Skip to content

Chapter 43

Chapter 43

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

POV. Tsaye yake a harabar wani wurin saida motoci, yayin da ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin ke ta nuna masa kalar motocin da suke da su a wurin. “Wannan fa?” Ya faɗi a yayin da ya nuna wata Audi RSQ. Ma'aikacin ya kalleshi. “Ranka ya daɗe wannan fa tana da tsada sosai” Nan take Kuliya ya hango kansa a cikin zuciyarsa yana kashe sauraye a fuskar mutumin. Kuma ba tare da wani tunani ba yace. “Ka ga na maka kama da wanda ba zai iya siyan motar ba ne ko me ?” “Haƙuri ranka ya daɗe, ba haka nake nufi ba...” Kuliya ya masa baza ya juya ya nufi hanyar fita, da gudu mutumin ya bi bayansa yana bashi haƙuri, amma haka ya ƙi ko kallonsa bare ya amsa, ya riga ya yi zuciya, ba zai siyi mota a wurinsu ba. Haka ya fita daga wurin, ya nufi wani wurin da ban, a inda ya je ɗin ne ya siyi wata baƙar Honda Breeze. Sannan kai tsaye ya wuce wurin aiki. Ƙarfe biyu dot, ya tashi don ya je ya ɗauko Mishal, ba wai don lokacin tashin aikinsa ya yi ba, sai don yasan babu wanda zai ɗauko ta idan ba shi ba, shi ɗin da a yanzu yake amsa sunan mijinta!. A harabar makarantar ya yi parking, ya na raba idonsa a kan ɗaliban dake ta tunkuɗowa daga cikin makarantar. Ya kwashe kusan minti goma zaune cikin motar, kafin ya hangota tana tafiya ita da wasu mutum biyu, be damu da kallon waɗanda take tare da su ba, tun da Allah ya sa ya ganta ai shikenan. Ya san ba gane shi za ta yi ba, tun da ba waccan motar da ya kawota ba ce, shi yasa ya fito daga cikin motar, ya fara takawa zuwa wurin da suke. Zuwa lokacin ɗayar ta tafi, saura su biyu. A tare Rabi da Mishal dabkuma Angelica suka fito daga cikin makatarantar, kafin Angelica ta musu sallama ta tafi, suna tafiyar ne kuma suka ga mutum tsaye a gabansu. Kusan a lokaci guda suka kalleshi, gaban Rabi ne ya yi wata mummunar bugawa, ganin wani mutum, wani sak... sak Raja, nan take ƙwaƙwalwarta ta wasto mata hoton ranar da ta tsinci wallet ɗinsa, har ta buɗe taga hotonsu su biyu, tabbas wannan ɗan uwansa ne, ɗan uwansa dake matuƙar kama da ita da kuma shi Rajan kansa. Mishal kuwa kallonsa ta shiga yi, daga ta kalli Rabi, sai shi ma ta kalleshi, sai a lokacin ya kalli wadda suke tare. Allah ne kaɗai yasan cikin wani irin shock ya shiga, wata fuska yake gani, wadda zai iya cewa ta Mommansa ce, fuskar sak ta Zaid ɗinsa, Zaid ɗin da ya rabu da shi na tsayon shekaru masu tarin yawa, wannan fuskar da kammaninta ke kwance a kan tasa fuskar. Ƙwaƙwalwarsa ce ta hautsina, sannan ta kuma hautsunawa, tunaninsa ya birkice, ya kasa gane shin mafarki yake, ko kuma zahiri ne?. Bakinsa yana rawa ya kalleta tun daga sama har ƙasa. Zuciyarsa na bugawa da sauri. “Ka santa ne?” Mishal ta faɗi tana dubansa, me makon ya bata amsa, sai ya kalleta kawai, sannan ya haɗiye duk wani mamakin da yake ciki, ya ɗaga kafaɗarasa ta dama. “Zo mu tafi!” Allahu ƙadirun ala man ya sha'u, hatta da muryarsa sak irin ta Raja ce, sai dai akwai wani abu ɗaya da ya banbanta muryoyin nasu; muryar Raja na fita cikin sanyi da taushi ne, ta wannan kuwa ba ta da wannan sanyin, sanna babu innocent a cikin muryarsa. Da sauri ya