Chapter 71
Chapter 71
ci gaba da tsayiwa a bakin ƙofar, har kusan shuɗewar muntuna biyar, kafin ta ƙara bugawa. A wannan karon magana ya yi. “Shigo!” Ta murɗa handle ɗin a hakankali, sannan ta shiga, tsaye ta ganshi jikin wani shelf ya na duba takardu, a karo na farko kenan da ta fara shiga ɗakinsa. Kallonta yake kamar yanda take kallonsa. Hannunsa na dama riƙe da wani littafi, da a jikin covernsa aka rubuta 'I was never yours'. “Ina kwana” Ta gaida shi kanta a ƙasa, kamar ba Mishal ba, don a duk sanda za ta ganshi sai ya ƙara girma a idonta. Kuliya ya ci gaba da kallonta, sanye take da wani wide blue jeans, sai farar top da ta saka, wadda a jikinta aka rubuta 'Believe in your dreams' gashin kanta baje a bayanta, sai band da ta saka daga saman gashin, fuskarta fayau, babu ko da lip balm. “Lafiya, ya jikin nake?” Ya tambaya ya na aje book ɗin hannunsa. Ita fa ta ma manta da ba ta da lafiya, yanda ta yi overdose na maganin nan ba dole ma murar ta gudu ba. Sai ta gyaɗa masa kai. “Na ji sauƙi... Na gama abinci, kuma na ga har yanzu... Ba ka fito ba” Iko sai Allah, ita fa a rayuwarta ba ta ƙumbiya-ƙunbiya wurin faɗin abun da ke ranta, amma a karo na farko, sai ga ta tana inda-inda wurin faɗin wani abu. “Aiki nake, shi yasa ban fito ba. Amma na gama, mu je” Ya ƙarshe ya na tsayawa a gabanta, sai ta gyaɗa masa kai sannan ta juya, shi kuma na biye da ita a baya har danning ɗin. Abincin ta zuba masa, sannan ta zuba nata, suna ci ya na mata magana jifa-jifa, wani abu sabo, yau shi ne yake hira, ita kuma uwar 'yan surutun ta yi shiru, ta nutsu, kamar ba ita ba, saɓanin da da idan suna cin abinci ko in sun zauna irin haka ita ce ke masa surutai. Bayan sun kammala cin abincin ya ƙara komawa ɗakinsa, ita kuma sai ta zauna a falo tana kallon tv, yayin da takewa Ayra susa. Garam!, ta ji an bankaɗo ƙofar falon, ba shiri ta miƙe tsaye ta na kallon ƙofar, Jadda ce ta shigo ta na wani muzurai. Hatta Kuliya dake ɗaki sai da ya ji ƙaran turo ƙofar, hakan ya sa ya fito, amma ko kafin ya isa falon ya hangi Jaddan ta na shigowa, hakan ya sa ya ja ya tsaya daga corridorn ya na kallonsu. “Jadda!” Mishal ta kira sunanta. “Eh ni ce jikata. Zuwa na yi na ɗaukeki na tafi da ke. Dan na ga kamar shi kawun naki ba sanki yake ba. Shi ya sa na zo na ɗauke ki...” “Ki ɗauke ni mu je ina?” Mishal ta tambaya a sanda Jaddan ta riƙo tsintiyar hannunta. “Maiduguri nake so mu koma, gwara ki koma can cikin 'yan uwanki, ko karatun ne ma ai sai ki ci gaba da yi” Mishal na girgiza mata kai ta kai hannunta da bata riƙe ba ta kama na Jaddan dake riƙe da nata ta ɓanɓare. “Jadda yanzu fa ni matar aure ce.... Ina kike san na je ba tare da izinin mijina ba ?” Jadda ta rafka salati ta na kama baki. “Ke Hafsat!, wai ke nan daɗin aure kika sani?! Wato ke gaki matar gida ko?, Ub*n me shi wancan matsiyacin ya baki da har kika manta da mu haka?” “Jadda please, shi ɗin mijina ne a yanzu. Ba ki san shi ba amma kina zanginsa, dan haka kada ki sake.Dan idan kika kuma ba zan yi shiru ba” Salatin da Jaddan ta rafka a wannan karon ma