Skip to content

Chapter 72

Chapter 72

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

motar kai kace ce masa aka yi idan ya tafi a hankali duniyar ce za ta tashi ba tare da ya je ya cimmawa abun da yake san gani ba. Cikin wasu 'yan muntuna sai ga su sun iso 'Vinca Hospital'. “Sunanta Rabi'a!” Raja ya faɗi cike da ƙaguwa, yayin da suke tsaye a reception, sai kai kawo yake, Rhoda ta dafa kafaɗarsa cikin san kwantar masa da hankali ya fi a ƙirga, amma sam ba ya fahimtar me take shirin faɗi. “Zaid Aliyu!” Da sauri suka juya daga shi har Rhoda, don ganin mahaluƙin da ya kira shi da wannan sunan, bisa ga mamakinsu, sai ya ga wani abokinsa ne da su ka yi jami'a tare, ba course ɗaya suke offering ba, amma sukan haɗu a cikin makaranta. Duk da ya na cikin wani hali sai da ya yi wa abokin nasa murmushi, haɗi da miƙa masa hanu su gaisa. “Me ya kawoka asibitinmu?” Abokin me suna Huzaifa ya faɗa, Raja ya ɗan sosa kansa. “Wata mara lafiya muke nema...” Bai ko rufe bakinsa ba, receptionist ɗin tace. “Ku yi haƙuri ranka ya daɗe, amma babu mu da mara lafiya me wannan sunan...” Raja ya girgiza kansa. “Kuma an tabbatar muku da ta na nan?” Huzaifa ya tambayi Raja, Raja ya gyaɗa kansa a sanyaye. “Da ga masaniya me ƙarfi muka samu labarin, kuma an tabbatar mana da tana cikin asibitin nan” “Muje office ɗina, wata ƙila akwai wani temako da zan iya maka” Daga haka kuma suka ɗunguma zuwa office ɗin Dr. Huzaifa. Wuri ya nuna musu suka zauna, sannan shi ma ya zauna ya na tambayarsu. “Kamar yaushe kuke ganin an kawota nan?” “Sati uku baya haka...” Rhoda ta bashi amsa,sai ya gyaɗa kansa ya na ɗaukan wayarsa, kira ya yi, kuma bayan wani lokaci sai ga wata nurse ta shigo hannunta riƙe da files. Dr. Huzaifa ya karɓi fle ɗin ya na kallon fuskarta. “Ɗakin nan kika shiga ba?” Ya tambayeta saboda ganin yanda idonta ya yi jajir, alamun dai ta yi kuka, sai nurse ɗin ta sinkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsunta. “Sakina!” Ya kira sunanta, hakan ya sa ta ɗago da kanta ta kalleshi. “Sau nawa zan faɗa miki ki dena shiga ɗakin nan, in har za ki riƙa shiga damuwa irin wannan, me nene amfani zuwa ganinta?” “Na kasa iya hana kai na Dr., a duk sanda zan shiga na dubata sai na zubar da ƙwalla...” Huzaifa ya miƙawa Raja file ɗin, wanda ya kafesu da kallo. “Ki je kawai za mu yi magana daga baya” Kanta ta gyaɗa sannan ta fita daga office ɗin. “Akan wa kuke magana?” Raja ya tambaya hannunsa riƙe da file ɗin da Huzaifan ya miƙa masa. “Wata mara lafiya ce aka kawota asibitin nan, sati uku baya, Wallahi abun tausayi, wasu ne suka mata fyaɗe sannan suka cillar da ita a hanya, mutanen kusa da mu ne suka kawota nan, sati uku kenan amma babu wani nata da ya bayyana... Wannan file ɗin ya na ƙunshe da bayanan kaf marasa lafiyar da aka karɓesu a asibitin nan, a tsakankanin sati uku da suka wuce, ku duba, wata ƙila za ku iya samun wadda kuke nema” Ya ƙarashe ya na musu bayani kan abinda ya sa suka biyoshi, amma sam Raja bai fahimci zancen nasa na biyu ba, wannan maganartasa ta farko ita ce ta sa hankalinsa a kwalba ta kulle, don zuciyarsa ce ta hango masa dacewar bayanen da aka basu, da kuma wanda shi Huzaifan yake faɗa, to ko de ita ce?, amma ta ya za