Skip to content

Chapter 108

Chapter 108

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

kiran nurses. Tare da nurses guda uku suka dawo, su suka dakatar da shi a waje, su kuma suka shiga ɗakin. Jim kaɗan ɗaya daga cikinsu ta fito, bayan ɗan wani lokaci kuma sai gata ta dawo ita da likitan da ya duba Aliyun. Sun jima sosai a ɗakin, dan har sai da ya ƙagu. Sai ga su sun fito, da sauri ya shiga tambayar likitan jikin Aliyun. Likitan ya sanar masa da komai lafiya, dan har sun saka masa arm sling, gudun kada ya cika yawan motsa hannun. Amma kuma sun masa wata allura, wadda ta sa ya koma bacci, amma daga lokacin zuwa ƙarfe bakwai na safe zai iya farkawa. Da haka hankalinsa ya kwanta, har ya dawo ɗakin ya zauna ya ci gaba da gadinsa, har zuwa lokacin da ya farka. “Ya... Ya kake?” Cewar Kuliya, dan be ma san me ya kamata ya tambayi ɗan uwansa ba, wanda Allah ya haɗasu bayan shuɗewar shekaru masu yawa da rabuwarsu. A ɗazun da ya farka cewa ya yi Zaid ɗin ya ara masa wayarsa, akwai wanda zai kira. Bayan da Zaid din ya ba shi wayar, sai ya kira Anna ya sanar mata halin da yake ciki. Kuma tun bayan wannan maganar, wata magana bata ƙara shiga tsakaninsu ba. Zaid ya juyo ya kalleshi, me makon ya amsa tambayar da ya masa, sai ya ja ɗan uwan nasa ya rungumeshi. Duk cikinsu babu wanda be zubar da ƙwalla ba, dan faɗar kalar kewar juna da suka yi ma ɓata baki ne. “Wannan ne abun da ya kamata ace ka tambayi yayanka bayan kun haɗu?!” Cewar Zaid yana shafa kansa bayan da suka saki juna. Kuliya ya share hawaye. “Ban... Ban san me ya kamata na ce ba ne?” “Dama kai kana rasa abun faɗe ne?” Sai suka yi dariya. “Ina Mishal?” “Wa? Ko matarka ?” Sai Aliyu ya sunkuyar da kansa yana faɗin. “Eh ita” “Suna gidana, ɗazu na ga kiran matata, na san nan da anjima za ka sun iso...” Daga nan kuma sai aka buɗe babin hira, suka shiga bawa juna labaran abubuwan da suka faru a rayuwarsu bayan rabuwarsu, daga Zaid har Aliyun, Allah ne kaɗai ya san kalar farin cikin da suke ciki, bayan shuɗewar tarin shekaru, yau sai ga su a tare da juna,me ya fi wannan daɗi?. Ba su ɓoye juna komai ba, wani zancen su yi dariya, wani kuma su matse ƙwalla. Kuma cikin hirar tasu ne, Zaid yake sanarwa da Aliyu cewar ya haɗu da dangin Momma, kuma su ne ma suka aura masa matarsa, dan ita ce 'yar anti Maryam da Momma ke basu labarinta. Sosai suka tattauna kan matsalolin da suka faru da su, da kuma nasarorin da ko wannensu ya yi a rayuwa. “Ni da ma na san baka mutu ba, dan ce mana aka yi ka gudu, ba cewa aka yi ka mutu ba... Kawai de na haƙura na fawallawa Allah ne, fon na san ko ba daɗe, ko ba jima idan har Allah ya hukunta haɗuwar mu da juna za mu haɗu...” Zaid ya ci gaba da kallon ƙanin nasa cike da alfahari. Ji yake kamar ya buɗe cikinsa ya saka shi ya kulle, gudun kada wani abu ya ƙara zuwa ya shiga tsakaninsu. Ƙofar ɗakin aka turo, Mishal da Rabi suka bayyana a bayan ƙofar. Daga Zaid ɗin har Aliyu suka juyo suna kallon bakin ƙofar. Mishal na arba da Kuliya, zaune da rai, wata ƙwalla ta silalo daga idonta. Ba ta san ya ka yi ba, amma ita de ta san kowa dake ɗakin ya ɓace a idonta, ba ta