Chapter 31
Chapter 31
motar, ciniki suka yi da mai motar, ya zaro kuɗin ya biya, har da haɗa shi da gargaɗin kada ya ɗauki wani bayan ita, sannan kada ya yi gudu da ita. “Sai gobe 'Yan mata” Ya faɗi sunan in full, saɓanin da da yake faɗarsa a wata sigar. Rabi'a ba ta iya ce masa komai ba, sai hannun da ta ɗaga masa. Motar ta fara tafiya, zuciyarta na ƙara cika damamaki da tunanika iri-iri. *DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja* KULIYA POV. Tsaye suke a ɗakin tattaunawa na headquartern, yayin da ya buɗe musu map ɗin wurin da za su wa dirar mikiya a yau ɗin nan, don a yau aka basu damar kamo 'yan ta'addan da suke bincike a kansu. Sharon, Kamis, Sani, Mubarak, Symon da kuma shi kansa, su ne tsaye, kana kewaye da teburin da taswirar ke kai. “Wannan ita ce hanyar shiga gudan... Ta nan za mu shiga, akwai ƙofa ta baya, dan haka za su iya guduwa idan suka gane cewa muna cikin gidan... Dan haka Ab...” Bai ko ƙarasa furta sunan Abubakar ɗin ba, Abubakar ya turo ƙofar ya shigo, a tare suka ɗaga kai suka kalleshi. A gurguje ya ƙaraso ya tsaya a jikin teburin shi ma. “I'm so sorry guys, cinkoson ababen abun hawa ne ya makarar da ni” Kuliya ya haɗiye wani abu, a sanda ya ɗora idonsa a kansa, kammaninta suka faɗo masa a rai. Yarinyar nan ta rakurawa tunaninsa, ya gaji!, me yasa wai take damunsa ne ?. Sai ya ɗaga kafaɗarsa, sannan ya juya ya ci gaba da kallon taswirar. “Abubakar kai da Symon za ku tsaya ta nan, ni da Sharon, Kamis da Sani, za mu shiga...” Bai ƙarasa ba Abubakar ya dakatar da shi, ta hanyar furta abun da zai zama sanadiyyar faruwar ƙaddarar da Allah ya hukunta a wannan ranar. “Me zai hana ni da kai, Sharon, Kamis da Sani, mu shiga cikin gidan, Symon da Mubarak sai su tsaya a ƙofar baya!...” Cike da gamsuwa Kuliya ya gyaɗa kansa. “Well, hakan ma ya yi, Good to go guys!” “Yes Sir!” Suka amsa kusan a tare, sannan suka yi azamar fitar. *Abacha Road, Abuja...* Motoci ne guda biyu suka yi parking a ƙofar wani madai-daicin gida, cikin gaggawa ƙofofin motocin biyu suka buɗe a tare. Kuliya, Mubarak, Sharon, Kamis, Symon, Sani da Abubakar suka fito, kowannensu sanye da baƙaƙen kaya irin na aikinsu, jikin bullet proof jacket ɗin kowanne daga cikinsu an rubuta 'DSS' da farin rubutu. Kowanne a cikinsu hannunsa riƙe da bindiga, Kuliya ne ya yi wa Symon da Mubarak alama da su zaga ya ta bayan gidan, cikin sassarfa suka bi umarninsa. Shi da sauran kuma suka nufi cikin gidan. Shi ne kan gaba, su kuma biye da shi. Daga cikin gidan kuma, mutum biyar ne zaune kan kujeru, baje a gabansu kayan maye ne kala-kala, mace ɗaya ce a cikinsu, yayin da sauran suka kasance maza. “Chizoba, wai ka biya me tifar nan da ya kaɗe Kuliya ?” Ogansu dake zaune kan kujera ya tamabaya cikin harshen igbo. Chizoba ya amsa masa da: “Eh mana, dubu talatin na bashi” Ogan ya yi dariya, yana hango nasarasu a cikin idanuwansa, a sanda suka sauƙa a garin sai da aka sanar musu da cewar wani wai shi Kuliya zai kawo musu cikas. Kuma da suka bincika sai suka samu cewa ma a kansu yake bincike, hakan yasa suka saka wani me tifa ya daki motarsa, a sanda ya tashi daga wurin aiki. Yanda suka ga motarsa ta yi raga-raga ne yasa suka ɗauka cewar ya mutu. Babu wani mai basu matsala kan