Chapter 73
Chapter 73
fili ga me doki, sukuwa kawai ta rage, kuma Allah ya bata sa'a, amma ita da Mishal kam ko a lahira!. *No.181, Guzape, Abuja...* *07:55 PM.* YUSHAL POV.(ALIYU & MISHAL) “Ga shi” Muryar Kuliya ta faɗi, a sanda yake miƙawa Mishal wani ɗan ƙaramin bowl dake ɗauke da yankakkakiyar albasa. Rai a cunkune Mishal ta kai hannu ta karɓa, sannan ta juya kan stove, ta buɗe murfin tukunyar da take dafa jallof ɗin shinkafa, ta zuba albasar, sannan ta rufe murfin tukunyar. Ta ajiye bowl ɗin ta shiga wanke hannunta a sink. Kuliya ya ci gaba da kallonta, ya na nazarin yanayinta, tun bayan da suka yi wannan faɗan da Jadda bata dawo dai-dai ba, kuma saboda ya san ta na cikin yanayin damuwar ne ya sa shi dawowa gida da wuri. Amma duk da haka sai ya isketa cikin damuwar. Ko bayan da ta gama wankewa hannunta, sai ta ci gaba da tsayuwa a jikin sink ɗin, ta shiga karanta wasiƙar jakin da ba ta da ranar ƙarewa. A hankali Kuliya ya isa bayanta, sannan ya saka hannaynesa ya kewaye waist ɗinta, ya janyota baya, tare da mannata da jikinsa. Mishal ta rintse idonta, saboda da wannan sanyin da ya fara shiga kowace ƙofa ta gashi a cikin jikinta. “Me yake damunki?” Sai ta buɗe idonta, ta soma kallon garden ɗin gidan ta windown dake kusa da sink ɗin, amma bata ce masa komai ba. A hankali Kuliya ya sunkuyo da kansa zuwa kafaɗarta, sannan ya manna mata peck a wuya, wanda ya sa ba shiri ta damƙe bakin sink ɗin. “Me yake damunki?” Ya tambaya wannan karon a cikin kunnuwanta, kuma murya ƙasa-ƙasa, wadda ta sa Mishal saurin juyawa a cikin hannayensa tana kallonsa. Hannayenta a kan kafaɗunsa, idonta a kan kyakkyawar fuskarsa. Peck ya mata a goshinta, hakan ya sa ta lumshe idonta. “Me yake damunki?” Ya kuma tambaya a karo na uku, yayin da goshinsa ke kare da nata, hancinsa a kan nata. Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta fara hawaye, da sauri ya zare hannayensa daga jikinta ya dawo da su kan fuskarta ya na share mata su. “Ba ki yarda da ni ba ne ?” Da sauri ta girgiza kanta. “Na yarda da kai sosai, wata ƙila ma sama da yanda na yarda da kaina, ina cikin damuwa saboda rashin ganin Yayata, yau ma fa ba ta zo ba, jikina na bani cewar ta na cikin matsala” Kuliya ya girgiza mata kai ya na cije laɓensa na ƙa. Tare da share mata wata ƙwallar dake bin fuskarta, ashe kenan hasashensa bai zama gaskiya ba, ba abun da suka yi da Jadda ba ne a ranta, damuwar Rabi ce a ran nata. “Insha-Allah ta na cikin hali me kyau, ki kyautata mata zato, da yardar Allah zan nemo miki ita, wannan alƙawari na ne” “Ka min alƙawari?” Ta tambaya muryarta a raunane. Kuliya ya gyaɗa mata kai ya na ci gaba da share mata hawayen, kwanciya ta yi a jikinsa tana sakin wani kukan, Kuliya ya gyara mata riƙo a cikin jikinsa. “Ki na so mu yi faɗa?” Ta girgiza kanta, hakan ya sa jikinsa motsawa, saboda kanta dake kwance a ƙirjinsa. Ya ɗaga kafaɗa yana faɗin. “To ki dena kuka... Ke fa kina da ƙarfin zuciya, you are so strong Teddy Bear, so don't cry!” Sai ta gyaɗa masa kai. Sautin tafasar tukunya ne ya ankarar da su girkin da suke, don dukansu sun ma manta da girkin. Hakan ya sa da sauri Mishal ta fice daga jikinsa ta koma jikin stove ɗin. Shi kuma ya koma ya zauna a kan kujera ya na