Chapter 105
Chapter 105
Ta fito ta zauna a danning ta fara cin abinci, sai da ta kusan gamawa sannan Rhoda ta ƙaraso, ba ta yarda sun tafi ba, sai da ta zubawa Rhodan abinci ita ma, Rhodan na ci Rabin na bata labarin ɗan uwan Aliyun da suka gano. Ita kuma Rhodan na ba ta bayani a kan shari'ar da za su shiga gobe. Da haka har suka gama, sannan Rhoda ta ɗaukesu zuwa can acadamy ɗin. Bayan da Rhodan ta kaita sai ta tafi, tare da faɗa mata cewar; idan sun gama, ta mata waya, ita kuma za ta zo ta ɗauketa. Rabi ce zaune a kan kujerar jira, sanye take da wannan jerseyn da kum wandonta, wanda ta saka leggings da kuma long sleeve high neck shirt a ƙasansu, ƙafarta sanye da football shoes. Kanta kuma rufe da baby hijjab, yanayin shigar tata akwai gwanin ban sha'awa, dan kaf matan dake wurin babu me irin shigarta, ba za ta ce babu musulmai a cikinsu ba, amma babu bahaushiya ko bafulatana ɗaya a cikinsu, duka 'ya'yan iyamurai ne. Shi ya sa ita ta fita da ban a cikinsu. “Rabi'a Muhammad!” Me tantancewar ya kira sunanta da ƙarfi, hakan ya sa ta amsa tana miƙewa. Inda ya nuna mata ta ƙarasa ta tsaya. Har zuwa yanzu ba ta da wani isasshen kuzari a jikinta, ga cikinta da take jin yana yamutsawa, kamar za ta yi amai. Amma kuma ba za ta bari hakan ya zama ƙalubale gareta wurin cimma burinta ba, ita ta sa kanta cewar za ta iya, kuma da yarda Allah za ta iya ɗin. Za ta yi abun da za ta bawa kowa mamaki, ciki kuwa harda 'yan uwanta na haɗejia. Ball aka sa musu a tsakiya ita da wata yarinya da ta karanta sunanta a bayan rigarta, wai ita ‘Chioma’. A yanayin girman jiki ta fi Rabi ƙiba, amma kuma Rabi ta ɗan fita tsayi, gata a ƙasa duf, ta ci doya da tuwon mama Iyabo ta ƙoshi. A sa'ilin da aka hura usur, a lokacin suka fara gudanar da wasan. Tashin farko sai da Chioma ta ci Rabi'a har sau biyu. Kasancewar ita Rabin babu kuzari a jikinta. Bayan sun ci gaba da wasan, Rabi ta kaiwa Chioma wani yanka, wanda ya sa Chioman ta yi amfani da ƙarfinta ta hankaɗa Rabi gefe. Faɗuwa ta yi, hakan ya sa gwiwar hannunta kurjewa da grass carpet ɗin dake shimfiɗe a wurin. Tashi ta yi zaune tana kallon Chioma ɗin. Me ya sa ta yarda kan cewa Chiomar za ta iya kada ta?, ita ma fa macace kamarta, babu wani abu da ta fita da shi, dan kawai ba ta jin daɗin jikinta sai ta saki jiki Chioma ta na nasara a kanta?, ya isa haka! Menene ba ta gani ba a duniya, ta shiga halin da ya ɗara wannan ma, ta ga ƙalubale a rayuwa wanda ba ta taɓa sanin zasu afko mata ba ko da a mafarki kuwa. Dan Chioma tana 'yar kudu ba shi ke nuna cewar ta fita ƙarfi ba, su ma matan arewa suna da tasu jajircewar, ya kamata ace ta nuna musu hakan. Cike da ƙarfin hali da na gwiwa ta miƙe tsaya, sannan ta koma aka ci gaba da wasa, wannan karon a zafafe take wasan, hakan yasa ta riƙa cin Chioma har sai da lokacinsu ya ƙare. Couches ɗin dake wajen ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin har yanzu Rabi'an ba ta manta da wasu abubuwa da ta koya daga garesu ba. “Ina taya ki murna mrs. Zaid!” Cewar ɗaya daga cikin Coach ɗin nasu yana miƙa mata hannu alamun su gaisa, hannun nasa ta kalla, yayin