Chapter 25
Chapter 25
Kamata ya yi, sannan ya miƙar da ita yana shirin fita da ita daga kitchen ɗin. Sai da suka zo wucewa ta kusa da Hajjara, Mishal ta kalleta, kamar ba ita ceke yin gunjin kuka yanzu ba. Sai da ta faki idon Abubakar, sannan ta ƙiftawa Hajjara ido ɗaya, tana murmushin da ke nuna ita ta yi winning gasar. “You lose!” Ta furta hakan a iyaka kan leɓenta kawai, wanda Hajjaran dake ganinta ce kaɗai za ta iya gane me ta faɗa. A sanda Hajjara ta zube a ƙasa tana runzar kuka. A lokacin Mishal ta dawo da nata sabon kukan, tana riƙe hannunta. Hakan yasa Abubakar ƙara ruɗewa, don bai ko Hajjara bai waiwaya ba. *Nizamiye Hospital, Sector S. Cadestral zone, Life Camp, Abuja* “Kamar yanda na faɗa maka ne, yanka ba wani sosai ya shigeta ba, dan haka ba wata damuwa, za ku iya tafiya...” Likitan da ya duba Mishal ne ke korowa Abubakar bayani, wanda gaba ɗaya hankalinsa ya gama ta shi. Daga can wata kujera dake gefe a office ɗin kuma, Mishal ce zaune, daga ita sai long sleeve Oxford shirt ɗin uniform ɗinta, suit ɗina na aje a gefen kujerar da take kai. Kanta a ƙasa tana tuna abun da ya faru ɗazu. A ɗazun bayan da Hajjara ta rarumo wuƙa, sai ta ɗorata a tsintiyar hannunta sannan tace. “Zan yanka kaina, dan na rabaki da Abubakar, zan zubar da jini na fansa, dan na shiga tsakaninku, zan yanka kai na yanzu, sannan na kira shi na ce kece kika yanka ni...” Kuma tun kafin ta gama faɗin abun da za ta faɗa, Mishal tai wuf ta ƙwace wuƙar daga hannunta, sannan ta ɗora a nata hannun ta yanka kanta. Ta kuma yi sauri ta danƙawa Hajjaran wuƙar, kafin ta faɗi ƙasa, shi ne ta kurma wannan ihun tare da saka kuka. Sai kawai ta yi murmushi a fili, yanzu da ace ba ta yi hakan ba, da yanzu ita ce a ciki, ta rasa me ta tsarewa Hajjara da ta tsaneta haka, ba ta san me ta yi mata ba. Hannunta na hagu ta ɗago, ta kalli plastern da aka saka mata yanzu, sannan ta ɗaga kai ta kalli Abubakar da ya zo ya tsaya a kanta yana kallonta cike da tausayawa. “Sannu Hafsat, tashi mu je” Sai ta miƙe tsaye, tare da kai hannunta na dama ta ɗauki suit ɗin. Wayar Abubakar ta yi ƙara a sanda suka fito daga office ɗin, hannunsa ya sa a aljihu ya ɗauko sannan ya amsa. “Hello Sharon, howdey?!” Daga cikin wayar Sharon tace. “Fine sir... Kuliya ne ya yi hatsari jiya, sannan an kwantar da shi a asibiti...” “What?!, hatsari?!, a ina?, wani asibiti yake?” Ya katseta tare da jero mata tambayoyin. A lokaci guda kuma ya dakata da tafiyar da yake, hakan yasa Mishal ma dakatawa tana kallonsa. “Nizamiye hospital” Sai ya yi shiru. “Yanzu haka ina cikin Nizamiye hospital ɗin, wani ɗaki yake ?” “Room No.18” ”Nagode Sharon” Kuma daga haka ya sauƙe wayar. “Ukti abokina ba shi da lafiya, muje mu duba shi” Mishal ba ta damu da san sanin waye abokin nasa ba, dan haka kawai ta bi bayansa. *Room No.18, Nizamaye hospital* KULIYA POV. “Yanzu miye amfanin irin wanna?!, Ka daba abun da ya sameka ka gani da idonka, kullum ina cikin maka nasiha a kan yawan gudun da kake da mota, amma sam baka kulawa, yanzu ga irinta nan!...” Anna ce ke ta balbale shi da faɗa, yayin da take tsaye a kansa, kusa da gadon marasa lafiyar da yake zaune a kai. Ya jingina bayansa da gadon, gefen