Skip to content

Chapter 101

Chapter 101

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

dariya a tare, ashe soyyayar da sukewa juna ba za ta faɗi ƙasa ba, ashe Allah ya hukunta zamowarsu facalolin juna. Dariyar da Mishal ta yi ce ta sa jikinta jijjiga, hakan ya sa ta yi famu, sai ta ɗan cije lips ɗinta cikin jin zafi. Sai a lokacin Rabi ta lura da abun da yake faruwa da ƙanwar tata. “Me yake damunki Ƙanwata?” Nan da nan ƙwalla ta cika idon Mishal, ta turo bakinta gaba tana shirin fashewa da kuka. “Wallahi Anti Adawiyya Abu Aswad mugu ne, kuma zuciyarsa ma baƙa ce kamar kayansa, da ma ai na faɗa masa cewar sai na faɗa miki idan muka haɗu...” Nan take Rabi ta gane inda zancen ya dosa, amma kuma sai sunan da ta kira mijin nata da shi ya bata dariya. “Abu Aswad kuma Mishal?” Mishal ta share ƙwallar da ta zubo mata. “Abu Aswad mana, ba shi ne ba kullum cikin saka baƙaƙen kaya, shi ya sa na saka masa sunan...” “Na ji kin ce kin gaya masa cewar za ki gayamin abun da ya miki, da ma ya sanni ne?” Mishal ta kuma goge ƙwalla. “Ya sanki mana. Sanda kika ɓata shi na sa ya yi ta nemanki, kuma na san cewa shi ma ya gano cewar an saceki , amma shi ne ya ƙi faɗa min” Haƙuri Rabi ta shiga bata, kafin ta ƙarashe da bata shawarwari kan yadda za ta kula da kanta, da kuma gyara jikinta. Basu rabu ba sai da suka yiwa juna alƙawarin sanin dalilin rabuwar waɗanan 'yan uwan biyu. *No.86, Garki 2, Abuja...* *07:30pm* ZAID POV. Gama wayarsa da shugabansu ke da wuya, ya ji wayar ta sa na ringing. Hakan ya sa ya duba screen ɗin wayar, don ganin me kiran. Ganin Kawu Abdullahi ne ya sa shi yin murmushi, ya na ɗaga kiran. Gaisawa suka yi cike da girmamawa, kafin dalilin kiran ya taso. “Ɗazu muke jin wani zance a gida. Wai ka kai Rabi'a makarantar ƙwallon ƙafa!” Zaid dake tsaye a ƙofar ɗakinsa ya sosa kansa cikin jin nauyi, kafin yace. “Eh haka ne” “To tun wuri, ka yi gaggawar janye wannan ƙudirin naka... Ka bar ganin ita matarka ce, mu iyayenku ne, tun farko ya kamata ace ka shawarce mu kafin ka yanke hukunci a kanta. Ko a sanda take yarinya da mahaifiyarta ta kaita makarantar ba so muke ba, dan de muna ga yarinya ce, shi ya sa muka yi shiru. Amma a yanzu ta girma, tun da har mun mata aure, dan haka ba zamu ɗauki wannan shashancin ba. Tana mace me ya haɗata da wata ƙwallo?, zaman gida da kula da tarbiyyar yara shi ne ya dace da ita, ba gudu da gajeren wando a kan idon tarin mutane ba!...” Haka Zaid ya ja bakinsa ya yi shiru, har Kawun ya kai ƙarshe a faɗan nasa bai ce masa ƙala ba, sai da ya tabbatar da Kawun ya kai ƙarshe a wajen amayar da abun da ke bakinsa kafin ya seta kamillalliyar muryarsa, ya shiga koro bayani a natse, kuma cikin da girmamawa. “Na fahimce ka Kawu, kuma duk abun da ka faɗi gaskiya ne. Amma kuma ita ma Adawiyya tana da gaskiya. Ka san a ina ta yi gaskiya?” Kawu Abdullahi dake zaune a kusa da su Baba ya juya ya kallesu, dan kuwa suma suna jin duk maganar da Zaid ɗin yake, sai kuma ya girgiza kansa cikin faɗin. “A'a, sai ka faɗa” “Lokacin da ta farfaɗo a asbiti, ta kalli idona tace min maza ba su da adalci, kansu kawai suka sani; kuma kasan dalili?” Ya tambaya ba dan ya na