Chapter 102
Chapter 102
tana iya jiyo sautin bugun zuciyarsa dake shirin ɓalla allon ƙirjinsa ta fito. “Na san komai a kanki, ya kamata a ce kema kin san komai akaina!...” Tun kafin ya kai ƙarshen labarin nasa Rabi ta fara hawaye, tunawa da ta yi cewar ɗan uwansa da yake so, kuma yake tunani ya mace yana raye. “Zaid!” Ta kira sunansa tana sharar ƙwalla. Kanta Zaid ya shafa yana amsawa. “Aliyu ya na raye!” Wani irin bugu da ta ji zuciyarsa ta yi ya sa ta yi saurin tashi daga jikinsa, dan a tunaninta ko zuciyar tasa ta buga ne gaba ɗaya. Amma kuma sai taga har lokacin yana da rai, sai de kuma kamar ya mace, dan kallonta kawai yake, amma jikinsa a ƙame. Wai me take faɗi ne?, Aliyu yana raye?, Aliyunsa bai mutu ba?. A'a, wata ƙila dai kunnensa ne ke haihuwa, ko kuma Rabi'a tana faɗin hakkan ne dan ta kwantar masa da hankali. Aliyu na raye?. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *26* ~~~ *You ware using your ear to hear, and i am using my heart...* *** *No.181, Guzape, Abuja...* *10:11pm* KULIYA POV. _🎶I lost my way, somewhere in another galaxy_ _Too much to take, these memories end in tragedy_ _And all of these pleces , all of these faces, I didn't wanna let you down_ _And all these mistakes of mine I can't replace it, i gotta move on somehow 🎶..._ Waƙar dake tashi kenan a falon gidan. Daga can ɓangaren da kujerun gidan kuma suke, Kuliya ne durƙushe a gaban Mishal, wadda ke zaune a kan kujera, ya kama ƙafarta ta dama yabna saka mata safa, saboda sanyin da ake a gari. Safar ya gama saka mata, sannan ya kai hannunsa ya janyo hular sanyita dake gefen kujera, ya miƙe tsaye yana saka mata a kanta. Binsa kawai take da kallo, tana shawara da zuciyarta, kan ta yadda za ta ɓullo masa da maganar da suka yi da Adawiyya a yau. Zama ya yi a gafenta ya na cewa. “Shikenan?” Kanta ta gyaɗa masa tana gyara zamanta. Kallon da suke suka ci gaba da yi, kafin Kuliyan ya miƙe ya shiga kitchen ya aje plates ɗin da suka ci abinci. Har ya kamo hanya zai fito, sai kuma ya fasa ya koma dan ɗaukar ruwa. Babban kuskuren da ya tafka kenan a ranar. Dan a sa'ilin da ya rufe murfin fridge ɗin, asa'ilin wani ɗan ƙarami, kuma mulmullallen ƙarfe, ya fito daga cikin bindigar da aka harba da ƙarfin tsiya, kuma bai tashi sauƙa a ko ina ba, sai a damtsen Kuliya na dama. Wani irin shiga harbin ya masa, hakan ya sa shi sakin gorar ruwan dake hannunsa da sauri, sannan ya yi luuu zuwa baya ya na shirin faɗu, cikin dauriya da zafin nama ya kai hannunsa ya dafa island. Da ƙyar ya tsaya a kan ƙafafunsa ya na layi. Wani irin zugin azaba hannun nasa yake masa, hakan ya sa ya kalli hannun, bai tabbatar da abun da yake gani ba, sai da ya kai hannunsa ya kawar da ɗan guntun hannun T-shirt ɗin jikinsa, ya ga ramin da harbin da aka masa ya yi. Ji ya yi jini na ɗibansa, tunawa da ya yi da Mishal dake falo ya sa shi cije leɓensa na ƙasa. Ya kai hannunsa na hagu ya riƙe damtsen nasa dake ta zubar jini, da ƙyar ya ja ƙafarsa zuwa falon, dan ya san ko ma su waye suka zo gidan dan shi suka zo, kuma idan aka jima kaɗan za su iya shigowa cikin gidan, wata ƙila su cutar