fuskartsa na manne da plaster, hannunsa da kuma wuyansa gaba ɗaya rauni ne. Allah ne ma ya kawo masa abun da sauƙi, dan a sanda wannan babbar motar ta daki tasa sai Allah yasa ya fita ta wundo, sanda motar ta tashi sama. Bayan ya faɗo sai ya gangara bakin titi, hakan ne ma yasa ya ji raunikan jikinsa. Kuma a sanda jama'a suka kawo masa ɗauki ya suma, don haka bai farka ba sai cikin daren, shi ne ya tsinci kansa a asibiti. “Yanzu idan ka ga motar taka ba za'a ce ɗan adam ya fita daga cikinta ba, saboda yanda ta kwankwatse!...” Anna ta ci gaba da faɗi cikin faɗan da take, a hankali ya ɗaga kansa ya kalleta, sannan ya ce. “Ki yi haƙuri Anna, amma ni ban san daga inda motar take ba, kawai da...” “Ina za ka sani?, ai ba za ka sani ba!” Kuma tana kaiwa nan ta figi jakarta ta fita, dan ba za ta iya jurewa ba, Aliyu kaɗai ya rage mata a duniya, duk da ba ita ta haife shi ba, amma ta na sansa, tana masa so irin na ɗa da uwa. Gawara ta nuna masa fushinta a kan abinda ya yi, wata ƙila ya fahimci kuskurensa ya gyara. A hankali Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya shafa kansa. Duk yan da aka yi wannan haɗarin shiryyaye ne, dole ne ma wani ne ya shirya shi. Kuma ko kokonto ba ya yi, imma dai waɗan da ya taɓa sakawa ciki matsala ne, ko kuma waɗanda yake tunkara a yanzu. Kan nasa ya sauƙe shafawa, sannan ya kalli side drawer, inda wayarsa da sauran kayan da ke jikinsa a jiyan suke aje. Hannu ya kai ya ɗauki wayarsa da ya buɗeta tun jiya ya ga yanda ta farfashe. Bai damu da fashewarta ba, ya shiga daddanawa, duk da bata dannuwa da daɗin rai. Lambar Ram ya nemo, wani ma'aikacinsu wanda ya san kan computer, kuma ɗan baiwa wanda yake aikin ɓadda kama. “Easy...” Ya amsa gaisuwar da Ram ɗin ke masa bayan ya ɗaga kiran. Ya ɗaga kafaɗarasa a hankali,sannan yace. “Me ka gano ?” “Sir na samo location ɗin, sun sauƙa ne a wani gida dake Abacha road” Muryar Ram ɗin ta faɗa daga cikin wayar. A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa, sannan ya kashe wayar ba tare da yace komai ba. Ya kai hannu ya aje wayar tasa, kuma a dai-dai lokacin ne, ƙofar ɗakin ta buɗe. Abubakar ya fara shigowa, biye da shi wata yarinya ce, mai kama da Abubakar ɗin, sai dai kuma ita yafinyar ta fi Abubakar ɗin hasken fata da kuma kyau. Zuciyarsa ta faɗa masa cewar yarinyar na da kyau, wani irin sihirtaccen kyau, wanda a kallo ɗaya za ka tabbatar da cewa ƙwarai, tana da kyau. Amma kuma shi ba ya san raini, shi yasa bai ciki shiga sabgar mata ba, musamman wannan da ya gane cewa ita ce ƙanwar Abubakar ɗin da yake yawan masa zancenta. Kansa ya kawar yayin da Abubakar ɗin ya miƙo masa hannu alamun su gaisa. Gaisawar suka yi yana wani basarwa. Kallo ɗaya Mishal ta masa ta sheƙar, dan ta ga alamun wannan mutumin ɗan raini ne, amma duk da haka sai wani ɓari na cikin zuciyarta wanda yake me hankali ya ce mata; ko ba komai ai abokin Akinta ne, kuma da gani ya girme mata, dan haka ya kamata ta gaida shi. Ciki-ciki kamar me ciwon baki tace. “Ina kwana...” Wani abu me kama da igiya ya ɗaure zuciyar Kuliya a ma'ajinta, ya ji kamar zuciyarsa ta gaza, ya ji yana san ya sake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112