Skip to content

Chapter 79

Chapter 79

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

dan ta san ko ta ƙwanƙwasa ba lalle ya amsa mata ba, yaya lafiyar kura, balle ta yi zawo, tsaye ta ganshi jikin mirror, ya na taje sumar kansa. Ta ci kin mirror kawai ya kalleta, sanye take da wata farar off shoulder shirt, sai wani baƙin short culottes, wanda bai ƙarasa kan guwarta ba, ya ɗauke kansa ya na ci gaba da taje sumar kansa. Mishal ba ta damu ba, dan idan da sabo ta saba da wannan abun nasa , babu me iya zama da Kuliya sai me haƙuri, tsayawa ta yi a gefensa tana kallonsa, amma bai ko kalleta ba, sai ta rakaɓa ta gefensa ta shiga gabansa ta tsaya, wata gajeriyar harara ya maka mata, sannan ya kauce ya na ci gaba da tazar, Mishal ta ƙara matsawa ta tsaya a gabansa, sannan ta saka hannayenta ta karɓi matajin hannunsa, ta yi tattage dan ta ƙara tsayi, sannan ta shiga taje masa sumar. Memakon ya tanka mata, sai ya mata banza ya juya ya barta tsaye da matajin a hannu, Mishal ta girgiza kanta ta na mitar halin wanga bawan Allah, sannan ta aje matajin a kan mirror, ta biyo bayansa. Zama ya yi a bakin gado ya na kawar da kai. Mishal ta yi murmushi ta na tsayawa a gabansa, hannunta ta sa ta kamo haɓarsa ta juyo da fuskarsa gareta. “Me nene?” Fuskarsa ya ƙwace sannan ƙara juyar mata da kai, sunkuyawa ta yi ta kai hannunta kan buttons ɗin gaban rigarsa ta buɗe guda huɗu, duk bai kulata ba, sannan ta hau kan gadon ta zagaya ta bayansa, ta tsaya a kan gwiwoyinta, tare da saka hannayenta a kan kafaɗunsa, ta fara masa tausa. “Me nene ?” Muryarta ta tambaya bayan wani lokaci, memakon ya amsa mata, sai ya saka hannunsa na dama ya kamo nata, tare da ƙoƙarin janyota zuwa gabansa, hakan ya sa ta miƙe ta sauƙa daga kan gadon ta tsaya a gaban nasa, sai kuma ya kamo hannunta ya zaunar da ita a kan cinyarsa ta dama. Ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na sofara gashin da ya sauƙo mata kan fuskarta a bayan kunnenta, a lokaci guda yana kallon fuskarta. Mishal ta lumshe idonta ta buɗe, sannan a hankali hannayenta suka kewaya bayansa, kafin ta saka kanta a cikin wuyansa. “Me ya faru ?” Muryarta ta fito a kan fatar wuyansa, yanayin ya sa Kuliya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya saka hannayensa ya ƙara rungumeta a jikinsa. “Game da binciken yayarki ne...” Sai kuma ya yi shiru. Mishal ta sumbaci wuyansa ta na ƙara matse hannunta a bayansa. “Ummhum?” Muryar tata ta kuma faɗi a wuyansa. “Me gadin makarantar ku ne yake san ɓatamin rai, yau da na je, babu yanda ban yi da shi ba kan ya ba ni wasu bayanai, amma yace wai sai na nemo izini daga sama, shi ne na...” Jin ya yi shiru ya sa Mishal ɗan ɗagowa daga jikinsa ta kalli fuskarsa. “Ka mare shi, right?” Sai shi ma ya sunkuyar da kansa ya na kallonta. “Rai na ne ya ɓaci” “Na fahimta, amma ba haka ake ba, kamata ya yi ace ka tafi da yaranka, sai ku je a matsayin jami'ai, waɗanda suka je bincike, ko principal ba zai baku matsala ba” Kuliya ya rage girman idonsa ya na kallonta, me ya sa ahi be yi tunanin hakan ba?, ya sumbaci goshinta ya na ƙara janta jikinsa. “I love you Teddy Bear...” Mishal ta yi murmushi. “I hate you Abu Aswad..... Na gama abinci, mu je ka ci” Ya gyaɗa mata kai ya na