Chapter 75
Chapter 75
da ta yi kowanne a cikinsu ya na cire tufafin jikinsa, basu damu da ko kallonta ba, ballantana su saurari abun da take faɗi. kukanta ta ƙarawa ƙarfi ta na rintse idonta._ _“Wai me ya sa mutane ba su san Allah ba? An haɗasu da Allah amma sai ka ce da wani sheɗan aka haɗasu, me makon mutum ya bar abun da yake sai ma ya ƙarawa abun ƙaimi, dan Allah na roƙeku...”_ _Ta ci gaba da roƙonsu, a lokacin da Usee yace._ _“Kai duk ta bi ta cika mana kunne, dallah kusa ta yi shiru!”_ _Jaz ne ya ɗauko ƙarfen abun shisharsu me kauri, ba tare da Rabi ta ankara ba, saboda idanuwanta da suke a kulle, ta ji sauƙar yankan wani abu me kaifi a gefen fuskarta, hakan ya sa ta buɗe idonta da sauri, wani kalar raɗaɗin azaba ya ziyarci ƙwaƙwalwarta, nan take ta ƙwala wani uban salatin da sai da gidan ya amsa, gefen fuskar tata ya yanku ba kaɗan ba._ _“Kai dallah mahaukaci! Cewa na yi ka sata ta yi shiru ba wai ta ƙara volume ba!”_ Cewar Usee ya na rarumar wata vase, sannan ya ɗaga ta sama, ya bugawa Rabi a tsakiyar kanta. Nan take Rabi ta ji wani dimmm, kamar injinan da suke aiki a kanta sun dena, komai ya tsaya cak, babu wani abu dake aiki, kan kace me, jini ya wanke mata fuska. Babu shiri ta faɗi a ka gadon._ _Duk da idonta a lumshe yake, ta na jin sanda suke rabata da tufafin jikinta, hakan ya sa ta buɗe idonta a wahalce, sai dai hoton abun da take gani ya koma ja, saboda jinin da ya wanke mata fuska, ba sosai take cikin hayyacinta ba, amma ta na ji ta na gani haka suka shiga haike mata ɗaya bayan ɗaya._ _Duk da irin raɗaɗin azabar da take ji, ba ta da damar yin ihun neman agaji, ta na kwance ne a wurin kamar gawa, amma da ko wace azaba da suke mata jikinta ya na amsawa, ko wanne a cikinsu sai da ya haike mata sau biyu, tun tana buɗewa idonta fa lumshe har sai da komai na kanta ya ɗauke, ji da ganinta suka yi nisa, numfashinta ya yi sama._ _“Usee kamar yarinyar nan fa ta mutu”_ _Usman ya ɗan karkato da kansa kaɗan ya kalli kan gadon, inda Rabi ke kwance malale cikin jini, babu tufafi a jikinta. Sai ya zuƙi sigarinsa, ya furzar ya na faɗin._ _“Ku ɗauketa ku cillar da ita, idan abun sha ya ƙare, me za ayi da kwalba?”_ _Ba tare da ɓata lokaci ba suka cika umarninsa, a cikin blanket ɗin dake kan gadon suka nannaɗe, sannan suka ɗauketa suka saka a mota, suka fita daga gidan. Sun ɗan yi tafiya me tsayi daga gidan Usman ɗin, kafin suka samu gefen titi, suka faki ido, duk da dare ne ,babu kowa a layin, suka cillar da ita a wurin kafin suka ƙara mai._ (Ya Ilahi ya Allah!...). A hankali wata siririyar ƙwalla ta zubo daga idon Rabi wada ke kwance a kan gadon marasa lafiya, tana nan kwance kamar gawa, kuma idanuwanta a lumshe. Wata ƙwallar ce ta sake gangarowa daga idonta ta shiga kunnenta. Sannan a hankali bakinta ya buɗe, cikin wata dasasshiyar murya ta fara faɗin; “Da... Dan... Dan A... Allah, kad... Kada ku... Kada ku min... Ka... Kar ku... Cutar... Cutar da ni... Ni...” Haka bakinta ya ci gaba da faɗi, kafin kuma jikinta ya fara jijjiga, da alama duk abun da ya faru a waccan ranar take gani a cikin mafarkinta. Cikin abun da bai wuce daƙiƙa