Chapter 32
Chapter 32
juya kallonta kan Habiban, ta ga yanda ta tsareta da ido. Hannunta na rawa ta kai ta karɓi kofin, sai da ta raintse idonta, ta yi bismillah, sannan ta kafa kai ta shanye abun cikin kofin. Taste ɗin bakinta ya mata wani iri, dan abun sam ta kasa gane na miye, sai dai tana da tabbacin koma miye sharri ne. Kofin ta aje mata a gabanta, ta miƙe, ta kama hanyar fita. Habiba ta bi bayanta da kallo tana murmushi, tasan kamar yanda yayarta ta faɗa mata ne, komai ya zo karshe tun da ta sha wannan abun, saura kuma jiran ganin sakamako. “Honeynah, Ya kika yi shiru?” Muryar Yaya ta faɗa, yayin da yake kallon Rabi'a, wadda ke zaune a kan wani benci dake bakin shagon, shi kuma yana daga cikin shagonsa, wayar Anti Saratu riƙe a hannunsa, yana tura mata abubuwan da Rabi'an ta lissafa masa. Rabi'a ta sunkuyar da kanta ta na murmushi. “Ni kam ina san wannan kunyar taki, tarbiyyarki da kyawunki su ne ke ƙara min shauƙin ƙaunarki Rabi'ata...” Rabi ta ƙara sinne kai tana wani murmushi me kama da dariya. Shi ma Yayan murmushin ya mata, yana juyar da kansa ga turin da yake mata. Kafin daga bisani ya shiga ba ta labarin yanda wasan jiya ya kasance, dan yasan yanda take matuƙar san ball, kuma shi ma yana tayata. Sai da suka ɗan taɓa hira, sannan ta masa godiya ta fito daga shagon. Wata mota ta ga ta yi parking a bakin titi, kasancewar shagon Yayan a bakin titi yake. Fuskar Mama ta gani a gaban motar zaune a gefen drivern. Kanta ta girgiza kawai ta yi gaba, ta zo wucewa ta kusa da wasu matasa dake kan benci suna hira, hirar ta su ta ɗauki hankalinta. “Wannan 'yar gidan tsohon najaduncan ce ko?” Na kusa da shi yace. “Ko ba Mama ba ?, Ita ce, kai kuwa barewa ba ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ?... Ai kamar Kumbo kamar kayanta ?” “Allah ya kyauta mana kawai...” Sauri ta ƙara, gudun kada ta ji abun da zai sa ta fashe da kuka nan take. Daga can cikin motar Mama ta shagwaɓe fuska tana kallon sabon Alhajin da ta yi. “Gaskiya Baby ni sati zamu yi” Alhajin ya yi dariya irin tasu ta goggagun 'yan bariki. “Baby Mamancy! Ai sai yanda ki ka ce, idan kin ce mu yi wata ma babu wata matsala” Daɗi har ran Mama, ta je ta yi wata a England ita da wannan Alhajin?, ai har ta hango irin kuɗin da za ta yi. “Shikenan, zuwa yaushe za mu tafi?” Alhajin ya shafo ƙaton tumbinsa, sannan yace. “Nan da next week, kawai dai ki zama cikin shiri, sannan ki aikomin da hotonki na passport” “To sai na jika” Ta faɗi tana masa wani farrr da ido, sannan ta kama ƙofar motar ta buɗe. Idan ka hangeta daga nesa, cewa za ka yi sam ba ta haɗa jini da hausawa ba. Wata matsataiyar duguwar riga ce a jikinta, sai wani ɗan fingil-gilin mayafi da ta riƙoshi a hannunta. Small knotless barid ɗin dake kanta, wadda aka kitsa mata ita da wani golden attachment ta sauƙo tana lilo a gadon bayanta. Fatar jikinta har wani pink-pink take, don tsabar man bleaching ɗin da take shafawa. Ga wani nose ring da ta saƙala a gefen hancinta. Duk wanda zai mata kallo ɗaya, a tashin farko zai kirata da karuwa!. Ko sallama babu, haka ta sa kai a cikin gidansu. Habiba da har lokacin na zaune a ƙofar ɗaki ta miƙe tsaye tana washe baki. Ganin Maman ma na fara'a. “Umma, mu