Skip to content

Chapter 24

Chapter 24

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
Download Book

ba a tawagarsa kake ba, to fa shi babu ruwansa da kai. Elevator ya shiga, wadda ta kai shi zuwa floor ɗin office ɗinsa. Ya fita daga ciki, kafin ya shiga office ɗinsa, kujerarsa ya ja ya zauna, sannan ya kunna desktop, ya shiga danne-danne. Kafin bayan shuɗewar wasu lokuta, ya ɗauki wayar land line ɗin dake kan table ɗinsa ya aika kira, kuma kalamai biyu kawai ya faɗi sannan ya katse kiran. Bayan ɗan wani lokaci, aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin, gyaran murya ya musu kamar kullum, kafin ƙofar ta buɗe. Sharon, Abubakar da Symon suka shigo, nuni ya musu da kan set ɗin wasu sofa da ke tsakiyar office ɗin, alamin su zauna a can. Zama suka yi, a sanda shi ma ya taso daga kan tasa kujerar, hannunsa riƙe da wasu takardu ya zauna a kusa da su. ya shi ga musu bayani akan abun da ya sa ya kirasu. “Kamar yanda muka riga muka fara wannan binciken, tun farko na sanar muku da rukuni garesu... Sunan ogansu Tomes, yana da yara shida, sannan akwai mace ɗaya a cikinsu... Kuma ana zarginsu da fasaƙwaurin miyagun ƙwayoyi, kisa...” Sai kuma ya yi shiru, yana tauna maganar da zai faɗa ta gaba, dan har wa yau kalmar na masa nauyi a bakinsa, musamman ma idan ya tuna cewa wannan hanyar ita ce silar samuwarsa, ita ce silar zuwansa duniya, ita ce silar raba mahaifiyarsu da farin cikinta. Wannan hanyar ita ce ta sa bayan rasuwar mahaifiyarsu aka rasa wanda zai bawa rayuwarsu agaji, har ta kai ga ya rasa yayansa, ɗan uwansa, mafi soyuwa a ransa. Kafaɗarsa ya ɗaga yana ci gaba. “...Fyaɗe, sai kuma saye da siyarwar miyagun ƙwayoyin... A halin yanzu na yi magana da Ram, ya na tricking location ɗinsu, kuma daga zarar ya gano inda suke, kai tsaye farmaki za mu kai... Ko a mutu ko a yi rai!” Abun da bai sani ba shi ne,wasu lokutan abubuwan da mukan furta su ne ke faruwa, wasu ƙaddarorin kan faru kamar yanda muka ayyana a zukatanmu. Wannan kalaman nasa na da alaƙa da wata ƙaddara da Allah ya hukunta faruwar ta 'yan lukuta ƙalilan da za su zo. Wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, sannan ta saita wasu lamura. A yammacin wannan ranar, bayan lokacin tashinsa a aiki ya yi, yana tuƙi cikin baƙar motarsa ƙirar honda elevate. Hannunsa na dama kan sitiyari, yayin da ɗayan kuma yake kan bakinsa. A hankali ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, yana tsuga gudu a motar tasa, dan dama can shi haka tuƙinsa yake, ba ya tafiya a hankali, kuma hakan ne ke sawa suke raba gari idan za su yi tafiya shi da Anna, don haka take cewa; ita tabna san rayuwarta, ba ta shirya mutuwa ba. Tunanin hakan yasa shi yin murmushi a cikin ransa, a fili kuwa babu komai a kan fuskar tasa, ba fushi yake ba, ba fara'a yake ba, haka kuma ba ƙunci yake ba. Duk ƙwaƙwaffin mutum ba zai iya tsintar abun da ke kwance a kan fuskar tasa ba. Kamar daga sama wata motar ɗiban yashi, ta daki motar tasa daga gefe. Motar tasa ta yi ta dungurawa tana sakewa a kan titin, hakan ya sa ta yi kwatsa-kwatsa tun kafin ta tsaya da dunguwarawar da take. *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja* MISHAL POV. Tsaye take a cikin kitchen, sanye cikin uniform, a hankali hannayenta ke jera kayan abincin da ta gama girkawa a cikin lunch box ɗinta. Ƙofar kitchen