Chapter 46
Chapter 46
cikin kogin soyyaya! ” Raja ya kai hannunsa ya dunguri kanta yana kamo wuyanta. Ya ɗaga kafaɗarsa yana faɗin. “Cuzzie yaushe kika fara sa ido?” “Sanda ka faɗa soyyayar gaskiya... Ba irin wadda kake a da ba” Maganarta ta tuno masa da ita, Uchechi!, Wani sashi na kansa ya ambato masa sunanta, a hankali ya saki wuyan Rhoda, yana tuno alaƙar dake tsakaninsa da ita, kenan da shi ba son Uchechi yake ba?, to kenan da me yake ji a kanta?, kuma me yake ji a kan Ammantasa?. Tukkuna ma wani hali Uchechi ke ciki, tun bayan zuwansa Abuja ba su yi waya da ita ba. Naushin da Rhoda ta sakar masa a ƙirji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa yana kallonta. “Tunani ba? Ai da ma sai da na faɗa maka cewar ba son Uchechi kake ba, kuma ita ma ba sanka take ba, kuɗinka take so, kai ne ka kasa banbancewa tsakanin son gaskiya da na yaudara!...” Kallon ta ya yi na wasu 'yan sakkani, kafin ya kamo kunnenta. “Thunder go fire your head Rhoda! Ki ce har zarar zance kika koya?” “Zaid...” “Shiru! Ba na san wata magana!” Sai ta yi shiru tana sosa kunnenta da ya saki, tare da turo masa baki gaba. “Sorry” Ta faɗi tana sinne kai ƙasa, janyota ya yi ya mata side hug, kafin ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama yace. “Ke ɗin ce bakya jin magan Cuzzie... Maza mu je akwai aiki a gaban mu” Nan da nan Rhoda ta dawo serious, tunawa da ta yi da aikin dake jiransu a gaba, aikin shigo da makaman da Alhaji Bala ya ɗorasu a kai. *Hotoro, Ring Road, Kano...* Uchechi ce zaune a ɗakinta, ta sa gabanta yamma tana kallon mirror, yayin da take zaune a kan stool, kallon fuskarta take a mirrorn, yayinda take neman wani abu a fuskarta da wata ƙila shi ya sa Raja yake mata abun da ya so, wata ƙila ba ta da kyau yanda ya kamata, ko kuma akwai wani tabo a fuskarta da ya sa Rajan ba ya san kusantarta. Ƙofar ɗakin aka turo, kuma ba tare da ta juya ta kalli ƙofar ba, ta hango wanda ta shigo ɗikin, Mesoma ce, yayarta wadda take riƙe da ita. Ba ta juya ba har Mesoman ta zauna a bakin gadon dake bayanta, ta na ci gaba da kallonta. “Wai Uchechi ba za ki manta da wannan Rajan ba?... Tun da har ba za ki iya sato zuciyarsa ba, kuma ba za ki iya samawa kan ki ruwan da zai kashe miki ƙishin ruwar ki a kansa ba, zai fi kyau ki manta da shi” Juyowa ta yi ta kalleta. “Mesoma ina san Raja... Ba na jin zan iya rabuwa da shi, duk munin abun da zai min kuwa, batun samun Raja kuwa zan daure na yi haƙuri har zuwa lokacin da ya tsara mana dan mu yi aure, tun da yace ba zan taɓa samunsa ba idan har ba aure muka yi ba” Mesoma ta rage girman idonta tana kallon ƙanwarta. “Hanyoyi nawa na tsara miki na yanda za ki samu kuɗi a hannunsa ?, Da na tsara mikin ba ki samu ba ?” Uchechi ta girgiza kanta. “Na samu, na samu abun da ban yi zanton samu ba” “To me yasa da na tsara miki hanyar da za ki samu kansa ba ki bi ba?” “Mesoma ba zan iya bin hanyar da kika tsara min ba, waɗannan hanyoyin naki sun yi tsauri da yawa” Mesoma ta miƙe tsaye. “So... That was the only way that i have, tun da kin ga ba za ki iya bi ba, sai