ganin kowa sai Aliyuj da ke zaune a bakin gado, sanye cikin wasu bluen riga da wando, hannunsa na dama saƙale cikin arm sling, ya kafeta da idamuwansa ya na kallo. Dan haka ta taka da gudu ta yi kansa, kuma tana zuwa kusa da shi ta faɗa jikinsa ta rungume mijinta. Kuliya ya ɗan cije lips ɗinsa na ƙasa, saboda zafin famun da Mishal ta masa, amma haka ya ɗago da hannunsa na hagu, ya ɗora avkan gashinta dake cikin hijabi. “Abu Aswad... Abu Aswad ɗina... Abu Aswad... Da ma na san ba za ka mutu ka barni ba...” Faɗi take tana ƙara ƙanƙameshi. Hakan ya sa Zaid miƙewa daga bakin gadon ya ja hannun Rabi zuwa waje, tare da rufo musu ƙofar. Mishal ta ɗago da kanta daga ƙirjin Kuliya, ta shiga dudduba jikinsa, hawaye ya jiƙa mata fuska. Hannunsa ya ɗago ya kama fuskarta. “Abu Aswad ɗina!” “My Teddy Bear” Kuliya ya furta a hankali yana share mata hawayen. “Da ma ai na faɗa maka cewar ba za ka mutu ka barni ba...” Fuskarsa ya kara da tata ya na faɗin. “I love you Mishallyn Aliyu, i love you to the moon and back... I love you my Boo, my last love, my babe, my other half, my treasure, my honey bun...” Kafin a hankali, ya haɗe bakinsa da nata, suka shiga musayar yawu. Sakinta ya yi yana zaunar da ita a gefensa. Sai kuma ya kalleta sosai. Idonta har wani ƙyallin murna yake na ganin ya samu sauƙi. ”Kin yi kyau, wa ya baki hijabi kika saka?” Sai ta kalli hijabin jikin nata tana faɗin. “Anti Adawiyya ce ta bani” “Ya miki kyau sosai” Matsawa ta yi kusa da shi, kamar me shirin komawa cikinsa, ta maƙalƙale hannunsa na hagu. “Abu Aswad! Jiya fa na ɗauka cewar ka mutu. Na yi tunanin ka mutu ka barni.Na ɗauka cewar wani maraicin zan sake shiga” Kuliya ya yi murmushi ya na sumbatar kanta. “Insha-Allah zan ci gaba da zama da ke, har zuwa lokacin da zaki kawo mana babynmu!” Sai ta ɗago da kanta ta kalli fuskarsa. “Kenan zan samu baby?” Sai ya yi dariya. “Haka nake zato, ina da yaƙinin cewa mun kusa samun baby soon” Sai ita ma ta yi dariya tana kwantar da kanta a kafaɗarsa. “Ka san suna wa za'a sa masa?” Dariya shi ma ya yi, har jikinsu na jinjiga a tare. “Wai an tabbatar ne?” Ta ɗago tana fadin. “Me ɗin?” “Babyn mana. An tabbatar kina ɗauke da shi?” Nan take ta haɗe rai tana kai masa duka a damtsen hannunsa. “Auuchhh! Teddy Bear irin wannan duka haka?” Ta turo baki gaba tana faɗin. “To ba kai ka ce min na samu baby ba, kuma sai ka dawo kana min wani ƙauli da ba'adi” Ta faɗi idonta na ciccikowa da ƙwalla, dan ita har ga Allah ta riga da ta yadda da cewar ta kusa samun babyn, ya riga da ya sa mata rai, kuma sai ya zo yace ba haka ba?. “Wasa fa nake miki, amma idan kina so sai an ƙara!...” Ta san me yake nufi da sai an ƙara ɗin, dan haka ta ƙara ɗaka masa wani dukan, wannan karon a cinyarsa, ya dafe wurin yana dariya. “Ki yi haƙuri, kin ga fa ba ni da lafiya, ya kamata ace an raga min ai” Mishal ta share ƙwallar da ta silalo mata, dan ita ta mamanta da ba shi da lafiyar. “To ka yi haƙuri” “Ke!” Ta kalleshi. “Me ya sa kika yi laushi ne?. Abu kaɗan sai ki masa kuka, bayan na san da ba haka kike ba” Ya tambaya jin

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112