ayi ta kasance ita?. “Ina ne ɗakin mara lafiyar?” Rajan ya tambaya ya na kallonsa, har Huzaifa zai ce wani abu, sai kuma hoton fuskar yarinyar ya haska a cikin kansa, rannan da ya shiga ɗakin don dubata ya kalli fuskarta, a lokacin ya ga kamar ya san fuskar tata a wani wuri, duk da ɗinkin da aka mata a gefen fuskarta, amma ta masa kama da wani wanda ya sani, a yanzu da Raja yake zaune a gabansa, sai fuskarta ta haska a cikin kansa, haɗi da tasa fuskar. “Nan ne!” Huzaifa ya faɗi ya na nuna musu ƙofar ɗakin, Raja ya juyo ya kalli Rhoda, zuciyarsa na dokawa a kunnuwansa, ƙafafunsa suka masa nauyi, don ji yake kamar abun da yake zargi shi ne zai tabbata. Kamar mara lafiya haka ya kai hannunsa ya kama ƙofar ɗakin ya murɗa, tura ƙofar ciki ya yi, sannan ya shiga. Idonsa ƙyam a kan yarinyar dake kwance a kan gadon marasa lafiya, wasu na'urori ne ɗaure a jikinta, kuma babu sautin dake tashi a ɗakin sai na na'urorin. Duk da wani irin fari da ta yi, duk da wani ƙaton yanka da ya gani a gefen fuskarta, duk da gashin kanta da ya yi alamar kamar an yanke, duk da yanda fuskarta ta yi wani irin fayau kamar wadda ta mutu, duk da yanda idanuwanta ke a rufe kamar gawa, bai hana shi gane taba. Kuma ƙwaƙwalwarsa na ganeta, ta hankaɗo masa bayanan Huzaifa na ɗazu. _“Wata mara lafiya ce aka kawota asibitin nan, sati uku baya, Wallahi abun tausayi, wasu ne suka mata fyaɗe sannan suka cillar da ita a hanya, mutanen kusa da mu ne suka kawota nan, sati uku kenan amma babu wani nata da ya bayyana...”_ Nan take ya ji wata ƙara a ƙirjinsa kamar ta tashin bomb, a sanda kalaman suka tsaya, a lokacin ne ƙafafunsa suka ɗauki rawa, haka ma hannayensa, hatta da bakinsa rawa yake, duniyar ta masa. Wani irin shiru, sannan duhu ya mamaye injinan ganinsa. Fyaɗe!?, fyaɗe!?, fyaɗe!?, Ita ma?, kenan ita ma sai da aka samu wani ya aikata mata wannan zalincin?, me ya sa haka?, me ya sa ƙaddararsa take zuwa a haka?, me ya sa tarihi yake shirin maimaita kansa?, me ya sa?, me ya sa?, me ya sa?!... #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *19* ~~~ *Love is; when you hug someone and they feels like home...* *** *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.* A fusace Jadda ta shigo cikin gidan tana famar bambami, kamar wadda ta zauce. Hajjara na zaune a kan kujera tana taunar chewing gum, haɗi da latsa wayarta, wani ɗan iskan kallo ta bi Jaddan da shi, kafin ta ci gaba da kallon wayarta, daga gefen ta kuma Fahima ce zaune ta na wasa, yayin da Hammad ke zaune a kan dinning ya na cin abinci. “Wallahi wannan yaron da aka aurawa Hafsat ya ɓatata, yo in ba haka ba ta ya za ayi na je na ce ta taho mu tafi, amma ta ce ba za ta zo ba?, wata ƙila ma shanyeta ya yi!...” Haka ta dinga sambatu, har ta kai ɗakin da ke a mazaunin nata, ta riga ta yanke shawarar barin garin a yau, don babu abun da za ta zauna ta yi a Abuja, tun da wadda take zaune don itan ta ƙi yarda ta biyota, duk da wahalar da ta sha kafin ta samu adireshin gidan nata. Kuma ta riga da ta yamie shawarar datse ko wace alaƙa dake tsakaninta da Mishal ɗin, tun da ita ba ta da mutunci, wai ita 'yar daɗi miji, tun da ta zaɓi zama da shi ga

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112