Chapter 35
Chapter 35
laptop ɗin dake gaban Raja, zaune yake a kan kujerar falo, Rhoda na zaune a gefensa. Waɗanan su ne ire-iren maganganun da suka yi da shi a ranar da suka tattauna da shi a ganawarsu ta farko. Ba tare da sanin shi Alhji Balan ba, Raja ya naɗi komai ta cikin wata na'urar ɗaukar hoto da magana, wadda ya saƙala a gaban rigarsa a waccan ranar. Rhoda ta ɗaga hannunta, tare da bubbuga kafaɗarsa. “Mun yi aiki me kyau Raja... Ina tunanin wannan hujjar ma kaɗai ta ishe mu... Ba ma buƙatar wata...” Bisa ga mamakinta sai ta ga ya girgiza kansa, ya na jingina da jikin kujera. “Basu isa ba Rhoda, muna buƙatar wasu” Cike da mamaki take kallonsa, wata hujja za su buƙata bayan wannan ?, 'yar wannan maganar tasa da suka naɗa wadda ba ta wuce mintuna biyu ba, ita ce ta shigo da su wannan rayuwar da ba ta su ba. A ganinya wannan kaɗai ta isa ta hutar da su aikin bautar da suka sha tsawon shekaru huɗu. “Rhoda, ba ni da ke kaɗai Alhaji Bala ya zalinta ba, ya zalinci mutu ne da dama... Kuma ba shi kaɗai ne yake zalincin ba, har da ɗansa Usman... Kin san yara nawa Usman ya yiwa fyaɗe ?” Cike da ƙunar zuciya Rhoda ta girgiza masa kai, dan kuwa maganarsa ta tuna mata da bayanta, rayuwarta ta baya da mahaifiyarta. Dama abun da ya zamo sanadiyyar rabuwarsu da mahaifiyar tata. “Kusan yara mata goma ya yi wa fyaɗe!...” Idonta ta rintse tana kawar da kai. Raja ya zauna da kyau, sannan ya kamo hannaunta. “Kada ki damu, za mu ga ƙarshen komai, za su kwashi kashinsu da hannayensu, sai an ƙwatawa kowa hakkinsa... Ba ni... Da ke kawai ba... Kowa Rhoda, i mean each and every body da suka taɓa zalinta” A hankali wata ƙwalla ta sauƙo daga idon Rhoda, ta kwantar da kanta a kafaɗar Rajan, shi kuma ya shiga bubbuga bayanta, alamun rarrashi. A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cikin faɗin. “Wannan hujjar ta yi kaɗan mu kai babban mutum irin Alhaji Bala ƙasa, muna buƙatar hujjojji masu tarin yawa, waɗan da ba wai ƙasa kawai za su kai shi ba, rugu-rugu za su yi da shi... Za mu kai masa wannan kayan, kuma kin san daga haka zai ƙara yarda da mu, mu kuma daga haka za mu ƙara ƙaimi wurin kai shi ƙasa!” Rhoda ta share hawaye, tana yarda da maganar ɗan uwanta ɗaya tilo da ya rage mata a duniya, tun da har ya faɗi tasan zai cika, zai aikata duk abun da yace... A idanunsa kawai take hango irin faɗi tashin da ya riƙa yi a rayuwarsa don kawai ya ga ta samu gobe me kyau. “Lokacin sallah ya yi, zan je masallaci” Ya faɗi yana miƙewa, sannan ya dafa kanta, ya fice daga falon. A balcony ya haɗu da su Zuzu. Suna zaune sai zuƙe-zuƙensu suke. Wutar da ya hango a jikin tabar Jagwado ce ta sa hayyacinsa ƙoƙarin rabuwa da gangar jikinsa. Suma kuma sai a lokacin suka lura da shi, don haka suka yi saurin kashe wutar dukansu, dan sun san matsalarsa da wuta. Sun san halin da yake ciki, shi yasa ba sa shaye-shaye a kusa da shi. Saboda suna sonsa, suna sonsa Saboda yanda ya temaki rayuwar kowannensu. Sai da Raja ya dafe bango, sannan ya dawo hayyacinsa, da ƙyar ya kallesu. “Lokacin sallah ya yi, ku tashi muje ku yi...” “Ai kasan ba ma je gaban Ubangiji muna warin wuwu ba ko... Oga Raja ka bari sai mun ɗan eh yi wanka... Ka gane ko?...” Cewar Alandi yana miƙewa. Yanda