Skip to content

Chapter 27

Chapter 27

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,194 words 0 views Progress saved
Download Book

ta gansu tare a waccan ranar, kuma ita ma kayan jikinta irin nasa ne, ba don ta ga wannan ɗan uwan nasa na jikin hoton na miji ba ne, da za ta ce wannan macen ita ce 'yar biyun tasa. Ba wai dan suna kama ba, sai dan kayan da suke sakawa iri ɗaya. Last time ma da ta gansu kaya iri ɗaya ne a jikinsu, to gashi yau ma haka. Wani abu da ta lura da shi shi ne, shi ma ɗin kallonta yake, kamar yanda ita ma take kallonsa. Turewa komai ta yi daga cikin kanta, ta soma tunkararsu, don ta samu ta bashi wallet ɗinsa da ya jefar jiya. Don da ma da ita ta taho, tana ta addu'ar Allah yasa suƙara haɗuwa. Sai ta kasa magana a sanda ta ƙarasa inda suken, daga shi har wannan budurwar me kaya irin nasa sai kallonta suke, tsoro ya kamata, ta rasa abun cewa, sai ta shiga wasa da ƙarshen hijabinta ta ciki. Raja ya ci gaba da kallonta, a sanda yake ƙara tabbatarwa da kansa wani abu, ko yaya aka yi, tabbas ya haɗa jini da wannan baiwar Allahn, abun ya wuce kama kawai, saboda ya lura da wata tawada a gefen fuskarta, wadda Mommansu ma tana da irinta. Abun na ɗaure masa kai, shin dabma akwai sauran 'yan uwan Mommansu a duniya ?, amma me yasa basu neme su ba?, ko da yake ai Momman tace masa babanta ne ya koreta daga gidansa. Sai kawai ya ture komai, ya tsai da tunani ɗaya, ƙaddarar da ta haɗashi da wannan yarinyar, wata ƙila ita za ta sada shi da 'yan uwan Mommansu. “Sannunki!” Rhoda ta katse shirun da wurin ya ɗauka, kusan shuɗewar muntuna kenan, amma Raja da yarinyar babu wanda ya yi magana, shi ya sa ita ta ari bakinsu ta ci musu albasa. Rabi'a ta ɗago ta kalleta, sannan bakinta na rawa ta ce. “Sannu” “Me kike nema ?” Rhoda ta tambaya. Kuma kafin yarinyar ta amsa, Raja ya jiya ya kalli Rhodan, ko bai faɗa ba tasan me yake nufi, dan haka sai ta yi shiru, sannan ta juya ta koma cikin estate ɗin. Ganin yanda yarinyar ta ke ta kame-kame ne yasa shi yi wa Rhodan alama da ta bar wurin, dan bisa ga dukkan alamu, ido ne ya mata yawa. Ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya sannan wannan salihar murya tasa, me sawa mutum ya yarda da shi a tashin farko tace. “Ya hannunki?” Rabi ta kalli hannun sannan ta amsa da. “Ya yi sauƙi” “Ya ya sunanki?” Sunanta ?, to me zai yi da sunanta ?, ko de shi ya santa, ita ce ba ta da masaniya game da shi ?, ta haɗiye wani abu sannan tace. “RABI'A!...” Wani abu me kama da Allura ya caki Raja a ƙahon zuciya, zuciyar tasa ta shiga rawa a ma'ajinta, wani abu me kama da rauni ya shiga bin jikinsa, an kuma. RABI'A?!, Cewa ta yi sunanta RABI'A!. Jin ya yi shiru ya sa Rabi ta ɗago da hannunta wanda ke riƙe da wallet ɗin, ta miƙa masa. “Ga shi, wallet ɗinka ce da ka cillar jiya” Her voice was innocent, babu wani abu a cikinsa sai nutsuwa da kamun kai. A hankali kammanninta suka shiga rikiɗewa a idonsa, daga Rabi'a yarinya zuwa shekarun Mommansa a sanda ta rasu. Sunansu ɗaya, kammanninsu ɗaya. Sai yake jin kamar Mommance ta dawo. Amma ba wannan ba, shi sam bai lura da babu wallet ɗin tare da shi ba, saboda bai nemeta ba, shi yasa bai kula ba. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, kafin ya kai hannunsa ya karɓi wallet ɗin. Buɗewa ya yi ya kalli kayan ciki, babu abun da aka ɗauka, komai yana ciki yanda yake, kuma harda kuɗaɗensa ba ta taɓa ba. “Aiki kike a nan?” Ya tambaya, a sanda yake zaro kuɗi daga cikin wallet ɗin, Rabi ta ɗan kalleshi kaɗan, wai shi me ke damunsa ne?, yanayinsa kamar me jin bacci, haka ma muryarsa kamar wanda ya yi wani aiki ya gaji. Sai kuma ta yi saurin kauda idonta, ta kalli sauran ɗaliban dake tafiya ta ce. “Eh...” “Na fahimta” Kuma ya fahimta ɗin, abun da tunaninsa ke gaya masa ne ya tabbata, aikatau take a wurin, bai sake cewa komai ba, ya miƙa mata duka kuɗin cikin wallet ɗin da ya fitar. “Sunana Raja... Ki yi kuɗin mota da wannan, sannan nagode da ajiyar da kika min, AMMATA” Abubuwa huɗu ne suka haɗu a maganar tasa, sunansa, kuɗin da ya bata, godiyar da ya mata, sannan kuma sunan da ya kirata da shi; AMMATA!. Ta kalli dumin kuɗin da yake bata, sannan ta kalli fuskarsa, wannan lumsassun idanuwan nasa ne a kanta. Dan haka sai ta girgiza masa kai. “Ni ma na gode, ka bar shi kai...” Maganar ta bi iska, sakamakon hannunta na dama da Rajan ya kamo, ya danƙa mata kuɗin... * Rabi'a ta shawo kwanar layinsu, dai-dai kwanar da masu kayan siyarwa kan taru. Tsayawa ta yi a kusa da wani mai kifi dake soyawa. A kullum idan ta zo wucewa ta wurin sai ta haɗiyi yawu, saboda, kwaɗayin kifin da ke ranta. Ita fa da abata kaza gwamma an bata kifi. Gabshi kuma gidansu ba kifin ake ci sosai ba, sun fi cin kaza akan kifin. Hakan ya sa ba sosai take samun damar cin kifin ba. Hannunta na hagu dake damƙe da kuɗaɗen da Raja ya bata ta ƙara damƙewa, hakan ya tuna mata da yanda suka kwashe da shi a ɗazu. A ɗazun bayan da ya kamo hannunta, sai ya saka mata kuɗaɗen, sannan ya ninke hannunta kan kuɗin. Yayin da ita kuma ta saki baki da hanci tana kallonsa, wani abu me kama da ruɗani na kai-komo a cikin kanta. “Idan na faɗi abu ba'a mun musu... Kin fahimta ?” Ta shiga gyaɗa masa kai, kuma ba ta bar gyaɗa kan nata ba sai da ya saki hannunta. Ita kuwa ta fahimta, ba ta jin akwai wani wanda zai kaita fahimtar yaren nasa. A kan idonta ya ɗaga mata hannu, sannan ya bar wurin, ya barta da raunanniyar zuciya. Ta haɗiye wani abu a fili, sannan ta juya zuwa wurin me kifin. Magana ta masa kan ya bata na dubu ɗaya, sannan ta miƙa masa dubu ɗayan. Me kifi ya saka mata soyyayar karfarsar a takarda, ya ninke ya danƙa mata. Ta kamo hanyar gida ranta fes. Tana kaiwa gidan ta faɗa ɗakinsu, sai da ta faki idon kowa, ta saka kifin a jakarta. Sannan ta fito tai alwalar sallar la'asar. Ta yi sallar, kafin ta fito ta shiga yin ayyukanta da ta saba a gidan. Ta yi wanka ta saka kaya baya-baya. Ta dawo ɗaki ta zauna, tana ta dube-dube. Anti saratu dake kwance a kan katifarta, ta lura da abinda take hakan ya sa tace. “Rabi lafiya ?” “Hmm, ina Mama ?” Anti saratu ta yi murmushi. “Ta tafi gantalinta, Fatima da Mahmud su na gidan kawu Abubakar. Umma kuma ina jin tana ɗakinta, faɗamin ta samu ne ?” Ta tambaya ta na tashi zaune... Ran Rabi ƙal, ta tashi daga kan carpet ɗin da take, ta dawo bakin katifar ta zauna. “Ina mutumin da na faɗa miki cewa ya temakeni jiya ?” Anti Saratu

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112