Chapter 17
Chapter 17
ki damu, zan ɗau ƙaƙƙwaran mataki kuwa” “Ke Fati, uw*r me kike a ɗakin ne?, dallah ki yi sauri ki fito” Mama ta faɗi cike da masifa tana kallon ƙofar ɗakinsu, Habiba ta shiga soshe-soshen ƙeya. “Amm, Mama na ce Alhajin jiyan nawa ya baki ?” Mama ta juyo ta kalleta tana haɗe rai. “Ni ba na san bita da ƙulli, dubu hamsin ne, ya ce babu kuɗaɗe a hannunsa, zan baki dubu biyar kawai...” Habiba ta yi murmushin yaƙe. “Haka ne, amma dai an kinsa dai ko kuɗin ɗinki shaddara da na ɗinka miki a sallar nan ya fi dubu biyar...” “Ni fa Umma na gaji da gorin da kike min!, kawai dan kina min ɗinki sai ki kafa bina da bita da ƙulli?... Da na ce dole sai kin min ɗinki?... Idan ba ki min ba ma samari na za su min ai!” Kamar Maman ita ce uwa haka takewa Habiban faɗa. “Haba Mama, abun fa ba na ɓacin rai ba ne, ki kwantar da ranki mana” Mama ta ƙara juya kai tana huhhura hanci. Ƙarshen zamanin kenan, dama an sanar da mu cewa; baiwa za ta haifi uwar gijiyarta,to ga kyakkywan misali nan Habiba da Mama. Sannan an ce abun da ka yi shi za'a maka, hakan ce ke faru da rayuwar gidan Ɗan Lami, amma shi sam bai lura da hakan ba, dan ba iyalan nasa ne a gabansa ba. (Allah ya fihsemu turba mai kyau🙏). Bayan an sauƙo da ga idi, Saratu da Rabi gida suka dawo, in da Mama ta wuce yawon gantalinta, Habiba da su Fati ma gidan suka dawo. Kuma tana dawowa ta laftawa Rabi aikin abincin sallah, haka Rabi ta cire sabon kayanta ta hau aikin ba ji ba gani, duk da Saratu na tayata da wani abu. Da haka har suka yi suka gama, kuma bayan sun gama ba'a bawa Rabin abincin ba, sai kusan la'asar aka ɗan zuba mata kaɗan a kwano, wai duk dan a ƙuntata mata. Naman da kajin data soya ma ba'a saka mata ba, sai wanda Habiban ta ci ta bari, kuma ita hakan bai dameta ba, don bata damu da cin kaza ba, tafi san kifi, kaza bata birgeta a rayuwa. Duk da haka sai da Anti Saratu ta ɗiba mata naman ta bata, tace mata ta ci, ai da kuɗin da ta nema aka sayi naman. Bata san yi mata musu shi yasa ta ci ɗin, ba wai don naman ya mata daɗi ba. Da la'asar Zara ta shigo gidan tace ta zo su je yawon zaga gari, da farko sai da Habiba ta hana, amma da Saratu tayi uwa tayi makarɓiya sai ta haƙura ta barta. A wurin Rabi wannan sallahr ta musamman ce. Saboda tana cikin farin ciki, komai na tafiya mata dai-dai. Har ta fara ganin kamar wahalarta ta ƙare a rayuwa. Abun da ba ta sani ba shi ne; wasu abubuwan ma yanzu ne suka soma, wata wahalar ma bata shigeta ba tukkuna, wani ciwon ma bai sameta ba har yanzu!. Wani sabon kukan ƙunci da damuwa na nan tafe a gaba. Akwai ƙunci da baƙin ciki a rayuwa, akwai damuwa da iftila'i a rayuwa, akwai damuwa a akan wata damuwar. Ƙaddarar kowa da ban ce, kamar yanda Labarin kowa yake da ban. Labarinta yanzu zai soma, haka mahaifiyarta ta faɗa. Kuma yanzu zai soma ɗin. Don ba ayi komai ba ma, labarinta zai sauya tare da faruwar wata ƙaddara mai zuwa nan da 'yan kwanaki masu zuwa, ƙaddarar da za ta sauya komai, ta tarwatsa komai, sannan ta gyara wasu abubuwan. