Skip to content

Chapter 100

Chapter 100

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

sai ta ji kasala ta kamata, ta ji jikinta duk ba daɗi. Kafin ta fito daga banɗakin ma sai take jin juwa na ɗinbata. Da ƙyar ta iya ƙarasawa ta zauna a bakin gadonta, hannunta na dama dafe da cikinta. A dai-dai lokacin Zaid ya shigo ɗakin yana kiranta, ba ta samu damar amsawa ba, face binsa da kallo kawai da take, ganin yanayinta ya ɗarsa masa wani zargi a ransa. “Baki da lafiya ne?” Kanta ta girgiza masa tana miƙewa. “Lafiyata ƙalau” Be yarda ba, amma ba ya so ya takura mata, sai kawai ya gyaɗa kansa ya na kama hannunta. “Na fahimta... Kin shirya?” Kanta ta gyaɗa tana ɗan cije baki, saboda cikinta da take jinsa babu daɗi. “Raj!... Me muke a nan?” Muryar Rabi ta tambaya, a sanda ta ga Zaid ya kawosu wata football academy, makarantar da ta yi ta lokacin tana yarinya, dan a sanda Ummanta ke da rai nan take kawota training ɗin ball.‘As Roma Football Academy’ haka sunan makarantar. Zaid be amsa mata ba, sai fita da ya yi daga motar, sannan ya zagayo ta ɓangarenta, ya buɗe mata motar, mamaki ya ƙi barin kan Rabi, haka ta fito baki buɗe, sai bin wurin take da kallo, wurin da rabonta da shi kusan shekaru shida kenan. “Zuwa yanzu ta girma... Dan haka ba daga rukunin da ta tsaya za ta ci gaba ba, za mu turata cikin rukunin sa'o'inta” Cewar shugaban makarantar, yayinda Zaid da Rabi ke zaune a tsallaken teburin office ɗinsa. Zaid ya gyaɗa kansa, duk da ba yau ya fara faɗa masa hakan ba, tun ranar da ya fara zuwa makarantar shugaban ya sanar masa da wannan batun. Kuma ya yarda da hakan, shi ya sa ma ya kaita aka mata gwaji a asibiti, kafin ta fara buga ƙwallon da ta kasance burin rayuwarta. Juyowa ya yi ya kalleta. A dai-dai lokacin da ita ma ta kalleshi, idonta ya ciko da ƙwalla, bakinta har rawa yake, ta ma rasa abun da za ta ce da shi, sai kawai ta kafe shi da ido tana kallo. Da haka suka bar office ɗin, aka bata kayan da zata riƙa sakawa idan ta zo makarantar, wata jar jersy ce, da wandonta, shugaban ya sanar musu da cewar zuwa gobe za su dawo, domin za su mata gwaji, idan ta ci gwajin da za su mata, za ta iya fara karɓar horo tun daga ranar. Suna tafe a mota ledar kayan na kan cinyar Rabi, hannunta ta kai ta fito da jersyn ta ɗagata sama tana kallo. ‘ADAWIYYA’ shi ne abun da aka rubuta a bayan rigar. Ƙwallar da take ta shanyewa tun ɗazu ce ta gangaro kan kuncinta. Sai ta ga kamar tana rayuwa ne cikin mafarki, domin da ƙwallo a mafarki take ganinta, bayan hargitsin da ya ahigo rayuwarta sai ta manta da ƙwallon. Ta haƙa wani wawaken rami a zuciyarta, ta cilla burikanta na rayuwa, ta binnesu, don a lokacin gani take rayuwar tata ta zo ƙarshe, labarinta ma ya ƙare, komai ma ya ƙare. Shigowar Zaid rayuwata ya sauya komai, ya sauya yanda take kallon kanta, ya sauya yanda take ganin rayuwa, ya cika mata burikanta na rayuwa, duk abubuwan da take ganin ba masu iyuwa ba ne sun iyu, ta rasa me zata ce da shi, tace ta gode?, a'a, godiya ta yi kaɗan ta isar da shi, addu'a ita ce kawai abun da ya kamata ta masa, sannan ta ba shi ko wace kulawa, ƙauna da soyyaya. Ganin ya nufi hanyar Kaura ya sa ta share hawayenta, don bayan wani lokaci me tsayi, yau