da take dafe da guwar hannunta na dama wanda ke mata ciwo. Kanta ta girgiza masa tana faɗin. “Sorry sir, but ni matar aureci” Hakan ya sa Coach ɗin janye hannunsa a sanyaye. Daga nan kuma sai aka turasu sashen fara ɗaukar darasi, tun a ranar aka fara musu training kuma ba su suka gama ba sai ƙarfe biyar na yamma. * Rhoda ce ke tuƙa motarta a kan titi, tana tafe tana biya waƙar Dalling Jesus dake tashi a motar. “I love you so much darling Jesus... My darling Jesus... Darling Jesus...” Wayarta ce ta yi ringing, hakan ya sa ta faka motar a gefen hanya, tana kashe waƙar. Ganin Zaid ne ke koranta ya sa ta kai hannu ta ɗau wayar tana ɗaga kiran. “Kina ina ?” Abun da muryarsa ta fara tambaya kenan bayan da ta ɗaga wayar, amon muryar tasa ya bata tsoro, dan sautin nasa na ɗauke da wani abu me kama da damuwa ko tsoro. Kamar me san tantance wani abu, ta shiga wulƙita idonta a kewayen wurin da take. “Ƙarfe shida yanzu, na kai Ammatanka gida ne... Kai wai ina ma ka shiga ne?” Ta ƙarashe tana jefa masa tambayar. Sai ta ji ya yi shiru, kafin yace. “Ki koma gidan ki ɗaukota, sannan ki kawota Hymill hospital!” Damm, gaban Rhoda ya buga. “Zaid! Zaid!. Me yake faruwa?. Ka ga ɗan uwan naka?” Ta tambaya a kiɗime. “Ki je ki zo da Adawiyya... Ɗaki me lamba ashirin da shida” Daga haka ya katse kiran ba tare da ya jira abun da za ta faɗi ba. A hankali Rhoda ta sauƙe wayar daga kunnenta, duk yadda aka yi ba lafiya ba. Dan haka ta tayar da motar da sauri ta juya kan motar zuwa gidan Zaid. RABI'A POV. Rhoda na aje ta a gidan ta shiga wanka. Kuma kafin ta bar banɗakin ma sai da ta yi amai, ta rasa abun da yake mata daɗi, ko mai ta ci ba ya zama a cikinta sai ya dawo. Haka ta ɗaura towel ta fito jiki ba ƙwari. Duk da yau tana cikin farin ciki sosai, domin a yanzu ta na ganin labarinta ya gama cika, tun da har Allah ya mallaka mata Zaid a matsayin miji, ya sa mahaifinta shiryuwa, ya ganar da Habiba da 'yarta Mama tafarki madai-daici, sannan ya nuna mata auren Anti Saratu, ya kuma cika mata burinta na ci gaba da buga ƙwallo. Ita kuwa me za ta ce? Da ya rage ta dage kan ibadunta, don ta nunawa Allah jin daɗinta kan ni'imomin da ya mata. Ta ƙarashe tunanin tana saka wata doguwar rigar atamfa. Wayarta ta dawo ta ɗauka, ta aikawa Zaid kira, dan ta na so ta ji daga gareshi, tana san ta ji wani hali yake ciki, shin ya haɗu da Aliyun?, ko ba su haɗu ba?. Sau huɗu tana shiga amma ba ya ɗagawa, hakan ya sata shiga mamaki, a gefe guda kuma sai tsoro ya fara shigarta. Ta kama hanya da niyyar barin ɗakin aka turo ƙofar ɗakin da ƙarfu, Rhodan da ta tafi a ɗazu ce ta dawo, cikin wani irin birkitaccen yanayi da Rabin ta kasa gane masa. *Hymill Specialist Hospital, Life camp, Abuja* *07:00pm* MISHAL POV. Zaune take kan wata kujera dake bakin ƙofar ɗakin da aka kwantar da Aliyu bayan zuwansu asibiti a daren jiya. Abun da likitocin suka rara sanar musu shi ne, ya rasa jini da yawa, haka aka gwada na Zaid, sannan aka ɗiba ganin ya dace da nasa. Kuma tun safe ake ƙara masa jinin. Bai ƙare ba sai da azahar,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112