Chapter 3
Chapter 3
Kuma ba ita kaɗai ce ke sanye da irin kayan ba, dan gaba ɗaya ɗaliban dake kai kawo a harabar makarantar sanye suke da irin kayan jikin nata, maza ne kaɗai ke saka wando, kuma shi ne abinda ya banbantasu, hakan ke nuna cewa kayan shi ne uniform ɗin makarantar. Tafiya ta fara cikin takunta na wanda ƙuriciya bata gama saki ba. “MISHAL!, kin manta abincin ki....” Muryar drivernta malam Ali ta faɗi da ga cikin motar.Tsayawa ta yi da tafiyar, sannan ta juyo ta kalli motar, kafin ta fara takowa zuwa wurin motar. Ba tare da ta ce masa komai ba, ta buɗe gidan baya ta ɗauki lunchbox ɗin nata, ta rufe ƙofar motar, kana ta ɗaga masa hannu alamun bye, sannan ta yi gaba. Malam Ali ya girgiza kai yana murmushi, a cikin ransa ya na wa Mishal ɗin fatan shiryuwa, ita duk gari ana azumi amma banda ita, zai iya cewa tun da aka fara azumin ma bai fi guda goma ta yi ba, da ya mata magana ma sai tace masa wai akwai wahala haɗa azumi da zuwa makaranta. Duk inda ta wuce sai an bita da kallo, amma ita ko a jikinta, dan bata damu ba, saboda wannan ba shi ne karo na farko da aka saba bintada kallon ba, wasu kallonta suke cikin tsoro saboda sanin halinta, wasu kuma cike da burgewa saboda sanin jarumtarta, wasu kuma suna kallonta ne cikin jin haushi, wata ƙila saboda faɗa ya taɓaa haɗasu. Bata ko kalli kowa ba, duk da tasan cewa kowa kallonta yake. Har ta kai ƙofar class ɗinsu, ta saka ƙafarta a cikin ajin, sai kuma ta dawo da baya, ta gyara tsaiwarta tana kallon wannan yarinyar. Yarinyar da ke aikin shara a makarantar tasu, ba yau ne karo na farko da ta fara ganin yarinyar ba, hasalima tafi wata shida tana ganin gilmawarta a makaranta. Ba wannan ne yasa take kallonta ba, kawai rayuwar yarinyar ce ke bata tausayi, dan da alama yarinyar na cikin halin ƙuncin rayuwa, ita kuma haka Allah ya yi ta, duk da baƙin halinta da rashin jin maganarta da wasu ke gani, Allah ya hallici zuciyarta da tausayin wanda bashi da shi, haka Allah ya saka mata tausayin yarinyar. Duk da ba za ta iya kiranta da yarinya ba, saboda da alama ta girmeta, saide bata kai sa'ar Akinta(Yayanta) ba. Da alama ma ita yarinyar bata lura da ita ba, dan moping ɗin floor take bil haƙƙi da gaskiya. Ba tare da ta yi komai ba, ta juya ta shiga ajin nasu. Malamin geography ne a ciki, kuma tana shiga ajin ya yi tsit!, kallo ya dawo kanta kamar kullum. Ba tare da ta damu ba ta nufi seat ɗinta. “Ke Hafsat Muhammad Auwal!” Uncle ɗin geographyn ya daka mata tsawa, ta juyo ta kalle shi da sauri, idonta babu ko da ƙwayar tsoro a ciki, dan bata saba jin tsoron kowa ba, kowa gani take kai kai ɗaya yake da ita. A hasalle Uncle ɗin ya cillar da littafin da ke hannunsa, ya ɗauki wata cane ya yi kanta, yana ƙarasawa kusa da ita ya ɗaga bulalar sama zai zabga mata ta kai hannunta ta riƙe bulallar. “Babban kuskuren da za ka yi shi ne duka na da wannan bulalar, dan Wallahil Azim ka kuskura ka dakeni sai na rama” Ta ƙarashe tana wancakalar da bulalar, Uncle ya haɗiye wani abu a maƙoshinsa, yana ci gaba da kallon yarinyar, Ba ƙaramin jajircewa ya yi ba da har ya iya yunƙurin dukan yarinyar, dan malamai da dama na yawan bada labarin yarinyar a staffroom, wasu da ga cikinsu ma kan ce wata ƙila