Chapter 70
Chapter 70
kawai yake... Yake sona... Ka san... Ka san me ya min yau da safe?” Ta tambaya tana share hawayen fuskarta, kansa ya girgiza mata ya na murmushi. “A nan” Ta nuna masa lips ɗinta. “Annan ya sumbace ne, kamar haka; ummmuah!” Ta ƙarashe tana furta masa sautin sumbatar da bakinta. Sai kuma ta fashe da dariya. “Wai jiya cewa ya yi ya ba ni zuwa yau da... Yau da safe na... Na yanke shawara a kan soyayyarsa...” Sai kuma ta ƙara fashewa da wata dariyar. “Shashasha bai san cewa tun ba yau nake san sa ba....” Ta kuma saka wata dariyar, sai kuma ta jingina da jikin kujera, a hankali idonta ya shiga lumshewa, bakinta na motsawa, ta na faɗar wasu kalamai da shi bai ma san ma'anarsu ba. Ganin kamar shirmen nata ya ƙare ne ya sa shi miƙewa ya ɗauketa duka, sannan ya yi ɗakinta da ita, a kan gadonta ya kwantar da ita, sannan ya lulluɓeta ya fita. Ɗakinsa ya koma ya yi wanka, ya sauya kayansa zuwa wanda ya saba sakawa na zaman gida a irin wannan lokacin, wato baƙin sweat trouser da kuma baƙar T-shirt. Kitchen ya fara dubawa ko zai samu abinci, ya tarar da ta aje masa wanda zai iya ci, za ma ya yi ya na ci ya na murmushi a kai a kai, don shirmen nata ba ƙaramin nishaɗi ya bashi ba. Bayan ya kammala cin abincin ya ɗan taɓa aiki a system ɗinsa, kafin ya fara jin bacci, system ɗin ya rufe, sannan ya nufi ɗakinsa dan ya kwanta, sai wata zuciyar ta raya masa da me zai hana ya je ya kwanta a ɗakinta, wata ƙila ta buƙace shi ko da cikin dare ne. Ba tare da wani tunani ba ya nufi ɗakin nata, sai ya tarar da ta hargitsa kwanciyar da ya mata ɗazu, ba kamar. Murmushi ya yi ya na gyara mata kwanciya, sannan ya kwanta a gefenta ya na kashe musu wuta. Janta ya yi jikinsa, sannan ya lumshe idonsa don yin bacci, ba jimawa kuwa baccin ya ɗauke shi, don a gajiye yake, amma kuma baccin nasa bai yi minti goma ba ya farka, saboda wani duka da Mishal ta masa da ƙafarta, sam ya manta da ba ta iya kwanciya ba. Ƙafafuwan nata ya gyara mata, amma da aka jima sai ta ƙara lafta masa ƙafarta, tun ta na yi ya na gyara mata, har ya gaji ya rabu da ita, haka daren ya ƙare ta na ta bugunsa da ƙafarta. Da asuba ya farka, hakan ya sa ya tashi ya koma ɗakinsa, ya ɗan watsa ruwa kaɗan, sannan ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci, har ya dawo ba ta farka ba, hakan ya sa ya mata tashin duniyar nan amma ko motsi ba ta yi ba, har ruwa ya watsa mata amma kamar an mintsin kakkausa, sai ya ƙyaleta ya koma ya kwanta a gefenta. Wajejen ƙarfe 09:00 dai-dai wayarsa ta yi ringing. Cikin bacci ya ji ƙarar, hakan ya sa ya buɗe idonsa, hannunsa ya kai ya ɗauki wayar, sunan 'Sharon' ya ga ya na yawo a kan screen ɗin, sai ya ɗaga ya na wani cin magani kamar ta na gabansa. “Lafiya yau ka makara?” Sharon ta tambaya bayan sun gaisa, sai da ya juya ya kalli Mishal dake baccinta tsakani da Allah, hankalinta kwance, kamar tsumma a randa, sannan yace. “Hafsat ce ba ta jin daɗi, zan kaita asibiti” Sharon ta ƙunshe dariyarta sannan ta ce. “Allah ya ba ta lafiya, sai yaushe kenan?” “Gobe” Ya bata amsa