Skip to content

Chapter 33

Chapter 33

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
Download Book

suka saba kwana, ya zaunar da shi a bakin katifarsu, sannan ya koma bayan gidan ya ɗauko ledar ƙosan da Allah ya temakesu bai zube ba, ya haɗo da wani plate da suka saba cin abinci a ciki, sannan ya ɗebo masa ruwa. Ya dawo ya zauna kusa da shi, ya juye masa ƙosan a plate, tare da tura masa shi gabansa. “Ka ci Aliyu” Aliyu ya kalli ƙosan, sannan ya kalli yayansa, ƙwarin gwiwarsa, farin cikinsa, uwa, ubansa duka a halin yanzu Zaid ne. Sai ya kai hannu ya ɗauko ƙosan guda ɗaya, me makon ya kai bakinsa, sai ya kai setin bakin Zaid. Zaid ya kalli ƙosan, sannan ya kalli Aliyu, wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo masa, a hankali ya buɗe bakinsa, Aliyun ya ƙarasa saka masa ƙosan, yana taunawa hawayen na ƙara kwaranyo masa. Ya kai hannunsa ya ɗauko ƙosan shi ma, sannan ya kaiwa Aliyun baki, Aliyu ya karɓa ya na murmushi, da haka suka cinye sannan suka sha ruwa. Sai kuma suka zauna suna biya tilawar islamiyyarsu, dan bayan faruwar iftila'in nan sun ɗan je. A lokacin biyan kuɗin wata ne malaman suka korosu, makaranatar safe kuwa l ba su kusanceta ba, dan sunsan babu me barinsu su shiga basu da uniform, kuma ga shi term ya kawo ƙarashe. Karatun ƙur'anin dai shi suke ɗan taɓawa da ka. Bayan sun yi sallahr azahar, Zaid yace zai fita ya nemo musu abin da za su ci na rana. “Zaid ka tafi da ni... Ba na san zama ni ɗaya” Cewar Aliyu ya na miƙewa, Zaid ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya, sannan yace. “To muje” Aliyu ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya yana kama hannun Zaid. Har suka fito daga cikin gidan, Zaid ya ɗauki wani ƙyallen tsumma ya ɗaure ƙofar gidan, kana suka kama hanyar bakin titi. Idan daga nesa ka gansu za ka ce mutum ɗaya ne, kasancewar komai nasu kala ɗaya ne, farin fatar, kyan fuskar, hatta da takunsu iri ɗaya suke, na Zaid ne kawai yafi nutsuwa. Idan wannan ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sai ka ga wannan ma ya ɗaga, abun nasu gwanin ban sha'awa. A sanda suka fita titin, Zaid ya nunawa Aliyu wuri yace masa ya zauna, shi kuma zai je ya na barar. Aliyu ya zauna yana kallon yayansa, yanda yake miƙa hannu yabna barar sai da ya sa shi kuka. Wai yanzu su ne rayuwarsu ta koma haka, su ɗin da suke da gata, suke da uwa, wadda ta ɗauke musu kewar uba, su ɗin da ba su nemi komai sun rasa ba, amma cikin ƙiftawar ido, komai ya sauya, LABARINSU ya sauya, rayuwar ma baki ɗayanta ta sauya. “A taimaka mana sadaka fi sabillilahi...” Cewar Zaid yana miƙawa wani me shago hannu, mutumin ya miƙe a fusace. “Kai! Ba ɗazu ma ka zo ba?!...” Kafin ya ƙarasa yaron shagonsa yace. “Jiya ma sai da ya zo” “Sh*ge, da ma da irinku ake haɗa baki ana mana sata, bar nan wurin!” Ya ƙarashe yana hankaɗashi, har sai da Zaid ɗin ya faɗi ƙasa, da yake hakan ba komai ba ne a wurinsa, sai ya miƙe yana bawa mutumin haƙuri, don ba yau aka fara masa irin hakan ba. Kamar wucewar walƙiya haka ya ga tahowar Aliyu da gudu, kuma kafin ya fahimci abun da Aliyun ke ƙoƙarin yi, har Aliyun ya yi tsallen albarka, ya kifawa me shagon nan mari. “Kut!, Babbar buhun ub*ncan!, kayyasa! Ni ka mara yaro ?!” Cewar me shagon yana kama baki. Aliyu da ya