masa da ita. “Ab... Abu... Abu Aswad... La... lafiya...” Mishal ta faɗi tana miƙewa tsayi, ganinsa cikin wani hali ba ƙaramin ruɗata ya yi ba, kamar an kunna famfo, haka hawaye ya shiga mata zuba, da sauri ta nufi inda yake tana kiran sunansa, duk ta birkice, ta rasa abin yi. “Zo... Zo mu je ka zauna!” Ta faɗi tana jan hannunsa na hagu dake kan damtsensa na dama. Da sauri ya riƙe nata hannun ya na girgiza mata kai cike da dauri, leɓensa ya ƙara datsewa. A sanda ya fara jan hannunta zuwa ɗakinsa. Kamar raƙumi da akala haka ta riƙa binsa har zuwa ɗakin nasa, duk kuwa da shi ɗin ba ya tafiya da kyau, ta lura ma da layi yake. Wani abu da ya bata mamaki shi ne, ganin ya nufi closet ɗinsa da ita. Mamaki bai gama cinyeta ba har sai sanda ta ga ya danna wani switch da duk shigowarta wurin ba ta taɓa lura da shi ba. Ba tare da ɓata lokaci ba, lokar kayan dake wurin ta zuge zuwa gefe sannan ƙofa ta bayyana a gabansu. Hannunsa na hagu wanda ya yi kaca-kaca da jini ya kai ya tura ƙofar ta yi baya, sannan ya tura Mishal ɗin ciki, shi ma ya shiga. Ya na shiga ya rufo ƙofar, ya danna wani switch dake kusa da ƙofar, nan take lokar nan da ta yi gefe ta koma mazauninta na ainahi, kamar ma ba'a taɓa motsa ta ba. Mishal ta ci gaba da bin wurin da kallo, ganin cewar ɗaki ne, har da gado a ciki, ga kuma wani work table dake ɗauke da computers da kuma tardu. Duk da tana cikin halin ruɗu, bai hanata jin mamaki na jan ƙafarta zuwa ƙasa ba, to shi wannan ɗakin ta wani ɓangare yake a gidan?, dan ita ko da wasa ba ta taɓa sanin cewa akwai wasu ɗakuna bayan waɗanan ukun da ta sani a gidan ba. Jin abu ya faɗi yaraf a bayanta ya sa da sauri ta waigo. Idonta ya sauƙa a kan Kuliya dake yashe a ƙasa, hannunsa na hagu dafe da damtsensa na dama, wanda yake ta ɓuɓullar da jini. Da gudu ta isa kansa tana kiran sunansa, a hankali ta kama kansa tana shirin zaunar da shi. Da ɗan sauran kuzarin da ya rage masa ya miƙe zaunen ya na jingina da bango. Mishal sai duba jikinsa take, kamar wadda aka cewa akwai wani switch da za ta danna a jikin nasa, wanda zai hana zubar jinin da yake. Gaba ɗaya ya haɗa gumi sharkaf, kasancewar babu wata isashiyyar iska a ɗakin, dan ita ba ta ga windo ko wata ƙofa bayan wadda suka shigo ba. Hular kanta ta cire ta na faɗin. “Tsaya na saka maka wannan a wurin, may be zai hana jinin zuba” Da ƙyar Kuliya ya iya sauƙe hannunsa na hagu daga kan raunin, sannan cikin sauri Mishal ta cikukuye hukarta pink color tana danawwa a wurin. Jin ya yi wani irin nishi ne ya sa ta fashe da kuka me sauti tana kallon fuskarsa, idanuwansa har sama suke, alamun dai ya na gaf da rufesu gaba ɗaya. “Na shiga uku ni Hafsat, Abu Aswad kar ka mutu, dan Allah kar ka mutu ka barni, Abu Aswad ka min alƙawarin kasancewa tare da ni fa, kuma na san Anna ta faɗa maka cewar karya alƙawari ba kyau, kar ka karya alƙawari, Abu Aswad ka kasance tare da ni, Abu Aswad ɗina dan Allah!...” Sambatu take tana ƙarawa, ita kanta ba ta jin ma tana cikin hayyacinta, hular kanta da ta cire ce tasa gashin kanta barbajewa a bayanta,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112