juya ya nufi motarsa, ba tare da ya jira Mishal ɗin ba. “Seesee kin san shi ne?” Mishal ta tambaya tana kallon Rabi'a, wadda ta bi bayan Kuliya da kallo. “Ba shi na sani ba, wani ne da ban!... Ki je ya na jiranki” Cewar Rabi'a, bayan da ta gama tabbatar da cewa duk yanda aka yi wannan me kama da Rajan shi ne mijin Mishal ɗin. Ba tare da Mishal ta ce komai a kan maganar Rabi ta farko ba, ta gyaɗa mata kai, tare da mata sallama ta nufi motar ta shiga, kuma ba jira Kuliya ya figi motar a guje kamar yanda ya saba, suka bar cikin makarantar. Kamar yanda Mishal ta saba ganinsa haka yau ma ta ganshi, jingine jikin gate ɗin wannan estate ɗin dake tsalleken makarnatarsu, ba shiri ta juyo ta kalli wanda ke zaune a gefenta, sannan ta juya ta kalli na jikin gate ɗin a lokacin da suka wuce layin. Kanta ya kulle, saboda sau a yau ta gano banbancin da suke da shi, wancan na jikin gate ɗin yana da zaje da kuma ɗan gemu kaɗan, wannan na zaune a gefen nata kuma, ba shi da gemu ko kaɗan, sannan ƙwayar idon wancan gray ce, yayin da wannan tasa take baƙa. To me yake faruwa?, shin su 'yan biyi ne ko me ?, sun san da zaman junansu ?, ta ina suka haɗa alaƙa da Seeseenta?. Gaba ɗaya tambayoyin su ne suka cika kanta fal!, ta kasa banbance fari da baƙi, har hakan ya sa ba ta lura da irin gudun da Kuliya ke shararawa da su ba. Ba ita kaɗai ba ce kanta yake a kulle, hatta da Kuliyan shi ma kansa a kulle yake, ya kasa ganewa abun da yake shirin faruwa, rayuwarsa ta baya da yake ta kokawar mantawa da ita, ita ce ke dawo masa bayan ganin wannan fusakar, wacece ita?, me yasa take kama da su?, a ina Mishal ta santa?, don kayan jikinta ba kalar na 'yan makarantar ba ne, bare yace makarantarsu ce ɗaya. Ya rasa takamemen tunanin da zai kama. Tunaninsa da nutsuwarsa suka sake dugunzuma fiye da da. Ruɗani da cukurkuɗaɗɗun zantunka da tunanika suka yi wa ƙwaƙwalwarsa tsinkaye, ya kasa tantance meke shirin faru, wata ƙaddara ce za ta haɗa shi da wannan yarinyar?, wadda ke ɗauke da kammanin fuskarsa da ta Momma da kuma Zaid. Har suka kai gidan babu wannda ya samu amsa ɗaya daga cikin tarin tambayoyin dake kawunansu, parking ya yi a harabar gidan, kuma kusan a tare suka fito,amma shi ya rigata shiga cikin gidan. Me aikin da ke masa aikin shara da goge-goge ce kawai a gidan, da can ba wai shi takewa aikin ba, 'yar aikin gidan Anna ce, kuma Annan ce ta sakata ta riƙa zuwa gidan nasa duk sati tana masa shara. Kuma shi kullum ba ya dawowa gidan sai bayan sallahr isha'i, ha kan ya da ko kalarta bai sani ba sai yau. Ita ma a ruɗe ta shiga dubansu su duka, don ba ta taɓa ganinsa ba sai yau, kullum haka za ta zo ta yi aikinta ta fi, ko a gidan Amman ba haɗuwa suke ba, yau kuma sai ga shi ya dawo gidan a lokacin da ba ta taɓa zata ba, kuma ba shi kaɗai ya dawo ba, harda wata yarinya tare da shi. Mishal ta kalli matar a sanda take gaisheta, amsawa ta yi tana maida mata martanin gaisuwar, hanyar corridor ta kama, amma sai muryarsa ta dakatar da ita. “Zan koma wajen aiki, anjima kaɗan za'a kawo miki abinci...” Daga haka ya juya ya fice, Mishal ta bi bayansa da kallo. Ba tare da tace komai ba,

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112