Skip to content

Chapter 88

Chapter 88

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

gidan, har ta fara bacci saboda gajiyar da ta yi Jiddan ta taso ta tace mata wai ta zo ta rakata, maganar duniya ta yi amma Jiddan ta ƙi ta amsata. Har ta gaji ta rabu da Jiddan. Mamaki ne ya kamata a sanda ta ga sun nufi ɓangaren samarin gidan, kuma kafin ta gano abun da ke shirin faruwa, har Jiddan ta buɗe ƙofar wani ɗaki, ta turata ciki, sannan ta ja yo ƙofar ta kulle. Ba tare da ta iya tsayawa ta ga abun da ke cikin ɗakin ba, ta yi saurin juyawa tana bubbuga ƙofar, tare da faɗin. “Jidda!, ke Jidda! Wai miye ne hakan?” Daga waje ta ji muryar Jidda na faɗin. “Tsakar dare mijinki ya kira ni yace ya na san ganinki, shi ya sa na kawo masa ke!” Dammm!, gabanta ya buga, hakan ya sa ta juya da sauri, ta shiga ƙarewa ɗakin kallo, kuma idonta bai tashi sauƙa a ko ina ba sai a kan Raja dake zaune daga can gefen gadon ɗakin, waya riƙe a hannunsa, ya kafeta da shanyayyun idanuwansa. Da ƙyar ta iya haɗiyewa wani yawu me ɗaci. A sanda ta ga Zaid ɗin ya miƙe ya na nufota. Kanta ta kawar gefe tana ƙara matse jikinta a jikin ƙofar, banda lugudan bugu babu abun da zuciyarta ke yi, ƙamshin turarensa da ya cika hancinta ya sanar mata da isowarsa gabanta. Zaid ya saki wani murmushi ya na ɗaga hannunsa tare da dafa shi jikin ƙofar, ya mata rumfa a tsakiyarsa. Rabi ta ji kamar numfashinta ba ya fita da kyau, kamar ma ba ta shaƙar isaka ne. Kuma hakan be isa ba sai da Zaid ya kai hannunsa ya kamo fuskarta, hakan ya sa ta lumshe idonta ta kuma buɗewa, saboda ji ta yi kamar ya ɗora mata ƙanƙare a kan fuskarta, sakamakon sanyin da ta ke ji na rata jijiyon jikinta, ba shiri ta rintse idanuwanta gam-gam. “Ammatan Raja!” Amon muryarsa da kuma sunan suka sa ta ware idanunwata tar, ya ilahi!, ashe haka ta yi kewar jin sunan nata daga bakinsa?, ashe ta yi kewar wannan muryar tasa?, ashe shi kansa ta yi kewar ganinsa?, duk ba ta fahimci hakan ba sai yau, sai yau da take tsaye gabansa, a tsakiyar hannayensa. “Ba ki yi kewata ba?” Zaid ya tambaya ya na motsa hannunsa a gefe fuskarta, Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, a hankali ta juyo da kanta ta kalli fuskarsa wadda ta kusa haɗewa da tata, hatta da ɗumin numfashinsa ta na jin sauƙarsa a kan fuskarta, tazarar tsakanin hancinta da nasa bata da wani yawa, hatta da jikunansu sun kusa haɗewa. Ba ta san me ya sa ba, amma ta ga yanda idanuwansa suka ƙara lumshewa fiye da yadda ta sansu a da. Sai de ba za ta bari abun da take ji ya rinjayi kanta ba, ba za ta bari wannan salihar fuskar tasa ta rinjayi tunaninta ba, ita ta san waye shi, ta san ainahin gaskiyarsa. Don haka ta sa hannayenta biyu, ta ture shi zuwa baya. Sannan ta juya ta shiga fafutukar buɗe ƙofar. Zaid ya tsaya a bayanta kawai ya na kallonta. Babu yanda Rabi ba ta yi ba kan ƙofar ta buɗe ama ta ƙi buɗuwa, hakan ya sa ta juyo ta kalli Zaid dake tsaye a bayanta ya na mata murmushi. “Ka buɗe min ƙofa,ina san na fita” Kafaɗunsa duka ya ɗaga mata alamun shi fa babu ruwansa. “Magana kawai nake so mu yi, da zarar mun gama, zan barki ki koma” Muryarsa ta