Skip to content

Chapter 80

Chapter 80

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

wata magana ita kuma ta na dariya. Nan take Kuliya ya ji wani abu me kama da allura ya caki ƙahon zuciyarsa, ya ji kamar ya ƙarasa inda suke ya kwarfe yaron da mari, hakan ya sa duk sauran bayanan da me gadin ke masa ba ya fahimta. Idonsa ƙuri a kansu, ya na kallon ikon Allah, juyowar da Mishal za ta yi karaf suka haɗa ido, hakan ya sa ɗan gutin murmushin da take ya ɗauke ɗip, kamar ruwan sama. Ta san yau akwai dabi a gidan nan. *No.181, Guzape, Abuja...* *10:30 PM.* MISHAL POV. Safa da marwa take a ƙofar ɗakin Kuliya, tun ɗazu ta ya dawo, kuma ta yi maganar duniyar nan amma ya ƙi kulata, ko abincinta ya ƙi ci, ta rasa inda za ta sa kanta, ba ta san ya za ta yi ba, amma dole ta bashi haƙuri a daren nan, dole su sulhunta a daren nan, dan ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, ta riga da ta saba da kwana tare shi, bata jin yau za ta iya bacci idan babu shi kusa da ita. Juyowa ta yi ta kalli ƙofar, sai da ta shaƙi iska, sannan ta furzar, hannunta har karkarwa yake wajen buga ƙofar, amma haka ya mata banza, kuma ya na jinta, dan ya na ganinta ta ƙaramar camerar dake maƙale a ƙofar ɗakin, wadda ido ba ya iya ganinta, kuma ba ma iyaka ƙofar ɗakin nasa kawai ke ɗauke da camerar ba, akwaita a gurare da dama a cikin gidan, kuma ta cikinta ne ya ga abun da ya faru tsakaninta da su Siyama a waccan ranar, a sanda ya ga vedion ba ƙaramin mamaki ya yi ba. Hannun Mishal ya ƙara buga ƙofar a kusan karo na tara, zuwa lokacin har ta fara hawaye. Kuma ganin ta fara kukan ne ya sa zuciyarsa karyewa, dan haka ya miƙe ya nufi ƙofar, sai da ya yi kicin-kicin da fuskarsa, sannan ya buɗe ƙofar ya na wani cin magani. “Ya aka yi?” Ya tambaya ya na kallon fuskarta wadda ta yi ja saboda kuka, kallonsa ta ci gaba da yi tana kuka. Da ta rasa abun yi sai kawai ta faɗa jikinsa, ta saka hannayenta ta kewaye shi ta baya, sannan ta saki kuka me sauti, Kuliya ya ƙi ya riƙeta, duk da zuciyarsa na motsawa da ko wani ɗigon hawaye da take zubarwa. Jin bai riƙeta ba ya sa Mishal ɗagowa daga jikinsa ta na jan zuciya. “Abu Aswad ka yi haƙuri” Kansa ya ɗauke ya na wani shan ƙamshi. “I am sorry” Ya ƙi ko kallonta. Haka ta yi ta bashi haƙuri amma ya ƙi ya ko kalleta, da ta gaji da magiyar sai ta juya jiki a sanyaye tana hawaye, taku biyu ta yi ya sa hannunsa ya janyota, bata tashi tsayawa a ko ina ba sai cikin jikinsa, tana jin hannayensa a bayanta kuwa ta sakar masa kuka sosai. “Ka yi haƙuri please... Note book ɗin chemistry fa kawai ya tambayeni...” Kuliya ya ƙara matseta a cikin jikinsa. “Dariya fa na ga kuna yi Teddy Bear, kinsan ai dole na ji ba daɗi” Ita ma sai ta ƙara riƙe shi ta na faɗin. “Wallahi ba komai muke ba, ka yarda da ni, ai ni ma na san hakkin aure, ba zan tsaya da wani saurayin ba... Ka yi haƙuri” Kuliya ya saketa ya na goge mata fuska, ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na faɗin. “Is okay, ki dena kukan to” “Ka yafe min?” Ya gyaɗa mata kai ya na ɗaga kafaɗa. “Na yafe miki, amma kada ki ƙara masa magana... Ba ma shi kaɗai ba, ko wani yaro a school ɗinku babu ke babu shi” Ta gyaɗa masa kai ta na jan hanci, fuskarta ya riƙe ya na kallonta, kafin ya sunkuyo da fuskarsa kan tata, sannan a hankali ya haɗe bakinsa da nata ya na kissing, hakan ya sa ba shiri Mishal ta saka hannayenta ta kewaye wuyansa ta baya tana mayar masa martani. *Unguwar Jama'are, Haɗejia...