ɗagata daga jikinsa. RABI'A POV. Da sanyin safiya ta farka a gidan Kawu Habu, duk da jiya da daddare bata kwanta da wuri ba, kasancewar ramakon sallollinta da ta ci gaba da yi, sai da ta yi ƙoƙarin taya Mama Laure aikin gidan, amma tace ta hutar da ita ta kwanta ta yi ramakon baccinta. Kuma ba ta musa ba, sai ta kwanta ɗin, don ba ƙaramin bacci take ji ba, wajajen ƙarfe bakwai 'yar Mama Laure ta farko ta tasheta dan ta tashi su ci abinci, abincin suka ci, sannan ta sha magungunanta da ta taho da su. Ba daɗewa kuma ta ƙara komawa baccin. Sama-sama ta soma jin hayaniya a tsakar gidan, da farko ma kamar a mafarki take jin hayaniyar, jin hayaniyar ta ci gaba ne ya sa ta buɗe idonta. Muryar Abbansu ta ji a tsakar gidan, hakan ya sa ba shiri ta miƙe zaune, mayafinta ta raruma ta yafa a kanta, sannan ta fita tsakar gidan, don ganin meke wakana. A dai-dai lokacin da ta fita, a Ɗan Lami ya fice daga gidan, Mama Saratu da Mama Ramatu duk sun tsa-tsaya a tsakar gidan, ga kuma Kawu Habu daga gefe. A raunane ya kalleta, sannan yace. “Rabi sai de ki yi haƙuri, amma ba zan iya haƙura da ɗiban albarkar da Ɗan Lami ya zo ya min ba, dan haka kawai ki zo ki tafi!” Ta ɗauka cewar ita da tashin hankali sun yi hannun riga, ta ɗauka cewar rayuwarta za ta huta da masifun da suke samunta, ta ɗauka cewar tashin hankalin da ya ɗan yi nisa da rayuwarta ya tafi har abada, ashe yajin aiki ya yi, ashe be je ko ina ba, ashe kawai ya ɗan barta ta huta na kwana ɗaya ne, ina ake so ta sa kanta?, ta fita titi ta yi karuwanci?, a'a, wannan babban kuskure ne, ko kafin Umma ta rasu sai da ta gargaɗeta a kan hakan, to gwara dai ta kashe kanta, hakan zai fi sauƙi!... Waɗanan su ne ire-iren maganganun da take ta rayawa a ranta yayin da ta fito daga gidan Kawu Habu, babu yanda Mama Laure ba ta yi da ita ba kan kada ta fita, amma tace tun da me gidan ya koreta me za ta zauna ta yi?. Har ta hau kan titi ba ta cikin hayyacinta, ƙafafunta har harɗewa suke gurin tafiya, ta riga ta saddaƙar da gwara ta mutu, gwara ta bi Baby da Umma ko kowa zai huta, idan ta mutu duniyar za ta fi zama dai-dai, wata ƙila iyaka nan Allah ya hukunta ƙarewar labarinta. “...Wallahi daga Haɗejia nake!...” Kalaman suka biyo iska tare da silalowa suka rufta cikin kunnuwanta, nan take ƙwaƙwalwarta ta tuno mata da wani wuri ɗaya da zata iya zuwa dan ta huta, ƙwaƙwalwata ta hasko mata wani wuri ɗaya da ta saba samun farin ciki a duniya, gatanta, tushen mahaifiyarta, Haɗejia!. *Fall in love when you're ready, not when you're lonely...* *** *Brickhall School, Kaura District, Abuja* KULIYA POV. Ya na tsaye daga bakin gate ɗin fita daga makarantar, kamar yanda Mishal ta bashi shawara kan ya je da yaransa sannan ya je a matsayinsa na ɗan sanda, hakan ya yi, kuma ya yi nasarar samun damar yi wa duka ma'aikatan makarantar tambayoyi. Da yake lokacin tashi ne, gaba ɗaya ɗalibai sun firfito, 'yan day na ya ƙoƙarin tafiya gida, idan ya ɗan tsaya ya saurari bayanan megadin, sai ya ɗan juya ya ɗan yi kalle-kalle ko zai ganta. Kuma cikin wani ikon Allah a wannan karon sai ya gantan, sannan cikin kyakkyawan gani, dan tana tsaye da wani yaro wanda ke sanye da uniform, yaron na mata

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112