Chapter 26
Chapter 26
kallonta, amma dan kada ta raina shi, sai kai wai ya ƙi ya kalleta ma bare ya amsa gaisuwar. Abun ya bawa Mishal haushi, duk da ba da ƙarfi ta yi maganar ba ai yaci a ce ya ji gaisuwar, bata iya ɓoye-ɓoye ko riƙe fushi ba, don haka ta kalle shi tace. “Ba ka ji ina gaida ka ba ne ?!...” Sai a lokacin ta kalli abinda ba ta lura da shi ba a kallo na farko da ta masa, kammanin fuskarsa, kammace sak irinta Antinta ADAWIYYA!, kenan yayanta ne?, ko ɗan uwanta ne ?.... Haka tunanin ya ci gaba da yawo a cikin kanta. Ba Kuliya kawai ba, hatta da Abubakar kallonta ya yi, abun ya bashi mamaki, a cikin shekarunsa za'a iya kwasar nata, kuma a bar sauran da zai isa a bawa wani mai hankalin. Amma ko tsoro babu a idonta ta kalleshi take masa magana a tsaye. Idonta da ya kalla ne yasa gabannsa wani irin bugu, wanda sai da ya ji ƙaran bugun zuciyarsa a kunnuwansa. Ƙwayar idonta na da kyau kamar fuskarta, wasu irin olive green colour eyes gareta... #Labarinsu #SaiKaska #TaurariWriter's ••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *07* ~~~ *Once you taste a true love, ordinary will never do...* *** *No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja* A fusace Anna ta shigo cikin gidan, ta ja ta tsaya tana kallon Siyama dake zaune a falo, ita ta ma manta da Siyaman, wadda ta zo gidan a daren jiya. A yau da safe su na karin kummalo wayar Kuliya ta sameta, hakan yasa ba shiri ta tafi asibitin. Siyama 'ya ce a wurin ƙanwarta, wadda ta rasu, su biyu ne yaran ƙanwar tata, Siyaman da yayarta Karima. Siyama ta zauna a wurinta tsawon shekaru, kafin zamanta ya koma gidan yayarta Karima, amma duk da haka Siyaman na kawo mata ziyara akai-akai. Siyama ta miƙe tsaye da sauri, hankali tashe ta na duban Anna, dan Allah ya sani, ta raya abubuwa mabanbanta a cikin ranta, kan abun da ya samu masoyinta, saboda tun da Anna tace mata Kuliya ne ya yi hatsari hankalinta ya tashi, har da kukanta a sanda Annan ta tafi. “Anna ya jikin nasa ?... Fatan ba wani mummunan ciwo ya ji ba?” Anna ta kafeta da ido tana kallonta, tun ba yau ba ta riga da sanin cewa Siyama na san Kuliya, amma ita a ganinta kamar hakan ba mai iyu ba ne, ba za ta iya tilasta Kuliya kan ya auri 'yar ƙanwarta ba, duk da tasan cewa idan tace ya yi hakan ko da ba ya so zai yi, amma ba ta san tilasta masa yin abun da baya so. Bugu da ƙari ma sam Siyama ba ta dace da Kuliya ba, ba wai kyau ne ba ta da shi ba, ba wai ba ta da hali mai kyau ba ne, a'a, sai don sam halayenta ba za du dace da nasa ba, Kuliya ba irin Siyama yake buƙata a matsayin mata ba. Anna ta mata banza, ta cire hijabin jikinta, tare da rataya shi a jikin kujera, kafin ta zauna. Ganin haka yasa hankalin Siyama ƙara tashi, amma sai ta shiga ƙoƙarin danne hakan, ta yi sauri ta faɗa ɗakinta na gidan, ta shiga banɗaki, ta kulle, tare da sakin kuka, ta jingina da jikin ƙofar bayin, zuciyarta na mata zugi. Ta sha addu'ar Allah ya cire mata san Kuliya a ranta, don ta san cewa wannan son maso wani take, kuma da ma hausawa sun ce ƙoshin wahala ne. Kuma gashi tana wahalar, saboda Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki. *Brickhall school, Kaura District, Abuja* RABI'A POV. Bayan ta gama