Skip to content

Chapter 50

Chapter 50

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ƙofar yana kallonta, sanye take cikin wata blue and white boxed tie crop top da farar three layers ruffle skir. Duk da a zaune take, yana iya ganin alamar skirt ɗin ba ta sauƙa har kan idon sawunta ba, kamar dai sauran kayan da ta saba sakawa, don duk kayan da yake ganinta da su ba sa kaiwa ƙasa. Gashin kanta naɗe cikin french twist, daga saman gashin ta saƙala farin hair band. Kai kace wata Disney princess ce, kallonsa take kamar yanda shi ma yake kallonta, daurewa ya yi yace. “Ki shirya ki fito za mu je wani wuri” Zai iya cewa ya ga wacewar wani abu me kama da farin ciki a cikin idanunta, kafin ta miƙe da sauri, ƙafarta da bakinta har rawa suke wurin faɗin. “Fita zamu yi?” Ya kalleta na wasu 'yan sakkani. Jin ya mata shiru yasa ta kuma faɗin. “Ai a shirye nake, mu je kawai” Ta faɗi tana ƙoƙarin raɓa shi ta wuce, a karo na farko ya riƙo tsintiyar hannunta, ya na dawowa da ita baya, ba shi kaɗai ba, hatta da ita sai da ta ji kamar hysterianta na neman ta shi, sai kuma ya saki hannun nata da sauri yana kawar da kansa. Ita kuma sai ta kalli hannunta, yati6n da take kokawa da numfashinta da ya ƙi dai-daituwa, da ƙyar ta iya ɗagowa da kansa ya na ɗaga kafaɗarsa. “Be kamata ki fita a haka ba, saboda yanzu ke matar aure ce!” Ya faɗi ba tare da ya kalli fuskarta ba. Mishal ta sunkuyar da kanta ƙasa, yayin da abun da ya faru da ita waccan ranar ya shiga yawo a kanta, ba ta son tuna me ya furu a waccan ranar, amma daga zarar wani abu makamancin wanda ya faru a waccan ranar ya sake faruwa da ita sai ta tuna, yanda Yazid ya finciki hannunta da ƙarfi a waccan ranar haka shi ma ya yi a yanzu, tuna sunansa kaɗai yasa numfashinta fara ciccikowa. Da sauri ta kai hannunta kan wuyanta tana riƙewa, yayin da iskar ɗakin ta mata kaɗan wurin shaƙa, babu shiri ta shiga jan numfashi da sauri, hakan ya ankarar da Kuliya halin da take ciki. Kallonta ya yi da sauri, a lokacin da ta kai ƙasa, tana kokawa da numfashin nata, idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, yayin da hawaye ya shiga fita ta gefen idonta.Ji take kamar za'a zare mata numfashinta gaba ɗaya. A ruɗe Kuliya ya zube a gabanta yana kiran sunanta. “Hafsat!, Ke Hafsat!, Hafsat!” Inaa, ko ganinsa ma ba ta iya yi, bare har ta saurari abun da yake faɗi, ba shiri ya kai hannun ya riƙe fuskarta, yana goge mata gumin da ya shiga tsatsafo mata, har zuwa lokacin ba ta iya numfashi, can kuma sai komai ya tsaya cak, shure-shuren da take, da kokawar da take da numfashinta, da ma hawayen da take duka suka ɗauke, jikinta ya saki, kamar wadda ta mutu. Ba shiri Kuliya ya miƙe daga kanta, hankalinsa a mugun tashe, shi tun da yake be taɓa ganin abu makamancin haka ba, bai ma san me yasa meta ba, to ko aljanu gareta?... Tunaninsa ya katse a sanda idonsa ya sauƙa kan wata robar ruwa dake ɗakin, ba shiri ya miƙe da sauri ya nufi robar, ya ɗako ya dawo kanta ya na buɗe robar, tuninsa ne ya bashi cewar wata ƙila suma ta yi. Don haka ya shiga yayyafa mata ruwan a kan fuskarta da ta yi jajir, amma shiru, haka ya miƙe ya nufi work table ɗin da ɗazu ta taso daga