Chapter 90
Chapter 90
tace. “A haka kake so na? Ni fa ba kamar sauran mata ba ce!. Ina da banbanci da su. Maza biyar... Biyar ne suka haikemin... A haka kake sona?... To ka sani ni ba ni da wannan martabar ta 'ya mace... Ban mallaki komai ba sai raina, idan ka ce za ka ci gaba da kusanta tata irin haka ina me tabbatar maka da cewar ran nawa ma zan rasa shi nan ba da jimawa ba!” Ta faɗi hakan ne don ta tunzurashi ya rabu da ita, kuma ta na ganin kamar ya manta abun da ya faru da ita ne, don da ace ya na tunawa da ba zai aureta a yadda take ba, shi ya sa ta yi ƙoƙarin tunatar da shi. Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na shafa sumar kansa, me take so yace ne? Wata hanya zai bi don ya ganar da ita kalar san da yake mata?, da wani yare take so ya yi magana dan ta fahimci kalar son da yake mata?, tun kafin tsautsayin nan ya auku yake santa, yanzu kuma kawai dan ƙaddara ta sameta sai ya rabu da ita?, wannan ba me iyuwa ba ne, santa a cikin jikinsa yake, ba ya jin zai iya rabuwa da santa ko me za ta zama a duniya, kuma ya na fatan bugu na ƙarshe da zuciyarsa za ta yi ya kasance da sunanta ne. Lips ɗinsa ya lasa ya na sakin sumar kansa da ya riƙe. “Ammata, ni...” Ya nuna kansa, sannan ya ci gaba. “Ba dan komai nake sanki ba. Ba na sanki dan kina da wani abu. Bana sanki dan kin mallaki wani abu. Haka kuma ba na sanki dan ina buƙatar ki wadata ni da wani abu. Zuciyarki kawai nake buƙata Adawiyya!. Da zarar kin mallakamin ita zan nuna miki so. Zan nuna miki yanda ake so. Zan koyar dake so. Zan nuna miki yanda ƙaryyayar zuciya, kan haɗe ta dawo me kyau fiye da sabuwa. Zan tabbatar da na ƙawata duniyarki Ammata. Ko da sau ɗaya ne. Dan Allah, ki gwada ni... Ki gwada mallakamin zuciyarki ki ga kamun ludayina. Na roƙeki, Please!” Rabi ta buɗe idanunwata dake a lumshe ƙwalla wata na bin wata. Idon nata ta sauƙe a kan Raja dake durƙushe kan gwiwoyinsa a gabanta, ya na roƙonta abun da za ta iya mallaka masa cikin sauƙi. Ya Allah! Me ya sa wai ita nata ƙaddarorin basu da sauƙi ne?. Ta san da cewa soyyayar Zaid na ɗaya daga cikin ƙaddarorinta na duniya, wannan haka yake, kuma a rubuce yake. Durƙusawar ita ma ta yi a gabansa ta na kallon idanuwansa. “Raj ni ba ni da wani abu da zan baka. Fanko!.... Fanko ce ni, na zama wata kala, saboda kwai ƙaddara ta faɗa min. Ƙaddarar da ba ni na tsrawa kaina ba, ƙaddara ce fa Raj, ƙaddara ce, amma haka Yaya ya guje ni saboda wannan ƙaddarar da ban jarabci kaina da ita ba. kuma na san ko ba Yaya ba babu wanda zai iya aurena a yadda nake, kai ma kawai de ka dage ne. Amma ni da kai ba mu dace ba...” Kafin ta kai ƙarshen kalaminta, Zaid ya saka hannyensa duka biyu ya janyota cikin jikinsa, tare da haɗe bakinsa da nata, ƙwalla me ɗumi na sauƙa daga idon ko wannensu, Rabi'a ta kama bayan rigarsa gam, dan ji take kamar za ta zame daga hannayensa, kamar ƙasa ce za ta tsage biyu, ita kuma ta rufta ciki. A hankali Zaid ya saki bakinta ya na rungumeta, tare da shafa sumar kanta dake cikin ɗankwali. “I adore you