gama fusata a sanda ya ga an hankaɗa masa ɗan uwa yace. “Eh ɗin, na mareka, ko akwai abun da za ka iya?” Ya faɗi idonsa ƙyam a kan mutumin, babu wani alamun tsoro tare da shi, ji yake ma kamar zai iya kikkifa masa marin da ya fi haka, ga shi dai ba shekaru gareshi masu yawa ba, amma zafin zuciyarsa ya fi na ɗan shekara ashirin, ji yake a kan yayansa babu abun da ba zai iya ba. Ko dan sunansa Aliyu ne ?, Oho. Zaid ya kamo hannunsa ya na jansa baya. “Zo mu tafi Aliyu...” “Rabu da ni Zaid, sai na nuna masa martaba da kimarka a wajena” Nan fa me shagon nan ya shiga zage-zage yana masifa, har maƙotan shagunansa suka fito. Ɗaya daga cikin masu shagunan ne ya kamo hannunsu Zaid, ya ja su zuwa gefe. “Ni kuwa yara ku ba 'ya'yan wannan likitar ba ne ta bayan layi ?” Mutumin ya tambaya, yana ganin kammanin customern tasa a fuskar kowannensu. Aliyu bai iya bashi amsa ba, kasancewar zuciyarsa na tafarfasa, har yanzu ji yake marin da ya yi wa me shagon nan bai wadatar ba, kamar ya na buƙatar a ƙara masa, soboda abinda ya yiwa Zaid ɗinsa. Zaid ne ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan yace. “Eh, mu yaranta ne” “Kwana biyu ba na ganinta, fatan dai lafiya ?” Zaid ya sunkuyar da kansa ƙasa. “Yau wata biyar kenan da rasuwarta, gobara ce ta kama a gidanmu, kuma a lokacin da gobarar ta kama tana cikin gidan...” “Innallillahi wa inna ilaihi raji'un... Wallahi yara ban sani ba.... To yanzu ku da wa kuke zaune?” “Ba mu da kowa, mu kaɗai ne” “Subhannallahi, shi yasa kuke bara ?” Zaid ya gyaɗa masa kai, don da ma shi ne yake bashi amsar. “To kunga, ku zo ku zauna a shagona, na sai muku abinci ku ci, da yamma idan Allah ya kaimu, zan kaiku gidan marayu, ai za ku iya zama a can ko ?” Da sauri suka kalleshi, sannan kuma suka kalli juna, ba musu suka gyaɗa masa kai. Mutumin me suna Ila ya yi murmushi, har wa yau ya na tuna irin alkairin mahaifiyarsu gareshi. Domin akwai wata rana da ta taɓa zuwa shagonsa ta iskeshi ya yi tagumi, ta tambayarsa; lafiya? shi ne ya shaida mata da matarsa ce ta shaihu, ga shi ko na yanka ba shi da shi. Har wa yau ya na iya hango murmushin da ta yi a lokacin, sannan ta lale maƙudan kuɗaɗe ta damƙa masa, tare da faɗin a sha hidumar bikin suna lafiya. Har da kukansa a lokacin, don Allah ya sani yanda yake a cikin buƙatar kuɗi. Da ma jarin nasa ma bai taka kara ya karya ba. * “Na ji buƙatarka Malam Ila, sai dai a gaskiyar batu, ba mu da gurin zaman mutum biyu, yaro ɗaya kawai za mu iya karɓa, saboda yanzu haka ma gidan nan a cike yake da yara, yaro ɗayan ma za mu karɓeshi ne kawai dan ka dage” Cewar shugar gidan marayun da Malam Ila ya kai su Zaid, zaune take a kan kujera, yayin da take kallon Malam Ila dake tsallaken kujerarta, Zaid da Aliyu kuma na tsaye daga bayansa. A yau sun ci abincin da rabonsu da cin irinsa tun watanni biyar da suka wuce, wato ranar da Mommansu ta rasu, Malam Ila sai da ya tabbatar da sun ci sun ƙoshi, sannan ya kawo su nan wurin. Cike da fatan zuwansu wurin zai sauya rayuwarsu, amma maganar da matar ta yi ita ta murmushe wannan fatan nasu har garinsa. “To yara kun dai ji... Yanzu mecece mafita ?” Cewar Malam Ila yana juyowa ya kallesu. “Malam Ila mun gode da temakonka.... A gaskiya ba

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112