kansa, ya ɗauko littafi ɗaya sannan ya dawo kusa da ita, fiffita ya shiga mata yana kiran sunanta. Kamar wadda aka tsikara da allura, lokaci guda numfashinta ya dawo, ba shiri ta miƙe zaune tana wani irin tari, har lokacin Kuliya be fasa mata firfita yana jero mata sannu ba. Sai da ya ga ta dawo hayyacinta ne ya dubeta da kyau, ya ga yanda take ta sauƙe ajiyar zuciya, be san lokacin da ya ja ta jikinsa ya rungumeta daga zaune da suke ba. Idanuwan Mishal ne suka ƙara girma, a lokacin da ta fuskanci cewar ita ce a tsakiyar hannayen Kuliya, ita ce a kusa da shi, kusan da har suna iya jiyo bugun zuciyar juna, babu abun da ya ba ta mamaki sai yanda ta ji zuciyarsa na aiki da sauri, mamaki ne ya kamata na me ya tsorata shi har haka. Yanda ya ƙara matseta a cikin jikinsa ne ya sa ba shiri jikinta ya shiga kyarma, tun da ta zo duniya ba za ta iya tuna lokaci guda da ta shiga yanayi irin wannan ba, tabbas tana rungumar 'yan uwanta, amma wannan rungumar ba irin waccan ba ce, wannan ta sa ban ce, kamar akwai wani abu na musamman tattare da kusancin nasu, sai ta ji ba ta son ya saketa, kamar su ci gaba da tsayawa a hakan, saboda ta ji rungumetan da ya yi kamar ya na son kangeta daga wani abu mara kyau dake shririn faruwa da ita ne. “Daga magana sai ki suma?!, me ya yi zafi haka Hafsat?!” Muryarsa ta faɗi bayan wani lokaci, kuma amon muryar tasa ne yasa Mishal ta ƙara matse jikinta cikin nasa, muryar kamar ba tasa ba, kamar ba Kuliya ne ya yi maganar ba, da ma ya iya magana a tausashe kamar haka?, To ai gwara da ba ya yin magana a tausashen, don wata ƙila da ace yana yi, da duniyar ce gaba ɗayanta za ta yi haske cikin duhun daren. A hankali ya saketa yana kallon fuskarta, a karo na farko Mishal ta ji ba ta san haɗa ido da shi, hakan ya sa ta sunkuyar da kanta ƙasa. Kamar wanda aka jefowa tunaninsa daga sama haka Kuliya ya dawo hayyacinsa, sai yanzu ya gano abun da ya yi, ba shiri ya miƙe tsaye yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, kansa ya kawar gefe, zuciyarsa na ƙara saurin gudun da take a ƙirjinsa, don sai yanzu ma ya ji wani irin shock a jikinsa na riƙetan da ya yi. Da ƙyar ya lalubo muryarsa cikin faɗin. “Ki... Ki kwanta ki yi bacci kawai, sai da safe!...” Ya faɗi ya na shirin juyawa, amma sai muryar Mishal dake ƙoƙarin miƙewa ta dakatar da shi. “No... na ji sauƙi za mu iya tafiya” Juyowa ya yi ya na kallonta, amma ita kuma ta ƙi yarda su haɗa ido. Shi ya masa gane mata, yanzu fa ta suma?, kuma sai ta ce su fita?. “No, kina buƙatar hutu, don haka ki kwanta kawai...” Cewar Kiliyan yana ƙoƙarin juyawa a karo na biyu, amma sai muryar Mishal ɗin ta ƙara katse shi. “Da gaske nake na ji sauƙi, babu wani babbar matsala, na riga da na saba da wannan ciwon, so it's common” Juyowa ya kuma yi ya na kallon fuskarta dake kallon ƙasa, kamar me shirin san tantance gaskiyar abun da ta faɗi. * Da gudu motar Kuliya ke tafiya a kan titi, yayin da Mishal ke zaune a gefensa, kayan da suke jikinta ɗazu su ne a yanzu ma, sai dai wani baƙin gyale da ta ɗora a kanta, hanya kawai take kallo tana tuna abun da ya faru ɗazu, yanda Kuliya ya matseta

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112