Uchechi, Raja ya ɗaga mata hannu alamun ta dakata. “Ni za ka ci amana Raja?, Ni?, Ni Raja?, Idan ka isa Yesu ya kwashe min albarka!, A kan wannan ƙazamar za ka gujeni?...” Tass!, ka ke ji, Raja ya wanke fuskar Uchechi da mari, hakan yasa ba shiri ta sake shi tana dafe fuskarta setin inda ya mara, hawaye wani na bin wani a kan fuskarta, ta ɗago da idanuwanta ta kalleshi. Ba ƙaramin tsorata ta yi ba, ganin idanuwan Raja buɗe a kanta, wani abu da za ta iya cewa tsawon zamanta da shi ba ta taɓa gani ba, a ko da yaushe idanuwansa kusan a lumshe suke, amma yau ga su buɗe a kanta, sun yi jajawur, jikinsa har karkarwa yake dan ɓacin rai, mutanen dake wucewa har sun ɗan fara tsayawa tagumi, duk da layin babu mutane sosai. ”Don't you hare what i just said?, I said that she is my wife to be!, You better respect her before i injured you!” Kuka sosai Uchechi ke yi, haka ta juya da gudu ta shige motar da ta fito daga ciki, ba ɓata lokaci motar ta bar wurin, ba ta taɓa tabbatar da cewa Raja ba ya santa ba sai yau, ta gaji da abun da ya ke mata, don haka za ta sakar masa mara ya yi fitsari, babu ita babu shi, za ta jurewa komai da zai mata amma banda cin zarafi. Ta haƙura da shi har duniya ta naɗe. Da sauri Raja yake sauƙe nufashi, ya ɗaga hannunsa ya dafe goshinsa, zuciyarsa na bugawa da sauri, be so ya bayyanawa Rabi ta ji wannan sirrin zuciyar tasa a yau ba, ba yau ya kamata ta sani ba, ba a irin wannan lokacin ya kamata ta

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112