ki yi ta zama cikin ƙunci” Da sauri Uchechi ta miƙe tana kamo hannunta. “Ki temaka ki nemo min wata hanyar” “Ba ni da wata hanya bayan wadda na riga ma baki, idan kin ga za ki iya binta, fine, if not sai ki sa haƙuri a zuciyarki” Mesoma ta kama hanya ta fice daga ɗakin, cike da neman mafita Uchechi ta koma ta zauna a kan stool, ta furzar da iska daga bakinta. Cike da takaici ta yi fatali da kayan dake kan mirrorn. To wai ita ya za ta yi ne?, me ya kamata ta yi dan samun kan Raja?, wata hanya ya kamata ta bi don ta mallakeshi?!. *No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.* “Wallahi Musa tun muna shaida juna ka kira wannan yaron da kuka aurawa jikata, ya faɗa mana ina ya kaita! In ba haka ba Wallahi sai nai maka abun da kowa zai zo yana nadamarsa!” Muryar Jadda ke faɗin hakan cike da masifa, yayin da wayarta ke kare a kunneta, daga gefenta kuma Hajjara ce zaune tana ƙunshe dariyar muguntar dake cinta, dan ita ta kunno wutar. Suna zaune ne a falon gidan, yayin da Jaddan ke ta sirfawa Ammu Musa buhun bala'i. “Wai dan Allah Jadda haka ake rayuwa?, Ta ya za ki ce na kira mutum na tambayeshi inda ya kai matarsa?” Muryar Ammu Musa ta faɗi cike da gajiyawa da halin Jadda. “Au haka ma ka ce? To ka kyauta, Wallahi za ka ga abin da zan maka, shashasha, wanda bai san inda ke masa ciwo ba!” Daga haka ta latse wayar ta cillar da ita gefe tana hucin bala'i. “Gaskiya Jadda Ammu Musa bai kyauta ba, ta ya zai ɗauki 'yarmu ya bawa wani wanda ba musan shi ba? Ba mu sani ba ma wata ƙila ɗan ya kan kai ne?” Cike da san tittilawa wutar fetir Hajjara ke bayanin, dan har yau ba ta manta da abun da Mishal ɗin ta yi mata ba, gashi dai takaba take, amma baƙin cikin Mishal ɗin bai bar ruhinta ba. Aiko fiterin da ta bilbila ɗin ya sauƙa a tsakiyar zuciyar wutar, don ta tashi sama ta ƙara ruruwa fiye da yanda take ci a da. “Aiko ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ko ni ko Musa, dan Wallahi ba zan zauna ina gani ya sabautar min da jika ba, duk in da zai je dole ya dawo ya sameni, dan Wallahi ba zan bar garin Abuja ba sai na san gidan da ya kai min jika” Nan take murnar da Hajjara ke ti ta koma ciki, don kuwa ita ba haka ta so ba, ta so a ce da zarar Jaddan ta gama abun da za ta yi ta kama hanya ta koma Maiduguri, ita kuma a bar mata gidanta ita ɗaya, tun da yanzu ɗayar abokiyar gabar tata ba ta nan, sai ta mulka gidan san ranta, duk da Ammu Musa ya ce idan an yi arba'in za'a raba gado, don akwai dukiyar Mishal da Abubakar ɗin ya ba shi riƙo. Wutar da take ganin ta hura sai ta dawo kanta,sakamakon mantawa da ta yi ba ta janye hannunta daga saman wutar a sanda ta tittila fetirin ba, Zama da Jadda?, tashin hankali kenan. _____________________ _Wayyo Allah cikina!🤣🤣_ _Kai jama'a, wai aka ce idan za ka haƙa ramin mugunta, ka gina shi gajere, kuma an ce mugunta sayin faƙo, idan baka iya ba ka ɓata jikinka_ _Ga Uchechi a kan layi..._ _Wani ya faɗamin abun da zai faru a aanda Uchechi ta san cewa Raja ya faɗa soyyaya da wata_ _Sannan ga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112