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #Taurariwriters °°°°°°°°°°°°°°°°° *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *05* ~~~ *You never have to pretend with me, just give me your raw truth, all your imperfections and fears, and i will show you how beautifully broken pieces fit together* *** *Badawa layout, Kano...* RAJA POV. Kayan da ya san zai buƙata yake shiryawa a cikin jakarsa ta matafiya. Hannunsa na dama ne ya janyowa wata riga, tahowar rigar ya yi dai-dai da faɗowar wani hoto. Kansa ya sunkuyar ƙasa, idonsa ya sauƙa a kan fuskokin da ke jikin hoton. Waɗanan lumsassun idanuwan nasa suka kafe hoton suna kallo. Mutum uku ne a jikin hoton, na farko fuskarsa ce, waɗanan gray ƙwayar idanun nasa ce tasa ya gane hakan, sai kuma fuskar Aliyu, sannan ta Momma, wato mahaifiyarsu. A hankali ya aje rigar, sannan ya tsugunna ya ɗauki hoton, har wa yau bai manta ranar da aka ɗauki hoton ba. _“Kai Aliyu tsaye daga nan..... Kai kuma Zaid ka tsaya a haka....”_ Wannan shi ne abinda ta faɗi a wancan lokacin. Dariyar da suka yi a wancan lokacin ta shuga amsa kuwwa a cikin kunnuwansa. Ba shiri ya yi saurin cilla hoton cikin jakar da zai yi tafiyar. Zuwa yanzu hoton ya sauya a idonsa, daga cikin falon gidan da aka musu hoton, zuwa baƙin gidan da wuta ta gama cinyewa. Wayarsa ce ta shiga ruri, hakan yasa dubansa ya kai kanta. 'UCHECHI' Shi ne sunan dake yawo a kan screen ɗin, duk yanda aka yi yasan zuwa gidan ta yi. Rhoda da su Zuzu suka hanata shigowa. Sai kawai ya fasa ɗaga kiran nata ya katse kiran, sannan ya aikawa Rhoda kira. Daga can harabar gidan kuwa, Rhoda da su Alandi ne suka tare bakin gate, suna zagin Uchechi, tare da faɗa mata ba fa za su barta ta shiga cikin gidan ba. “Ke ki bar nan!....” Cewar Rhoda tana zare mata ido, Uchechi da ta kai iya wuya, ganin ta kira wayar Raja ya katse mata tace. “Ba zan tafi ba, sai kun bar ni na ga masoyina...” “Sh*giya 'yar wahala kawai... Karya me bin maza... A haka za ki ƙare....” Jagwado ya faɗi cikin muryarsa dake nuna cewa a buge yake. “Duk abinda za ku faɗa ku, faɗa, ni dai ba zan tafi ba... har sai kun barni na ganshi...” “Ai ko za ki riɓe a nan... 'Yar akuya kawai...” Alandi ya faɗi yana maka mata harara kamar wata mace. Me gadi na daga bayansu yana kallonsu, kusan kullum ita Uchechin sai ta zo gidan. Kuma da zarar su Rhodan suna nan basa barinta ta shiga. “Rhoda! Let her in!” Muryar Raja ta faɗi daga bayansu. Cike da takaici Rhoda ta juya ta kalleshi, Allah ya sani ta tsani yarinyar nan, bata santa ko kaɗan.bShi yasa bata san ta riƙa raɓar Rajan. Kiran wayar Rhoda da ya yi ya ji a kashe ne yasa shi fitowa don ya musu magana kan su barta ta shigo, yasan in har be yi hakan ba za su barta ta shigo ɗin ba. Uchechi ta yi murmushi cikin makawa Rhoda harara, ta raɓa su ta isa gaban Rajan har da ɗan gudunta. Rungume shi ta yi a kan idonsu, wai duk dam su ji haushi. Shagwaɓa ta shiga masa irin wadda ta saba har suka shige cikin gidan. Rhoda ta saki wani hucin takaici, ji take kamar ta bi bayansu ta maƙure Uchechin, ta karta har lahira kowa ma ya huta. “Kar ki damu Rho, muna zaune a nan zamu ji kansu, ke dai ki zuba musu ido kawai, in har ta zaƙe yanzu Raja zai saita mata hanya...” Zuzu ya faɗi dan ya kwantarwa da Rhodan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112