kallonta. *Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja* RAJA POV. Zaune yake a kan kujerar dake kallon gadon marasa lafiya na ɗakin da aka kwantar da Rabi'a. Bayansa jingine da jikin kujerar, yayin da ƙarfen da aka saƙala drip ɗin da aka saka masa yake aje a gefensa, hannunsa na dama juma saƙale da allurar dake aika drip ɗin zuwa cikin jikinsa, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Rabi'ar dake kwance akan gadon. A ɗazun suma ya yi, har sai da aka ƙaramasa ruwa, kuma ya na farkawa ya fito daga ɗakin da aka kwantar da shi, ya dawo nan ya zauna. A hankali wata ƙwalla ta gangaro daga idonsa, bayan da ya tuna irin gararin rayuwar da take ciki, yanzu kuma ga wani baƙin tabo me matuƙar muni ta ƙara samu. Amma alƙawari ya yi wa kansa, na babu abun da zai hana shi aurenta, ko da sama da ƙasa za su haɗe, ko da duniyar ce za ta tashi, ko da kuwa aurenta shi ne abu na ƙarshe da zai yi a duniyar nan, ba fyaɗ... Kasa ƙarasa kalmar ya yi a ransa, don haka kawai ya tsalleketa ya tafi tunaninsa na gaba; ko da cuta me karya garkuwar jiki ce tare da ita, ba zata hanashi aurenta ba, wani kalar so yake mata da ya wuce soyyaya kawai, sai dai soyyayar haɗuwar jini, kasancewarta ɗaya daga cikin ahalinsa shi ne ya ƙara ninka soyyayarta a ransa. Ganin ruwan da aka saka masa ya ƙare yasa ya kai hannunsa ya cire allurar, sannan ya manne wurin da plaster, saboda kada jini ya zubo, miƙewa ya yi, duk da ya na jin jikinsa babu ƙwari, amma haka ya taka a daddafe har ya isa jikin gadon da Rabi'a ke kwance kamar gawa. Zama ya yi a gefen gadon ya na kallon fuskarta, sannan ya kamo hannunta na dama, wanda ke saƙale da clip na wata na'ura dake jikinta, hannunsa ya saka cikin nata ya damƙe, dubansa ya dawo kan fuskarta. Wadda a yanzu ta sauya suffa daga tata ta da, sakamakon wani yanka dake gefen fuskarta na hagu. Ɗinkin da ya ga an yiwa raunin ya sa ya fahimci girmansa, ga kuma yanda fuskarta ta ɗan tattare daga gefen hagun, saboda yankan da aka mata, amma duk da haka kammanin fuskarta ba su sauya ba. Sai kuma gashin kanta da ya lura da kamar sun rage masa tsayi, duk da shi bai taɓa ganin gashinta ba, amma ya yana da yaƙinin cewa gashin kan nata ba haka yake ba, kuma ya fahimci kamar saboda raunukan dake kanta aka rage yawan gashin. Idanuwanta a rufe, fatar bakinta ta yi fari sol, a kallo ɗaya idan ka mata sai ka ce maccacciya ce, shi kansa ba don Huzaifa ya tabbatar masa da tana raye ba da ba zai yarda da tana da ran ba. Jikinta sanye yake da rigar asibitin, wadda take blue colour, sai farin bargon asibitin da aka rufa mata a rabin jikinta. Ya tuna yanayin murmushinta, ya tuna sanyin maganarta, ya tuna nutsuwarta, ya tuna hankalinta, ya tuna yanda take kallonsa da idanuwanta masu kama da na Aliyu, ya tuna komai a kanta, hatta da ranar da ya fara ganinta sai da ya tuna. Idonsa ya rintse a sanda hoton file ɗinta da ya buɗe a ɗazu ya dawo masa cikin tunani, wai mutum biyar ko sama da haka ne suka mata fyaɗe, sannan bayan haka ma harda raunikan a jikinta, ga kuma dukan kanta da aka yi, wanda shi ne maƙasudin shigarta doguwar suma. A hankali ya buɗe idanunsa nasa, wanda ya yi ja kamar sabon
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112