faɗa bayan wani lokaci, Rabi da ta ci gaba da kokawar buɗe ƙofar ta juyo ta kalleshi. “Me kake buƙata?” Ta tambaya idonta cikin nasa, Raja ya kuma yin murmushi ya na isowa gareta, hannunta na dama ya kama ya shiga janta, duk yadda ta kai da tirjewa sai da ya sadata da bakin gadon ɗakin. Ya zauna a bakin gadon, sannan ta ƙarfi ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Rabi'a ta shiga mutsu-mutsun ƙwacewa, amma fur Raja ya hanata. “Idan har ba ki tsaya mun yi magana ba, ba zan barki ki fita ba, sai de ki kwana a nan” Jin maganar tasa ya sa ta tsaya da abun da take, Zaid ya saka hannunsa ɗaya ya kama ƙugunta baya, jin hakan ya sa Rabi jan wata iska, idanuwansa ta ci gaba da kalla, kammar tana shirin gano abun da yake shirin furtawa a cikinsu. Mustu-mutsun ta ci gaba da yi hakan yasa yace. “Sshhhhh!, ki dena” Muryarsa ta fito a hankanli cikin duhun daren, kuma amon muryar tasa ne ya haddasarwa Rabi jin kasala, ba ta san lokacin da ta saka hannayenta ta ƙanƙame gaban rigarsa ba. “Good girl” Ya faɗi a setin kunnenta, jikin Rabi ya shiga rawa, wani abu ya shiga bi ta kan zuciyarta tun daga samanta har zuwa ƙasa. “Wani abu nake san nuna miki” Jin hakan ya sa ta yi saurin kallon fuskarsa. Wayarsa ta ga ya kunna, don haka ta kalli fuskar wayar, tar take iya ganin fuskar Habiba cikin wayar, sannan kuma kar sautin muryar Habiban yake shiga cikin kunnuwanta. “Ke ce wadda aka cutar, dan haka dole sai da izininki maganar za ta iya zuwa gaba, shi ya sa na buƙaci da na nuna miki. Shin kina san ki shigar da ƙara a kanta?” Muryarsa ta faɗa bayan da vedion ya kai ƙarshe, Rabi da idanuwanta suke a ƙafe ta kalli fuskarsa, abun da Habiban ta faɗi sam bai ba ta mamaki ba, tun ba yau ba ta san cewa Habiba ce a bayan ko wani abu dake faruwa da su, amma abun da ya ba ta mamakin shi ne, yanda Habiban tace ita silar yi mata fyaɗe, ko da yake ai abun ba na mamaki ba ne, tun da har Yaya ya ƙita ita kuwa me zai ba ta mamaki a duniyar nan. Jin ta yi shiru ya sa Zaid ya matse hannunsa dake kan ƙugunta ta baya, Rabi'a ta zabura tana ƙara iyowa cikin jikinsa sosai. “Kin yi shiru?” “Ba na buƙatar shigar da wani ƙara! A saketa kawai, ta ci darajar Anti Saratu, be side ai ba ma ita ya kamata a kama ba, ga babban me laifi a nan!” Zaid ya yi murmushi, duk kuwa da ya san cewa hakan za ta iya faruwa. Ita har wa yau a wurinta shi me laifi ne. “Kar ki damu, za su kama ni ai, dubuna ce ba ta cika ba. Kuma ko sun zo kama ni zan ce su bari sai na yi ajiya tukkuna, sai su kama ni” Girar Rabi ta haɗe cike da mamaki. “Ajiya? A ina?” Hannunsa ya ɗaga zai taɓa fuskarta, amma sai ta janye fuskar tata, sai ya yi murmushi. “Well! Yanzu ba za ki gane karatun ba, sai nan da wani lokacin... Kuma miye na kawar da fuskar? A zaune kike a cinyata fa!...” Tunowa da hakan ya sa ta zabura za ta miƙe, amma sai Zaid ya sa duka ƙarfinsa ya dawo da ita, ita kuma sai ta tura shi, kasancewar ya na riƙe da ita sai ya yi baya tare a ita, bayansa ya faɗa kan gadon, yayin da ita kuma take kwance a ƙirjinsa. Fuskarta yake kallo a hankali, yayin da

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112