aikin da ya kawo su garin Abuja. A tunaninsu kenan, sai dai cikin abin da bai fi muntuna uku ba, komai ya sauya. Gidan ya karaɗe da ƙarar harbe-harbe. Daga waje babu abin da ke tashi sai ƙarar musayar wutar da ake tsakaninsu da su Kuliya. Kuma a cikin musayar wutar ne, ɗaya daga cikin 'yan ta'addan ya aikowa da Kuliya harbi, kasancewar shi bai lura ba, yansa harbin bai same shi ba, Abubakar da ya ankara ne ya hankaɗashi gefe. Shi kuma harbin ya same shi a ciki!. *Unguwar Madallah, Suleja, Niger State* RABI'A POV. _🎶Bari ki ji, ki zauna_ _Batun so na zana_ _in zanyi batun ƙauna, za ki shigo labarina_ _Na zaga duniya_ _Ko wacce nahiya, na zamma jan wuya, amma kin saita ni da ƙauna🎶..._ Waƙar Idan babu ke, wadda Umar Mb ya rera ce ke tashi ta cikin wayar Anti Saratu, wadda ke kwance ta na sauraren waƙar, yayin da take daddana wayarta. Daga can gefe kuma Rabi ce ke gogewa kayanta, Fatima kuma na daga ɗayan ɓarin tana tsifar kai, daga cikin ɗakin Habiba kuma, Mahmud ne kwance yana bacci, yayin da ita kuma Habiban ke bakin ƙofar ɗakin, ta na kaɗa wani abu a cikin kofi. Ɗaya daga cikin magungunan da Malamin yayarta ya bata ne, kuma yace a haɗa da madara, ta sa an siyo mata madarar, shi ne yanzu take haɗawa, zuciyarta cike da fatan kasancewar abin da take fata. “Anti Saratu Yaya yace min jiya an yi wasa” Cewar Rabi, tana motsa iron a kan kayanta. Daga kan katifa, Anti Saratu ta ɗan kallota sannan tace. “Ko na baki ki je ki turo ?” Da sauri ta gyaɗa mata kai. Anti Saratu na murmushi ta miƙe zaune, sannan ta kashe waƙar ta miƙa mata wayar. “Dan Allah ki ce masa nima ya saka min sabbabin fina-finan indian hausa guda uku... Nawa zan bada ?” Rabi'a na saka hijabi ta yi dariya. Kullum idan za ta je turi shagon Yaya Sai Anti Saratu tace za ta biya kuɗi, shi kuma baya fasa cewa ba zai karɓa ba. Ta karɓi wayar tana faɗin. “Ni na gaji da garan bawul ɗin da kuke da ni, nasan cewa zai yi an yafe miki, dan haka ki bar kayanki” Anti Saratu ta yi murmushi tana kwanciya. “An ji asara dai, daga bin maza sai kallon wasan maza, mtswww!” Cewar Fatima tana makowa Rabi harara, Rabi'a ta juyo ta kalleta, du-du-du a shekaru Fatiman ba za ta wuce 14 ba, amma yanda take mata rashin kunya kai kace sa'arta ce. “Fatima! Ba na hanaki yin wannan rashin kunyar ba? Ko Rabi'a sa'arki ce?...” Rabi'a ba ta tsaya ta gama jin faɗan da Antu Saratu ta fara ba ta kaɗa kanta ta fita. Tana saka takalmi suka haɗa ido da Habiba. Ba tare da sanin daliliba ta ji gabanta ya faɗi. Saurin dafe ƙirjinta ta yi tana karanto duk addu'ar da ta zo giftawa ta tunaninta. Ta ƙarasa saka takalmin, sannan ta kama hanyar fita. “Ke Rabi! Zo nan!” Kamar daga sama muryar Habiba ta katseta, hakan yasa ta tsaya da tafiyar, gabanta ya ci gaba da bugu. Tsoro ya mamaye mata ruhi. Da ƙyar ta iya juyowa ta kalleta. Suka haɗa ido, ba shiri gabanta ya ƙara tsnanta bugu. Haka kawai ta ji ba ta yarda da wannan kiran da ta mata ba, ta haɗiye wani kakkauran miyau, sannan ta soma takowa zuwa gareta. Kusa da ƙofar ɗakin ta tsugunna. “Ungo shanye!” Habiba ta faɗa tana miƙo mata wani abu a kofi, kallon abun dake cikin kofin kaɗai ya haddasawa Rabi faɗuwar gaba fiye da ta da. Ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112