Chapter 66
Chapter 66
nasu suka yi ɗaki. Kamar da Annan take jira, ta samu guri ta zauna tana musu kallon tuhuma, ganin yadda ko waccensu ta kafa inda-inda ne ya tabbatar mata da gaskiyar abun da suka aikata, duk kuwa da ta san Kuliya ba zai mata ƙarya ba. “Yanzu ke Karima a matsayinki na babba, ya kamata a ce kin aikata abun da kika aikata?, Ko za'a kira abun da Siyama ta yi a matsayin yarinta naki ba za a ce yarinta ba ce, saboda kin fita shekaru da sanin ya kamata. Amma saboda ke babbar kwabo ce, kika wanki ƙafa kuka je gidan matar mutane kuka rufa mata duka ko?!” Da sauri Siyama ta girgiza kanta, hawaye na ciko mata ido, musamman da ta tuna abun da ya faru a wacan ranar. “Anna Wallahi. Wallahi ba mu...” “Ƙarya kuke!, Idan ba ku ne kuka daketa ba za ta buga kanta da kanta a jikin bango ne, ta zo tace ku ne kuka mata dan kawai ta muku ƙazafi?” Da sauri Karima ta gyaɗa kai. “Wallahi Anna ba mu daketa ba, hasalima ita ce ta dake mu, duba ki gani...” Ta ƙarashe tana nunnuna mata tabon raunikan jikinta. Anna ta yi dariya, irin kun rena min hankalin nan. “Karima ko ƙur'ani za ki dafa kan wannan maganar taki ba zan yarda ba, jibe ki fa, yadda kike rusheshiyar nan da ke sai na yarda waccan 'yar fingilar yarinyar ita tai miki wannan raunin?, saboda ga Annan mahaukata ko?, to ni ba ma wannan ne ya kawo ni ba, zuwa na yi na ja muku kunne, babu ku babu gidan Aliyu, sannan babu ruwanku da sabgar matarsa, idan kuma ba ku ji ba ku je ku yi, Wallahi ni da kai na zan sa Aliyun ya hukunta ko waccenku, har ke Karima, tun da ba wani fikon arziƙi kika masa ba, in kun ce bakwa ji sai ku gwada mu gani!” Tana ƙarashewa ta miƙe ta fita, don da ma abin da ya kawota kenan, Siyama ta zube a kan kejera tana fashewa da kuka. “Kin ga inda kika kai mu ko Anti, yanzu ga shi bayan dukan da muka sha Anna ma ta ƙara mana da nata kashedin” Karima ta matse ƙwalla, tunawa da irin dukan da suka sha da ta yi. “Da ma ni sam soyyayar Kuliya ba ta karɓeni ba, ban da wahala babu abun da nake sha” Ta ƙarshe tana miƙewa, tare da nufar ɗakinta da gudu. Karima ta yi tagumi tana jinjina sharri da kissa irin na wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar da suka rena, ko dan ai an ce ɗan hakin da ka rena. ____________________ _Gani nan na yi tagumi hannu bibbiyu_ _jama'a!, wai ina Rabi ta shige ne?, wani ya temaka ya nemo mana ita_ _Ku ni fa na kasa gano abun da ya faru tsakanin su Karima da kuma Mishal_ _Salmanians, shin kuna kusa?_ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••••••••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *16* ~~~ *Don't be afraid of falling apart. Some of the must beautiful heart are built from tragedy.* *** Follow my Wattpad account 👇 https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends ~~~ *Bayan sati uku...* *No.181, Guzape, Abuja...