ɗaya ba, ta wangale idanuwanta tar, ta na maida numfashi kamar wadda ta yi wani aikin ƙarfi, idonta ta ƙara lumshewa, sannan ta buɗe su tar. Kafin ta miƙe zaune, ta na ta dube-dube, sai kallon ɗakin take, kafin dubanta ya dawo jikinta, tabbas ta na asibiti ne, to duk yanda aka yi ɓacin ran da Raja ya saka mata ne ya sa ta suma, shi ne aka samu wani bawan Allahn ya kawota asibiti, har ta yi mafarkin an mata fyaɗe. Wanna hasashen da zuciyarta ta yi ne ya sa ta sauƙe ajiyar zuciya, haka ne ma, haba!, da ma in ba haka ba ta ya za'a yi ace an mata fyaɗe?!. Hannunta ta kai ta ciccire na'urorin da aka saka mata a jikinta, sannan ta shiga ƙoƙarin sauƙo da ƙafacunta ƙasa, ta daddafa har ta samu ta iya sauƙa daga kan gadon. Sai de me?, miƙewar tata ke da wuya ta ji ƙasanta ya yi wata irin amsawa, ba wai amsawa ta zafi ba, a'a, ji ta yi kamar an saka wani abu an ɗaure wurin, duk da haka ba ta karaya ba, wannan hasashen da zuciyarta ta yi shi ne ya ba ta ƙwarin gwiwa da kuma na zuciya, haka ta tattaka cikin wani irin taku me kama da na 'yan koyon tafiya, ta nufi banɗaki. Daɗewar da ƙafafunta suka yi ba su yi tafiya ba ya sa suke amsawa idan ta na taku, ƙofar bayin ta tura, sannan ta shiga, kai tsaye jikin mirror ta isa, kuma abun da ta gani shi ne ya rikirkito da duniyarta ƙasa. Wata tsawa da walƙiya suka haska a cikin kanta, wani irin tashin hankali da ba ta san akwai irinsa a duniya ba ya ziyarceta. Wannan yankan da aka mata a gefen fuska, ya na nan, har da ɗinki an yi wa wurin, dan har ya warke an cire zaren. Sannan ga gashin kanta da aka yanke mata, gashinta da a da yake sauƙowa har gadon bayanta, shi ne yanzu yake iyaka kafaɗunta, ga kuma tabon dukan da aka mata a kanta. Sannan wannan raunin fuskar tata shi ne ya ɗan sauya kammanin fuskarta, duk da ba du ba, amma yanayin fuskar tata ya sauya. Waɗanan alamomin su ne suka ƙaryata hasahsen zuciyarta, waɗanan alamomin su ne suka murmushe fatanta har garinsa, wanan alamomi su ne suka tabbatar mata da duk abin da ya faru a waccan ranar ba mafarki ba ne, gaskiya ne, da gaske ne cewar waɗanan mugayen samarin guda biyar, sun haike mata, da gaske ne cewar yanzu ita ba ta da wata martaba kamar ta sauran mata, kuma da gaske ne cewar ita yanzu ba budurwa ba ce, yanzu ita ba ta da wata kima da daraja wadda jama'a za su kalleta da ita, ba ta da wani abu da za ta nunawa mijin da za ta aura. A lokacin da ƙwaƙwalwarta ta kai ƙarshe wurin zayyano mata waɗanan kalaman, a dai-dai lokacin ne ta ɗago da hannunta ta shafa fuskarta, ta taɓa kanta. Nan take ta ji wani kukan ɓacin rai da na tashin hankali sun haɗe wuri guda sun tsaga haƙwaranta, sun raba laɓanta, sun fito cikin 'yancinsu. Wani kalar kuka take me sauti, jikinta har rawa yake. “Me ya sa ni ba ni da ƙaddara me kyau?!, me ya sa komai nawa yake rugujewa?! Me ya sa ni ba zan yi farin ciki kamar kowa ba?!, Me ya sa za'a zaɓi da a lalata min rayuwa?!, Me na yi haka?! Wani kalar zunubi gareni?!, Allah na tuba ka yafemin, Allah na roƙeka da kada ka ƙara ɗoramin wata jarrabawa bayan wannan, ya Allah
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112