Allah ya yi za ta haɗu da ƙanwarta. Sai da suka fara zuwa suka ga Rhoda, kafin ta fice ita ɗaya, bayan ta da faɗa musu cewar za ta je ta ga ƙanwarta, Zaid be hanata ba, don shi ma ya na so su tattauna da Rhoda kan case ɗinsu, saboda suna kyatata zaton zuwa gobe za'a shiga kotu. Kanta tsaye Rabi ta shiga makarantar, masu gadi sai tambayarta suke, kan dalilin dena zuwanta makarantar, ita kuma tana amsa musu da rashin lafiya ta yi, kuma su ma sai suka yarda, saboda ganin tabon dake kwance a gefen fuskarta. Duk da sun ga sauyi sosai a tare da ita. Kafin ta kai ss3 har ta fara hawaye, saboda ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, ta ƙagu ta haɗu da Mishal, don ta bata labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu. Cikin wata irin sa'a, tana isa ƙofar ajin ana kaɗa ƙararrawar break, hakan ya sa ta tsaya cike da zumuɗi tana san ganin fitowar Mishal. Sai da ko wani ɗalibi ya fice daga ajin, kafin Mishal ta miƙe tana muzurai, sai ciza baki take don tafiyar ma da ƙyar take, haka ta shiga taku cikin ƙarfin hali, har ta kai waje. Ba tare da ta lura da wanda ke tsaye a bakin ƙofar ajinsu ba ta fara tafiya ta na nufar playground. Rabi'a ta lura da yanayin tafiyarta, amma kuma ɗaukin ganinta ya sa ta ture komai tace. “Mishal!” Cak Mishal ta tsaya da tafiyar da take, sakamakon sauƙar sautin muryar yayarta da ta ji, yayarta mafi soyiwa a ranta, yayarta da take ji da ita, yayarta da take cikin halin damuwa na rashin ganinta. “... Kin ji abun da ya faru da ni!” Cewar Rabi, a sa'ilin da ta ɗiga aya a ƙarashen labarin da take bawa Mishal, suna zaune ne kan kujerun da suka saba zama a da, Mishal wadda idonta ya cika da ƙwalla ta kalli yayarta. Duk da Yazid bai samu damar ci mata zarafi ba, amma ta san yaya zafin abun yake, ta san irin baƙin ciki da ƙuncin da ake shiga, ta san zafi da tabon da abun kan barwa 'ya macen da ta fuskance shi. Ita ba ta da wani wayo sosai, amma ta san irin ƙasƙancin da mata 'yan uwanta kan fuskanta, idan har basu kai budurcinsu ɗakin mazajensu ba. Duk da ita Adawiyyan ta tsallake wannan ramin. “Yaya ina so na faɗa miki wani abu” Rabi ta share hawayenta tana kallon Mishal. “Kina kama da Aliyu, kuma na san ke ma kin san hakan, kina da danganta da shi?” Rabi ta yi murmushi tana ɗauke kai. “Wata ƙila idan na faɗa miki ba za ki yarda ba. Amma mijinki cousin brother ɗina ne, sannan kuma shi ne ƙanin mijina. Ɗan biyunsa ne, amma abun da ya shiga tsakaninsu ya rabasu ne... ban sani ba” Wani irin shiru ya gifta a wurin, ba ka jin komai sai sautin wucewar iska. A cikin wannan shirun, Mishal ta kunce ta kuma saƙa ya fi sau a ƙirga. Kenan wannan wanda take gani a tsallaken makarantarsu shi ne Zaid ɗin da Adawiyya ta aura?. “Da... Da ma Raja shi ne Zaid ɗin?” Mamaki ya kama Rabi. ”Kin san shi ne?” Mishal ta gyaɗa kanta da sauri ta na share ƙwalla. “Na sanshi...” Rabi ta yi ajiyar zuciya tana ɗaga kanta sama. “Ya kamata mu san abun da ke faruwa a tsakaninsu” Rabi ta faɗi tana sauƙe kanta ƙasa. Mishal ma kai ta gyaɗa mata cike da gamsuwa. “Yau idan muka koma gida zan tambayi Aliyu” Rabi ta yi murmushi. “Ni kuma zan tambayi Zaid” Sai kuma suka yi

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112