aljana ce, dan normal ɗan adam ba zai iya abin da yarinyar nan ke yi ba. Ta addabi kowa a makarantar, watan da ya wuce har wani malami ta mara, ɗalibai kuwa kullum sai an samu wanda zai kawo ƙararta. Sai da ta aika masa harara, sannan ta aje jakaarta a kan desk, ta zauna tana baza ƙwayoyin idonta a cikin ajin, hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa. Sai da ta yi ƙwafa sannan ta buɗe jakarta ta ɗauko littafi ta gyara zamata ta shiga kwafar note ɗin da uncle ɗi ya ci gaba da yi. * “Wai me yasa ke bakya azumi kamar 'yan uwanki musulmai” Muryar Angelica yarinyar Mishal ta faɗi a sanda aka fito break, dan sai dai a kirata da yarinyarta, saboda duk wani aike ko bautar Mishal ɗin ita Angelican ce ke yi. Kuma kaf makarantar Mishal bata da ƙawa ko ɗaya, ita ma Angelican ita ta cuso kanta gareta. Mishal ta ture flask ɗin gabanta tana miƙe ƙafa. “Saboda bana san wahala, bazan iya haɗa azumi da zuwa makaranta ba” Ta bata amsa cikin harshen turanci, kamar yanda itama Angelican ta mata maganar cikin harshen turancin, kasancewarta baturiyar Engiland. Aiki ne ya kawo mahaifinta zama a nigeria. “Amma su Rashida su na yi” “Baki ji me nace ba ?” Sai Angelica ta girgiza kai, tana kai loma bakinta. “Kai ka ga wata balarabiya” Wani sabon ɗalibi da ya fara zuwa makarantar ya faɗi yana kallon Mishal da ga nesa, abokin nasa da ake nunawa Mishal ɗin ya juyo ya kalli wurin, kuma a lokaci guda idonsa ya zare cike da tsoro da kuma mamaki. “Kai!!, karfa kace min santa kake!” Sabon ɗalibin me suna Abdul ya yi murmushi. “Ka jika da wani zance, waye zai ga wannan kyakyawar ya ce ba ya so, Allah da da na ganta na ɗauka balarabiyace” Abokin ya haɗiye wani abu. “Abdul da ka je ka ce kana san wannan, gwara ka samu Madam Joke (Malamarsu ta Math) ka ce kana santa” Abdul ya ƙyaƙyale da dariya. “Kai ana gabar kana yamma, me zan yi da wata Joke arniya kuma tsohuwa, ga kyakkyawar baby a nan” “Idan za ka ka bar jirana, tun da na haneka baka ji ba, idan ka je ita zata maka bayani....” Kuma yana kaiwa nan ya fita da gudu ya bar wurin zaman cin abincin nasu. Abdul ya bi bayansa da kallo yana dariya, ya gyara tie ɗin wuyansa, sannan ya gyara stocking ɗin wandonsa, ya nufi wurin da kyakkyawarsa take. “Ke rabu da assignment ɗin nan, wallahi bazan yi ba, in yaso idan mun haɗu da python ya kasheni” Cewar Mishal Pytho shi ne sunan da suke kiran malamin math ɗinsu da shi, kuma sunan ya samo asaline tun sanda suna jss3, lokacin da ya koyar da su Pythagoras rule. “Ke idan ki ka ƙi yi ba damuwa, ni fa ?, wata ƙila ya karyani, gwara na je na yi” Angelica ta ƙarashe tana miƙewa tare da barin wurin. Mishal ta gyara zamanta tana aika lomar abincinta baki, kafin wata murya ta daki dodon kunnuwansa. “Salam!” Kuma kafin ta ɗago da kanta ta amsa sallamar, har wanda ya yi sallamar ya ja kujerar da Angelica ta tashi ya zauna. Mishal ta ɗan kalleshi na wasu sakkani. Bata taɓa ganinsa a makarantar ba, hakan kenuna mata cewar sabon zuwa ne, dan in ba baka ba,babu yaron da ya isa ya yi gigin mata magana kaf brickhall. “Ba kya azumi ne na ga kina cin abinci?...” Bata amsa shi ba, sai kallonsa da ta ci gaba da yi da olive
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112