buƙatar amsa ba, dan kafin ya amsa masa ya ci gaba da cewa. “Dalilin shi ne; mu maza a kullum gani muke mune a gaba, dan haka dole duk abun da muke so shi za'a ayi, hakan ba wai kuskure ba ne, saboda mu Allah ya bawa girma, amma kuma su ma suna da nasu 'yancin. Domin ko addini ya basu 'yanci, daraja da kima, sai de ni kuma a yau ba ma duba hakan, sai namiji ya auri mace, ya zaunar da ita a gida, ya hanata rawar gaban hantsi, ya sa ƙafa ya take mata burinta da kuma 'yancinta, ga shi de ba ta son abun da yake mata, amma saboda ganin ita macace sai ta haƙura ta ja bakinta ta yi shiru. Kawu a mafiya yawan lokuta muna dannewa mata hakkinsu, suna da baiwa kamar mu, suna da shauƙi kamar mu, suna da zuciya kamar mu, duk abun da zai fusata mu suma zai iya fusata su, banbanci mu da su shi ne, su sukan iya jurewa abun su shanye a cikinsu, wata dan 'ya'yanta, wata dan iyayenta, wata ma dan mijin shi kansa, haka za ta jure rintsi da wuya. Kawu, Adawiyya ta shiga taskun rayuwa kala-kala, taga iftila'i da ban da ban, yanzu ne ya kamata ace ta samu jin daɗi da hutu, a yanzu ya kamata ace burukanta sun cika. Ni kuma ina son ta yi farin ciki, kuma na yi alƙawarin sama mata duk wani abu da zai dawwamar da murmushi a fuskarta. Ƙwallo mafarkinta ne, lefi ne dan na temaka wurin ganin ya zama gaskiya?!” Shiruuu, har bayan shuɗewar wani lokaci, a cikin wannan shirun Baba dake kishingiɗe ya miƙe zaune da kyau, cikin alfaharin kasancewar Zaid jika a gareshi, Kawu Abdullahi kuma nadamar kiransa da masa wannan kashedin yake. Kasa cewa komai ya yi, ya kashe wayar. Jin wayar ta katse ya sa shi sauƙe wayar. Sannan ya fita daga ɗakin, dan da ma niyyar fita yake, kiran shugaban nasa ya same shi. Shi ya sa ya tsaya ya amsa saboda muhimmanci kiran. Kitchen ya nufa, dan ya san ba za ta wuce can ba. Damm, zuciyarsa ta harba bindiga, lokacin da ya saka ƙafarsa a cikin kitchen ɗin, abu na farko da ya fara arba da shi shi ne, Wutar gas a kunne tana ci. Irin waɗanan dalilan ya sa baya san shiga kitchen, ko da magana yake san yi da Rhoda idan har tana kitchen sai de ya haƙura. Ba shiri ya ji kansa na juyawa, duniyar ta fara masa duhu, numfashinsa ya shiga kokawar ɗaukewa. Rabi dake wanke nama a sink ta juyo da sauri jin fitar wani kalar numfashi. “Ga ruwa” Cewar Rabi tana miƙa masa ruwa a cikin wani glass cup, Zaid da ke zaune kan kujera a falo ya ɗago da kansa ya kalleta. Kafaɗarsa ya daga ya na miƙa hannunsa tare da karɓar glass ɗin. Rabi ta zauna a gefensa tana shafa kafaɗarsa a sanda yake shan ruwan. Ita ta karɓi cup ɗin ta aje, bayan da ya kammala shan ruwan. Gefen fuskarsa take kallo cike da damuwa. Har zuwa lokacin tana shafa kafaɗarsa a hankali. “Na zubo maka abinci?” Zaid da ya cilla duniyar tunani ya girgiza mata kai, ya na jingina da bayan kujera, hakan ya sa Rabi ta ɗauke hannunta daga bayansa, ta dawo da shi ƙirjinsa tana masa tausa. Ganin har zuwa lokacin be dawo dai-dai ba ya sa tace. “Me yake damunka wai?” Kallon fuskarta ya yi na wasu 'yan sakkani, sai kuma ya kama hannunta dake kan ƙirjinsa, ya kwantar da ita akan ƙirjin nasa, ta yanda har

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112