* *08:40 PM.* Kusan mutum gome ne suka sa salati a tare, bayan da Rabi'a ta kai ƙarshen labarinta, tun bayan barinta gidan shekaru biyar baya har zuwa yau babu abun da ta ɓoye musu. A ɗazu da yamma ta sauƙa a garin Haɗejia, farkon ganinta sai da 'yan uwan nata suka yi murna, amma kuma ganin yanayinta da kuma damejin dake fuskarta ne ya sace musu gwiwa, haka suka shiga jero mata ruwan tambayoyi, amma bata samu ta amsawa kowa ba. Har zuwa ƙarfe takwas, kafin kakanta ya aiko kiranta, kuma daga lokacin da ta iso falon kakan nata sai ta tarar da ba shi kaɗai ne a ciki ba, duka kawunnenta da 'yan uwan kakan nata duka suna ɗakin. Sannan ko da suka tambayeta ba ta ɓoye musu komai ba, tun daga wahalar da ta yi ta sha a gidansu, har zuwa aikatau ɗin da take, har kan fyaɗen da aka mata, zuwa korarta da Ɗan Lami ya yi. Kakanta Alhaji Ali ya ci gaba da kallonta, wani abu na yawo a cikin kansa, ɓaro-ɓaro ya na ganin yanda tarihi ke maimaita kansa, irin abun da ya faru da me sunanta ne ya faru da ita, 'yarsa ta cikinsa da ya kora saboda ta yi cikin da ba na aure ba, wanda ya zo ya yi nadama daga baya, har ya shiga fafutukar nemanta, amma kuma ko da ya samu inda take sai aka sanar da shi ya je a ƙurrarren lokaci, don kuwa ita Rabi'an ta rasu, yaranta 'yan biyu da aka ce ta haifa kuma ba a san duniyar da suka shiga ba. Tsoho Alhaji Ali ya ji ƙwalla ta cika idonsa. “Irin cin amanar da Ɗan Lami zai mana kenan?, Bayin Allah a nan a gabanku fa nake tura masa kuɗi duk sallah na ce a yi wa Rabu ɗinkin sallah, amma kun ji, rabonta da sabin kaya tun wanɗanda ta bar gidan nan da su” Cewar kawu Abdullahi, babban ɗa a wurin Alhji Ali, haka kuma babban wa a wurin su Maryam. “Ni ai ba wannan ne ya bani mamaki ba, kadarorin Maryam ɗin da ya ɗaga ya siyar su ne suka ba ni mamaki” Cewar Kawu Hassan, ƙani a wurin kawu Abdullahi. Haka dai suka ci gaba da maida zance, har da masu cewa ƙarar Ɗan Lami ɗin ya kamata a yi, Rabi kuwa jinsu kawai take, dan ita kaf duniya yanzu ba wannan ne a gabanta ba, farin cikinta ɗaya, da danginta suka karɓeta, suka nuna mata ƙauna kamar yanda suka saba. Sai kuma matsalarta; Raja!. Har yanzu tunaninsa bai bar cikin kanta ba, har yanzu ta na iya hango fuskarsa a cikin kanta, har yanzu ta na iya hango kanta a tsakanin hannayensa, har yanzu akwai sansa a cikin zuciyarta, amma ko ta ƙi ko ta so dole ta cire wannan son, don ba zai amfaneta da komai ba, face ya wagalar da ita, aure tsakaninta da makashi ɗan daba ba abu ne me iyuwa ba, wai ita ya aka yi ma ta yarda da shi har haka?, ina hankalinta ya shiga da har ta bari zuciyarta ta yarda da shi, ta inda har ta kasa tambayarsa wani aiki yake. Me ya sa idonta ya rufe ta

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112