aikinta na safiyar yau, sai ta dawo senior section ta zauna, tana ta zuba ido ko za ta ga gilmawar ƙanwarta amma shiru. Har lokacin zuwa makatanar ya wuce, ɗalibai sun riga da sun fara darasa. Ta miƙe za ta bar wurin, da zaton cewa wata ƙila yau ɗin ma ba za ta zo ba kamar jiya, sai kuma ta ja ta tsaya ganin Mishal ɗin na doso wurin, jakarta goye a bayanta, hannunta na dama riƙe da suit ɗinta, yayin da tsintsiyar hannunta na hagu ke liƙe da plaster. Ganin plastern ne ya tadawa Rabi hankali, hakan ya sa ta dosheta da sauri. Tun daga nesa Mishal ɗin ma ta ganeta, don haka ta ƙara saurin tafiyarta tana sakar mata murmushi. “Ƙanwata me ya samu hannunki ?” Abun da Rabin ta fara tambaya kenan, bayan da ta isa gaban Mishal. Mishal ta ɗaga hannunta na hagu ta kalla, sannan tace. “Ba wata damuwa fa Sisto, is not big deal, wani ɗan ƙaramin raunine na samu, and na je asibiti an yi treating ɗinsa, so forget about me, what happened to your own hand?” Ta tambaya a sanda ta ga raunin hannun Rabin. Kuma maganar tata ta tunawa Rabin zagayen halin da take ciki. Fuskar nan wadda ke ɗauke da kammaninta ta tuna, amma sai ta share tace. “Me too... Babu komai, just small injury” Mishal ta ci gaba da kallonta tana mamakinta. “Sis na tambayeki mana” Rabi'a ta gyaɗa mata kai alamun tana saurarenta. “Me yasa kike aiki a nan?” Rabi ta ɗan juya kanta ta kalli inda suke, kamar me neman wani, sai kuma ta juyo ta kalli Mishal ɗin. “Ƙanwata an fara darasi, ki je ki ɗauki karanatuki, na miki alƙawarin faɗa miki gobe idan Allah ya kaimu...” Mishal ba ta ƙara cewa komai ba, sai kawai ta gyaɗa mata kai, kafin ta wuce. Rabi ta bi bayanta da kallo tana murmushi. RAJA POV. Tare da Rhoda suka fito daga estate ɗin da suka kama gida a ciki, magana suke kan yanda haɗuwarsu da Alhaji Bala za ta kasance a daren yau, don a ɗazu ya kira waya ya sanar da su cewara a yau ne yake so su haɗu. A jikin wata mota dake fake a ƙofar gate ɗin estate ɗin suka tsaya. Ya na sauraron jawabin Rhoda, yayin da lumaassun idanuwasa ke kallon ɗaliban makaranarar tsallaken estate. BRICKHALL SCHOOL, shi ne sunan makarantar. Lokacin tashi ya yi, dan ɗaliban tafiya gida suke, wasu a motoci ake ɗaukarsu, wasu kuma a school bus. Wata magana da Rhodabta faɗa ce ta jawo hankalinsa, hakan ya sa ya juyo ya kalleta. Tunaninsa ya tsaya cak, sakamakon hoton da ya taho masa da fuskarta. Wannan fuskar da ke kwance a kan tasa fuskar, wannan fuskar da ke kwance a ta Aliyu, haka kuma ita ce kwance a ta Momma. Da sauri ya juya ya kalli inda ya ganta, fitowa take daga cikin makarantar ita ma, sai dai ita ba ta sanye da uniform, yanayin shigarta ba zai bari ya yi tunanin cewa za ta iya zama ɗalibar makaranatar ba, kuma shekarunta ba za su bari a kirata da malama ba. To me take a nan ɗin?. RABI'A POV. Tana fitowa daga makarantar ta shiga dube-dube ko za ta ga ƙanwarta, dan tun da safiyar yau da suka haɗu ba su sake haɗuwa ba, gashi har an tashi. A maimakon ta ga Mishal ɗin da take nema, sai idanuwanta suka kallo mata wannan fuskar. Tsaye a tsallaken makarantar, jingine jikin wata mota, sanye cikin T-shirt da jeans, gefensa kuma wannan matar ce da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112