a taƙaice. “Sai goben” Ya na gama sauraren hakan ya katse kiran sannan ya aje wayar a inda ya ɗauketa. * “Yau Sir ya na more amarci... Dan haka ba zai fito ba” Cewar Sharon ta na kallon su Symon, wanɗan da suka zo suka sakata a gaba kan ta kira Kiloya ta ji me ya sa yau bai zo ba. Dariya suka kwashe da ita, daga nan kuma sai aka shiga hira a kan Kuliya da Mishal. * Ya kamata ace zuwa yanzu ta tashi, Kuliya ya faɗi a ransa, ya na kaiwa hannunsa tare da ɗan tattaɓa fuskarta. “Ummmm!” Ta faɗi cikin muryar bacci. “Hafsat” Ya kira sunan a hankali ya na kallonta, yayin da yake kwance a gefenta. “Ummmmmm!” “Ki tashi gari ya waye” Idonta ta buɗe a kansa, sannan ta ƙara lumshewa, ta kuma buɗewa, kuma a lokacin ne ta gano abun da ke faruwa, Kuliya ne kwance a gefenta, sannan a kan gadonta. Ba shiri ta tashi zaune ta na waige-waige, kamar me neman wani abun, ita dai tasan bayan ta yi sallar isha, ta zauna a falo ta ci abinci, sannan ta ɗora da magungunan da ya aiko mata a jiyan, maganin murar ma da yawa ta sha, wai duk don ya mata magani da wuri, saboda ita ba ta san murar nan, kasancewar idan ta na yi takura mata take yi. Kuma bayan hakan ita ba ta tuna komai ba. Kuliya ya miƙe zaune ya na kallonta, abun da ta yi jiya ya dawo masa sabo, hakan ya sa shi murmusawa a fili. “Kin tashi lafiya?” Kallonsa Mishl ta yi a firgice, ta na san ta tuna wani abu da ta yi a daren jiya, amma ta kasa, ta kasa tuna komai, dole akwai wani abu da yake ba dai-dai ba. “Har rana ta take ba ki yi sallah ba, ki je ki yi sallah” A hautsine Mishal ta sauƙa daga kan gadon ta faɗa banɗaki da gudu, Kuliya ya yi murmushi ya na sauƙa daga kan gadon ya fita daga ɗakin. #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *18* ~~~ *It's not hard to make someone feel loved.* *** *No.181, Guzape, Abuja* MISHAL POV. A gurguje take aikin haɗa breakfast, don tasan yau ba ƙaramar makara ta yi ba, saboda ta na da tabbacin ma ko makaranta ba zuwa za ta yi ba, sai dai kuma akwai abun da ke ɗaure mata kai, me Kuliya yake ɗazu a shimfiɗarta, kuma ita da ta kwanta a falo me ya kaita ɗaki?, sannan shi ma me ya sa bai fita aiki ba yau?, abubuwan sun ɗaure mata kai. Ga kuma kan nata dake mata ɗan banzan ciwo, sai jikinta da take ji a mace, haka ta yi sauri ta gama haɗa sandwich da kuma jallof ɗin indomie, tare da hot chocolate. Ta kwashe komai ta jera a kan danning, sannan ta koma kitchen ɗin ta shiga wanke kayan da ta ɓata. Har ta gama ba ta ga Kuliya ya fito ba, sai ta shiga gyara gidan, kuma gyaran gidan ma har ta kammala bai fito ba, abun ya so ba ta mamaki, ta san ko a da da ba ta girki da shi ya na fitowa da wuri ya ci abinci, kuma ta hakan ne ta gane cewa ba shi da jimirin yunwa, amma ga shi yau bai fito ba, to ko de tunani yake ba ta yi girki ba?. Da wannan tunani ta nufi ƙofar ɗakinsa, sau ɗaya ta ƙwanƙwasa, ta ji muryarsa ta yi gyaran murya a cikin ɗakin, tunaninta ya ba ta cewar wata ƙila wani uzurin yake yi da ba ya so ta shiga ta gani a lokacin, sai ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112