ɗin ta buɗe, Hajjara ta shigo tana mata murmushi kamar wancan karon, kuma a yanzun ma sai da ta tsorata, dan ba ta san da me ta zo ba wannan karon. Ƙarasowa ta yi gabanta ta tsaya tana mata wani irin kallo. “Ya akabyi Tsaka?!” Mishal ɗin ta tambaya, tana maida dubanta kan kayan da take jerawar. Sunan ya daki gangar zuciyar Hajjara, amma da ta tuna abin da ya kawota sai kawai ta basar. “Tsaka ba?, za kuwa ki ga ma'anar tsaka” “Ai babu kalar tsakar da ban ga ba... Me haɗa mutum da mutum ai tsaka ne Hajjara!... ko babu wanda ya taɓa baki labari cewar kaf tarihi babu wanda ya kai tsaka iya munafirci?” Ta kira sunanta kai tsaye, kuma tana kallon cikin idonta. Dan ba ta shakkarta ko tsoronta, tsoron sharrinta kawai take. “Yaro man kaza... Ke a tunanin ki za ki iya raba ni da mijina kuma na zauna ina kallonki ?” Mishal ta ɗan yi murmushi tana harɗe hannayenta a ƙirji. “Hajjara... Ke ce kika ɗauke ni a matsayin kishiya, ko da wasa ba na kishi da ke, saboda ban ga dalilin yin hakan ba, na ga kamar jahilcinki na san taɓa miki ƙwaƙwalwa, babu aure tsakanina da mijinki... Kuma kafin ya fara saninki ni ya fara sani... Amma ba zan yi mamaki ba dan kina kishi da ni, tun da 'yar da kika haifa ma kin ƙita saboda tana da nakasa... Me zai sa na ji haushi dan ni kin ƙini?” A wasu lokutan duk da ƙarancin shekarun Mishal da kuma yarintarta tana da hankali, dan wani zubin takan yi magana ta hankali. “Wata ƙila daga yau ba za ki ƙara ɗaga yatsarki a fuskata ba...” Hajjara ta faɗa tana kallonta. Mishal ba ta fahimci abin da take nufi ba, sai da ta ga ta shiga waige-waige a cikin kitchen ɗin, sannan ta gane me take nufi. Kuma ba ta ƙara tabbatar da abin da kanta ke gaya mata ba, sai da ta ga Hajjaran ta rarumo wuƙa. Abubakar na zaune a falo yanawa Daala wasa, sai ji ya yi an ƙwalla wata razannaniyar ƙara, wadda yake jin tana fitowa daga kitchen. Tsabar tsoratar da ya yi, ya kasa gane ƙarar waye. Ba shiri ya miƙe, ya nufi kitchen ɗin gadan-gadan. Ba ƙaramin tashi hankalinsa ya yi ba, a sanda ya yi arba da abinda ke aukuwa a kitchen ɗin. Mishal ce zaune a kan marbles, hannaunta na dama riƙe da na hagu. Yayin da tsintsiyar hannunta na hagun ke zubar da jini, sai kuka take tana hawaye. Dubansa ya kai kan Hajjara dake tsaye a kanta, hannunta riƙe da wuƙa. A tsorace Hajjara ta kalli Mishal sannan ta kalleshi, sai kuma ta cillar da wuƙar, idanta ya cika da ƙwalla, ta ci gaba da kallon Abubakar tana girgiza masa kai, alamun a'a. “Innallilahi wa inna ilaihi raji'un, Hajjara, kashemin ƙanwa kike san yi?” Abubakar ya tambaya a kiɗime, yayin da ya ƙarasa gaban Mishal yana duba hannun nata. Hajjara ta shiga girgiza masa kai, tana san ganar da shi gaskiyar abin da ya faru. Ita fa ba ta yi komai ba, ba ta san ya aka yi komai ya auku ba. Cikin muryar kuka ta shiga faɗin. “Abubakar Wallahi... Walahi ban mata kom...” “Ki min shiru!, Kada ki sake min magana. Na ɗauka tsanarta kawai kika yi, ahse har kasheta ma za ki iya yi!” Abubakar ya katseta a zafafe, bayan da ya ɗago daga duba Mushal ɗin da yake. Ya ƙara tsugannawa kan Mushal da ke ta kuka kamar zata fasa gidan. Yasan ƙanwarsa da dauriya, ba komai takewa kuka ba tun tana ƙarama, tana iya jure komai duk zafinsa, dan haka tun da take kuka, dole ciwon nata ba ƙarami ba ne.

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112