shiga daga ciki” “To...To!” Habiba ta faɗi cike da zumuɗi, ɗakin nata suka shiga, ta tsaya tana kallon Mama, tana jiran abun da za ta faɗa. “Wannan sabon Ahajin da na yi ne, tafiya ta kama shi zuwa ingila, kuma yace da ni zai tafi” “Ayyirri!...Yirriri!” Habiba ta rangaɗa guɗa tana kama danannen hancinta hancinta. “Ni na san ban yi haihuwar banza ba, ni da kaina na san cewa na yi farar haihuwa... Ingila fa Mama?, Ƙasar turawa ?” “Nan fa” Mama ta tabbatar mata murmushi kwance kan fuskarta data sha mai. Saratu da Rabi dake ɗaki suna iya jiyowa komai, zuwa lokacin Fatima ba ta ɗakin, dan Anti Saratu gama mata faɗan ta tashi ta fice ta bar gidan gaba ɗaya. Anti Saratu ta girgiza kai cike da takaicin mahaifiyarta da ƙanwarta. Rabi da ta fara kallon wasan a waya ta kalleta. “Ba ƙunci ya kamata ki yi ba... Ki musu addu'a kawai” Anti Saratu ta yi murmushi. “A kullum ina yi Rabi, amma gani nake kamar abun nasu ba na ƙare ba ne” “Kada ki ce haka Anti Saratu, Allah ma jiroƙon bayinsa ne, ki dage da addu'a, Allah zai amsa miki ” #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters °°°°°°°°°°°°°°°°°°° *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *09* ~~~ *Someday, you will get everything you deserve, and it will be beautiful* *** *Shekara ta 2000* *Kano...* “Aliyu!, Aliyu! Wai kana ina ne ?!” Zaid ke ƙwalawa Aliyu kira, bayan da ya dawo gidansu bai tarar da shi a inda ya barshi ba, sanye yake da wannan uniform ɗin islamiyyar da ya rage musu. Babu datti a jikin kayan, kasancewar ya na ɗaukowa ruwa a tuƙa ya musu wanki, sai haske da yadin kayan ya fara, alamun ya na jin jiki. Hannunsa na dama riƙe da ledar ƙosan da ya samu ya siyo, bayan ya je ya yi bara a bakin titi, Bara?!, a yanzu ita ce abin da yake dan ya samu ya kawowa ƙaninsa abin da zai ci. Sati ɗaya kawai Maman Naufal ta yi tana basu abincin da ba ya ƙosar da su, daga nan idan ya shiga gidan sai ta ɗaure fuska, har ta kai da ta ce masa kada ya ƙara shigowa gidanta. Ga shi su kuma babu gidan da suka sani a unguwar, da ma gidan nata ne kawai suke ɗan shiga, ganin yunwa za ta lahanta masa ƙani ne yas sa ya fara barar, sai ya tafi bakin titi ya tsaya yana roƙar jama'a. Da haka yake ɗan samun abun da zai kawowa Aliyun ya ci. To yau da safe ma ba su tashi da komai ba, hakan ta sa da wur-wuri ya fice ya tafi barar, sai da ya shafe sama da awa uku. Sannan ya samu na siyan wannan ƙosan... Tunaninsa ne ya katse, a sabda ya ɗora idonsa a kan Aliyu dake durƙushe a bayan gidansu. Hankali tashe ya yi cilli da ledar ƙosan ya yi kansa yana kiran sunansa. “Aliyu! Aliyu! Kai Aliyu me ya ke faruwa da kai haka ?” Ya tambaya a sanda ya ɗago shi, ya na kallon fuskarsa da tai jawur, kasancewarsa me farin fata, ga idanuwansa sun yi ja, kuma a 'yan kwanakin Zaid ɗin ya gano cewa dukansu sun rame. Sannan ya san ba komai ba ne face yunwa, musamman ma Aliyu da sam ba ya iya jurewa yunwa. “Yunwa kake ji ?” Zaid ɗin ya tambaya yana miƙar da shi, da ƙyar Aliyu ya iya gyaɗa masa kai, a hankali Zaid ɗin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya miƙar da Aliyun gaba ɗaya. Kama shi ya yi har suka shiga cikin ɗakin da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112