Adawiyya, i na sanki ko da ba kya gani. Ina sanki ko da ba ki da ƙafafu. Ina sanki ko da ba ki da hannaye. Adawiyya ko da mutuwa kika yi ba zan dena sanki ba... I love all of you!” Kalamansa ba ƙaramin tasiri suka yi a zuciyar Rabi ba, don tsabar tasirin da suka yi, Rabi'a ba ta san sanda ta ɗago da hannyenta ta ɗora su a kan bayan Zaid ba, ta na ƙara ƙanƙameshi a cikin jikinta, tare da ƙarawa kukanta sauti. Sai de kuma cikin sakan ɗaya... Biyu... Uku... A cikin na ukun ta yi sauri ta tureshi, saboda wannan fuskar tasa da ta hango, fuskarsa a lokacin da ya harbi wani bawan Allah. Da sauri ta miƙe da gudu ta bar kitchen ɗin. Ɗakin da yake a matsayin nata ta faɗa tana bankowa ƙofar. Tare da jingina a jikin ƙofa, ta silale ƙasa tana fashewa da kukan da ba ta san daga ina yake fitowa ba, ƙafafunta ta takure a jikinta tana sunkuyar da kanta cikin kuka. Ita da Allah zai ɗau ranta ma da sai abun ya fi mata sauƙi, ƙaddarorinta suna da tsauri, ga su kuma a laye, wata kan wata. Har ta bar kitchen ɗin kan Raja a sunkuye yake, da ƙyar ya samu ya ja da baya zuwa jikin cabinet, ya jingina da ita, sai sauƙe numfashi yake da sauri-sauri. Zai iya cewa a karo na farko kenan a rayuwarsa da ya yi nadamar shiga aikin DSS, wai me ya sa?, me ya sa komai nasa akan soyyayar Adawiyya yake da wahala haka?, ya tabbatar ba dan wannan aikin ba, da ba za ta ganshi ya harbi wani ba, da ba za ta ƙishi tana masa kallon makashi kamar haka ba. Duk sai ma ya ji ya tsani rayuwar, ji yake kamar kansa na tiriri. Cike da fusata ya ɗaga hannunsa na dama ya na dukan cabinet din dake bayansa. Ya gaji, dole ne ya ƙarƙare aikin nan cikin wannan satin, dole ya kawo ƙarshen komai. * Rabi'a na zaune a falo tana kallo. Jin wani sauti me kama da ƙaran kiran waya ya sa ta juyo ta kalli ƙofar ɗakin Zaid. Mamaki ne ya kamata a sanda ta fahimci cewa tabbas, sautin kiran waya ne ke tashi daga ɗakin, to be fita ba ne ko kuwa?, ita de ta san sassafe ya fice daga gidan, amma kuma yanzu ga ƙaran kiran waya ta na ji, duk yadda aka yi manta wayar ya yi. Bakinta ta taɓe tare da juyowa ta ci gaba da kallonta, jin sautin kiran wayar na ƙara tashi ya sa ta ƙara waigowa ta kalli ƙofar ɗakin nasa. Ko de wani abu ne yake faru? Ta tambayi kanta a sanda take miƙewa. Ɗakin ta nufa. Sai de bisa ga mamakinta ba ta ga wani abu mekama da waya a ɗakin ba. Har ta juya za ta fita, ƙaran kiran wayar ya ƙara dakatar da ita, hakan ya sa ta juyo ta shiga bin inda sautin ke fita. Can cikin loka ta ji sautin, don haka ta buɗe lokar, sai ta yi arba da wata kalar waya da za ta ce bata taɓa ganin irin ta ba. Har zuwa lokacin wayar na ringing, hannun ta kai ta ɗauki wayar, amma kuma babu lamba bare suna. Gaba ɗaya ta riga ta gama shiga duniyar mamakious, wani irin abu ne haka?. Ɗaga kiran ta yi, tare da kara wayar a kunnenta, shiru ta yi ba tare da tace komai ba, kuma daga ɗayan ɓangaren ma sai ta ji shirun, hakan ya sa ta yi ƙoƙarin sauƙe wayar, sai kuma ta tsinto
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112