ya fi na ɗazu. “Hafsat wai ko bakya cikin hayyacinki ne? Yo in ba haka ba ta ya za ki tsaya kina gaya min waɗanan maganganun kamar wata sa'ar ki?” “Jadda ke ce ba ki riƙe girman ki ba. Wani daɗi zan biki ki bani a Medugurin?, Babu wani abu da za ki iya bani a Meduguri face ki saka ido kina gani jikokinki su ƙarasa lalatamin rayuwar da suka so su lalata min tun farko. Ke a ko da yaushe ba ki da abun faɗi da ya wuce cewa kina son jikokinki, kina san jikokinki, a haka ake san jikan?. Ta wannan hanyar da kika ɗauka za ki iya riƙe ni, saboda sanin halinki ya sa 'yarki ta cikinki kafin ta bar duniya ta gargaɗi yayana da kada ya bari na tashi a wajenki. Yanzu kuma da hankali na kike so na biki mu tafi can?, can ɗin da babu wani me iya bani kariya?” Cike da mamaki Jadda take kallonta, wai yaushe ma Mishal ɗin ta yi hankali har haka?, Kamar ma ba ita ba, ko da yake ai an ce aure na gyara mutum, sannan yakan sa mutum ya nutsu. “Ba za ki biyoni ba kenan?” “Ba zan biki ba, ya fiye min alkairi na zauna a gidan nan, ko da Aliyu zai riƙa dukana ne, da de na biki mu tafi Meduguri, ballantana kuma babu wani abu da mijina ya rage ni da shi. Ko me na buƙata cikin gaggawa yake samar min da shi, bayan haka kuma ina san mijina, to me zai sa na biki?” “Kin yi da 'yar halak” Jadda na faɗin haka ta juya a fusace ta bar gidan, wasu hawaye masu ɗumi suka shiga sauƙowa Mishal a kan kumatu, wai yaushe rayuwarta za ta setu ne?, yaushe ne ita ma za ta samu dawwamammen farin ciki kamar kowa. Hannu ta ji ya kewayeta daga baya, sannan ta ji sauƙar haɓarsa a tsakiyar kanta, kafin ya ƙara janta jikinsa, ba shiri wani kuka me ƙarfi ya kufce mata, ta sake shi kuwa. Kuma cikin gaggawa ta juya ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannayenta suka kewaya ta bayansa, sannan ta ci gaba da yin kukanta me sauti. Kuliya ya ɗora haɓarsa a kanta, sannan ya shiga shafa kanta da hannunsa na dama, hanunusa na hagu kuma ya na shafa bayanta. “Shhhhh! Teddy Bear, komai zai wuce, komai zai wuce....” Haka ya ci gaba da nanata mata a kunnenta, yayin da ita kuma ta ci gaba da rera kukanta a cikin jikinsa, dan kuka ne irin wanda ta jima ba ta yi ba, ba ma za ta iya tuna rabonta da yin irin kukan ba, ko a lokacin rasuwar Abubakar hawaye kawai ta yi, amma kuka irin wannan ba ta saba yinsa ba. *T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.* RAJA POV. Kamar kullum ya nazaune daga balconym ƙofar shiga gidan, ya saka ƙofar gate a gaba ya na ta kallo, ya tsinduma cikin kogin tunani da ya saba shiga, ya na ta linƙaya a ciki, ba tare da sanin madafa ko kuma gaɓar da igiyar kogin za ta kaishi ba. “Zaid!” Muryar Rhoda ta kira shi, hakan ya sa ya juya ya kalleta. “Na samo address ɗin asibitin!”. Be san meke faruwa a kansa ba a lokacin, amma shi dai kawai ya yi fatan ina ma zai lumshe idonsa ya buɗe ya tsinci kansa a cikin asibitin. Wani irin gudu yake da motar, wanda ya wuce na hankali, shi da Rhoda ne, wadda ta saka ido ta na kallonsa kawai, yanda yake gudu da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112