yake magana kawai ya tabbatarwa da Raja cewa sun bugu, ya girgiza kansa yana ɗaga kafaɗarasa, ya sauya komai a tare da su, wannan shaye-shayen ne ya kasa hanasu yi. Amma ya ƙudircewa ransa cewar, suna gama wannan aikin zai sada kowannensu da Rehab. Agogo ya duba, ya ga lokacin tashin ɗaliban makarantar nan ya kusa, dan haka a gurguje ya ƙarasa masallacin estate ɗin. Ya yi sallah, sannan ya fita ya tsaya a inda ya saba tsayawa don ganinta. *Brickhall School, Kaura district, Abuja..* MISHAL POV. Tsaye take a tsakiyar abokan koyan faɗanta na Kungu fu. Sanye take cikin uniform 🥋 ɗin koyar da wasan kungu fu ɗin, ta ɗau matsayarta. Yayin da hannunta na dama ke dunƙule ta seta yarinyar da aka haɗasu faɗan, ɗayan ma a dunƙule yake amma a ƙasa. Ɗaya yarinyar ce ta kawo mata duka, hakan yasa cikin salon faɗan na kungu fu ta ware hannunta na dama, ta kama hannun yarinyar, tare da banƙara shi, ta rataya hannun yarinyar a kafaɗartsa, sannan ta kaiwa yarinyar bugu a gefen ciki da hannunta na hagu. Tini yafinyar ta shiga ɗaga hannunta, alamun saduda. Mishal ta saketa, hakan yasa hall ɗin koyon wasan nasu ya karaɗe da tafi, ita ce ta yi nasara kamar kullum. Cike da girmamawa ta miƙawa malamin kungu fu ɗin nasu gaisuwa, sannan ta ja baya. Malamin nasu ya ɗan musu wasu jawabai a kan wasan, sannan aka sallami kowa. Ita ta koma jikin lokarta inda ta saba aje kayanta ta sauya kayan, sannan ta damƙawa Angelica riƙon jakarta, suka fito a tare. Sai da ta je wurin Adawiyya suka yi sallama, sannan ta karɓi jakarta a wurin Angelica, tare da sallamarta, ta shige mota, Baba Ali ya tayar, suka fita daga makarantar. Kamar jiya yau ma sai da ta ga Kuliya tsaye a jikin gate ɗin estate ɗin nan, to wai shi wannan me yake zuwa yi nan ?, ta tambaya kanta. Sai kuma ta share, tare da faɗawa kanta cewar; to wai ina ruwanta ma?. Har suka kai gida tana shan hannu. Fita ta yi daga motar, a sanda suka iso gidan, ta shiga cikin gidan, Daala ta samu ita da Mama Ladi suna wasa a falo, kai tsaye sama ta wuce, ta shiga ɗakinta. Abu na farko da ta fara yi shi ne, aje jakarta a kan work table ɗinta, sannan ta shiga wanka ta fito, ta sauya kaya zuwa wata yaluluwar shift dress, rigar bata sauƙa har ƙasa ba, bakinta kan singalinta. Ta nannaɗe gashin kanta cikin bun, tare da saƙala wani hair pin ɗinta me shape ɗin bow. Da saurinta sauƙo zuwa ƙasa, sannan ta faɗa kitchen dan ta samawa kanta abun da za ta ci, duk da ta ga abinci a kitchen ɗin, amma alƙawari ne ta ɗaukawa kanta cewar ko yunwa za ta kasheta ba za ta ci abincin da Hajjara ta girka ba. Jallof ɗin rice stick ta shiga yi, babu jimawa ta gama, sannan ta dawo ta zauna kusa da su Daala ta soma ci. Loma ta uku kawai ta yi, wayar landline ɗin dake falon ta yi ringing, hakan ya sa ta aje bowl ɗin hannunta, ta miƙe tsaye ta na ɗaukan wayar. “Hello!” Ta faɗi a sanda ta kara wayar a kunneta, muryar kawu Musa ce ta doki dodon kunnuwanta, cikin kuka da shessheƙa. “Hafsat ke ce ?” Gabanta ya faɗi, amma sai ta dake tace. “Eh Ammu(Kawu)... Ni ce” “Ina Hajjara?...” Sai ta kalli falon, kamar me neman Hajjaran a falon, sannan ta kalli danning area tana amsa ma sa da: “Ba ta kusa”
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112