* *09:30pm* MISHAL POV. Kwance take a falo, ta duƙunƙuna cikin blanket, idanuwanta sun yi ja saboda kukan da ta ci, ta kunna tv ta tsura mata ido amma ba kallon take ba. Damuwa da ruɗani ne suka saka rayuwarta a gaba, yau kusan sati uku kenan, amma Antinta Adawiyya ba ta zuwa makaranta, tun ta na ganin abun kamar fashi ne, har fashin nata ya zo ya soma bata tsoro, dan zuwa yanzu ma an kawo wata sabuwar me yim shara a makarantar, kullum sai ta yi kukan rashin sanin halin da Adawiyyan ke ciki, ga kuma kaɗaici da yake damunta a yanzu, ga shi dai ba wani jimawa suka yi da Adawiyyan ba, amma haka kawai take jinta cikin kaɗaici, yanzu haka ta hana idonta bacci ne dan jiran dawowar Kuliya, tun da shi ɗan sanda ne wata ƙila zai iya yin wani abu akan case ɗin yayar tata. Ta na kwance a wurin har goma ta wuce, kuma sai a lokacin Kuliya ya shigo gidan rai a ɓace, wanda ya samo asali daga wurin aikinsa, Mishal na jin shigowarsa ta miƙe da sauri ta sha gabansa, kallonta ya yi na 'yan wasu sakkani, sannan ya shiga ƙoƙarin raɓata ya wuce, amma sai ta ƙara tare masa hanya. “Abu Aswad.Yayata ce ba ta zuwa makaranta. Kuma ban san meke faruwa da ita ba, dan Allah ke nemo min ita” ta faɗi hawaye na mata zuba. “Ke me ya sa baki san abinda ya kamata ba?, Yanzu na dawo gida da ɓacin rai, me makon ki bari na huce shi ne za ki tarbeni da wannan maganar?!” Kamar de wancan karon haka ya mata magana cikin hargagi, Mishal ta fashe da kuka sannan ta naushi ƙirjinsa. “I hate you Abu Aswad!” Ta na kaiwa nan ta juya da gudu ta faɗa ɗakinta. “Zan iya shigowa?” Kuliya ya tamabaya ya na turo ƙofar ɗakin Mishal, wadda ke zaune a kan gado ta na kuka, sai bayan da ya je ya yi wanka sannan ya samu sauƙowa, shi ne ya taso ƙafa da ƙafa don ya nemi yafiya. Saboda ya san ba laifinta ba ne, shi kansa yabna bincike a kan yarinyar me suna Rabi'a, amma har yanzu babu abun da ya samu. Ya je makarantar Brickhall yafi sau biyar a cikin sati ukun, amma sam sun ƙi su ba shi adireshin Rabin, ga kuma wani renin hankali da suke masa na cewar ai jiya ma ya zo, bayan shi kuma ya san bai zo a ranar ba. Zama ya yi a bakin gadon ta setinta, ya na kallon gefen fuskarta da ta kawar, fuskarta ta yi jajir, alamun dai ba ƙaramin kuka ta sha ba, shi ya rasa wannan wata iriyar ƙauna ce tsakaninta da wannan yarinyar. “Hafsat” Ya kira sunata a tausashe, sai ta ƙara haɗe rai ta na kumbura baki. “Ki yi haƙuri ba zan sake ba!” Juyowa ta yi suka haɗa ido, ta wurgar masa harara, ta ƙara kawar da kan nata, sai ta bashi dariya, hakan ya sa ya murmusa a ransa. “Yanzu ba za ki yafemin ba?” Ta kuma juyowa ta kalleshi. Jin yanda ya yi maganar kamar maraya. “I hate you, ka fita min daga ɗaki” “In dai yayarki ce zan nemo miki ita, yanzu ma na zo dan ki bani wasu bayanai a kanta ne, ta yanda zan yi saurin samo miki ita!...” Kallonsa take tana son tabbatar da kalamansa, can kuma sai ta matso kusa da shi. “Ka yi alƙawarin za ka nemomin ita?” Sai ya gyaɗa mata kai ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, shi kansa bai san haka yake da laushi ba sai a kan Mishal, ita ce zai ɗagawa murya daga baya kuma ya zo ya na bata haƙuri. “Ni dai ki yafemin!” Ya faɗi murya ƙasa-ƙasa, kuma amon muryar tasa ya sa Mishal ɗin lumshe ido sannan ta buɗe. “To ba na ce maka ba na san tsawaba.Amma kullum idan ka fusata sai ka min...” “Daga yau ba zan sake ba, na miki alƙawari” Ya katseta tun kafin ta rufe bakinta, sai ta yi murmushi tana share hawayenta. “Ina
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112