Chapter 41
Chapter 41
zuciyarsa, yanda ta kafe shi da olive green eyes ɗinta kaɗai ya isa ya sa shi a uku. Da ƙyar ya haɗiye wata iska, sannan ya fara takowa zuwa cikin falon. Mishal ba ta san wa ta kunya ba, hakan ya sa ba ta ji komai ba dan ya ganta a cikin irin wannan shigar. “Wannan kuliyar, take ce?” Muryarta ta fito a sake, kamar ta san shi, kamar ta saba da shi, haka ta masa maganar tana shafa bayan kuliyar. Ba tare da ya kalleta ba, ya aje ledar hannunsa a kan coffe table, ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya ce. “Ayra” Mishal ta ƙyal-ƙyale da dariya, dan ta fahimci cewa sunan Kuliyar ne Ayran. Ɗagowa ya yi ya kalleta, wai ita ba ta san rashin sabo ba ne?, ji yanda ta ke, kamar wanda suka saba tsawon shekaru. “Wato saboda kada a kirata da irin suna ka, shi ne ka yiwa Ayra star takwara, tab ɗi jam, Ayra star go sue you oo!” Kallonta ya ci gaba da yi, yanda take maganar a sake, da yanda take shafa jikin kuliyar, da kuma yanda take abu cike da yarinta ne ke nuna masa ƙarancin shekarunta. Leda ɗaya ya miƙo mata, cikin ledojin da ya shigo da su. “Ki ci!” Mishal ta ɗan kalli ledar, wai shi ba ya doguwar magana ne ?. Ba tare da tace masa komai ba, ta karɓi ledar, sannan ta ɗora Ayran a kanta, tana zama a kan sofa, tare da yunƙurin buɗe ledar. Gadan-gadan Kuliya ya ga tana shirin fara cin abicin da hannunta ba tare da ta wanke hannun nata ba. Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar faɗin. “You have to wash your hands first” Sai ta dakata da shirin kai lomar da take, ta ɗago ta kalleshi, ya na tsaye a yanda yake, sai kuma ta aje take away ɗin, sannan ta sauƙe Ayran dake kanta. Ta nufi ɗakinta dan ta wanke hannun nata. Kuliya ya bi bayanta da kallo yana mamakin irin halin da yarinyar ke ciki, Abubakar ya sha ba shi labarin irin halayenta, bai taɓa yarda ba sai yau. Lalle akwai aiki ja a gabansa, dole ne yasan yanda zai seta yarinyar nan, saboda sam ba ta san ma mecece rayuwa ba, rayuwarta take kanta tsaye. *Washe gari...* *07:30 AM.* Kuliya na tsaye a falo yana fitar da abincin da ya siyo daga leda, wanda ya siyo a restaurant ɗin da ya saba siyan abinci. Jin motsin buɗe ƙofa a corridor ne ya sa ya juya ya kalli ƙofar, kamar yanda ya sa ni, ita ɗin ce ta fito, sanye cikin kayan da ya fara ganinta da su, wato uniform. Backpack ɗinta riƙe a hannunsa na dama, yayinda suit ɗin uniform ɗin ke riƙe a hannunta na hagu. Ba tare da ta tambayashi ba har ta riga da ta yankewa kanta hukuncin cewa za ta je makaranta. Da alama ma dai ita ba ta san hakkin aure ba, ba zai yi wa kansa ƙarya ba idan yace ba ta ma san miye auren ba, ba ta san cewa yanzu tana ƙarƙashin wani ba ne. Sai ya ɗaga kafaɗarsa ta dama a hankali, kana ya Juya, ya ci gaba da fitar da abincin. Mishal ta aje backpack ɗinta a kan sofa, sannan ta ɗora suit ɗin nata a kan jakar. Ta ɗan kalli inda yake, wai shi ba shi da aiki sai saka baƙaƙen kaya, ta faɗi a ranta tana kallon baƙar suit ɗin dake jikinsa, amma kuma ai kwana kin da take ganinsa a tsallaken makarantarsu ba baƙaƙen kaya ba ne. Sai kuma ta taɓe bakinta kaɗan tana ƙarasawa kusa da shi. “Ina kwana” Ta gaida shi tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata da: “Ummm” Wai shi ba ya magana ne?, sai kuma ta kawat da komai, ta yi masa tambayar dake ranta tun jiya da ta gama cin abincin da ya kawo mata. “Babu kayan girki a gidan nan ne ?” A hankali Kuliya ya juyo ya kalleta, kayan girki?, to me za ta yi da su?, ita nan ɗin wai har wani girki ta iya?, inaaa, shiriritar ta ce kawai, dan a haka idan ka kalleta kai ka ce babbace wadda take da tunani, sai ka yi magana da ita za ka ga tsantsar yarinta. Ba tare da ya amsata ba ya ci gaba da abinda yake. “Magana fa nake...” Ya ƙi ko kallonta. “To ni dai ba na iya cin abincin waje, ina san na yi girki da kaina!” Still be kalleta ba har ya gama fitar da kayan, ya ware mata wasu robobi biyu, sannan ya tura mata. “Ki ci ɗaya yanzu, and you can take the other one to school” “Yanzu fa na ce maka ba na iya jurewa cin abincin waje...” Ba tare da ya ko kulata ba ya ɗauki nasa, sannan ya yi corridor. * Tafe suke a motarsa, yayin da Kuliya ke tuƙa motar Sharon da ta ba ahi aro a kwanakin, dan har yanzu bai samu damar siyan wata motar ba, tasa kuwa da ma bai ƙara bi ta kanta ba. Da yake yasan makarantar tasu, kansa tsaye can ya dosa, har cikin makatarantar ya shiga, sannan ya yi parking a harabar makarantar. Ba tare da ta kalleshi ba dan fushi take da shi , Mishal ta buɗe motar za ta fita. “Da ƙarfe nawa kuke tashi?” Ta juyo ta kalleshi tana turo baki gaba, ciki-ciki ta amsa masa da: “Ƙarfe biyu, idan kuma ina da class ɗin kungu fu sai ƙarfe uku muke tashi...” So yake ya tambayeta a wasu ranaku take da ajin kungu fu ɗin, amma sai miskilancin dake cikinsa ya hana, ba tare da ya sake cewa komai ba, ta ja jakarta ta fita. Ya bi bayanta da kallo har ta shige can cikin makarantar. Ya ɗaga kafaɗarsa sama yana furzar da iska, Allah ya haɗashi da mata. Amma ba komai, zai yi ƙoƙarin daure duk wata shirirtarta, zai san yanda ya yi ya ɗorata a hanya, don zai iya yin komai saboda Abubakar. _____________________ _Jama'a, kun ji fa dramar dake faruwa a cikin wanga tahiya_ _To... Ga Kuliya ango, ga kuma Mishal amarya😂😂. Dan Allah ya kuka ga yanayin zaman nasu?_ _To Mama ta shilla zuwa Ingila, sai ku taya ta da addu'a_ _Ga kuma oga Raja ma a nasa ɓangaren, yana nan yana gina mana soyyayar Rabi a zuciyarsa_ _Wani ya faɗa min ina labarin nan ya dosa?_ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters •••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *11* ~~~ *Let's never forget, it's you and me vs problem, not me vs you...* *** Follow my Wattpad account 👇 https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends *Brickhall school, Kaura District, Abuja* RABI'A POV. Tsaye take a kusa da filin buga ball na makarantar, daga nesa take leƙen yaran da suke buga ball a cikin filin, ji take kamar ita ma ta shiga cikinsu don a buga wasan tare da ita, amma ba hali, tun da ko kusa da su ma ba ta isa ta je ba. “Ke 'yar aiki!, Me kike a nan?!” Ta juyo da sauri tana kallon mammallakin muryar, wasu yara ne maza su uku, sanye cikin kayan sport na ball, kuma ta san 'yan wani aji ne, 'yan ss2 ne, ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112