Chapter 47
Chapter 47
kuma Jadda a nata ɓangaren, da alama ita ma za'a fafata da ita_ _Ga kuma Uncle Kuliya a gefe, kada fa kumanta da ya ga Rabi'a, wani ya faɗa min meke shirin faruwa..._ #Labarinsu #SalmaAhmadIsah #TaurariWriters ••••••••••••••• *LABARINSU* *©SALMA AHMAD ISAH* *TAURARI WRITERS* *12* ~~~ _-*I think the most beautiful thing you could ever experienced is finding someone who wants your all, even if your all is a mess*-_ *** Follow my Wattpad account 👇 https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends *DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja* KULIYA POV. “Wannan shi ne file ɗin next assignment ɗinka!...” Cewar Chidera, a sa'ilin da yake miƙa masa file ɗin aikin da ya kamata a ce ya aiwatar a gaba. A karo na farko tun bayan fara aikinsa, Kuliya ya ji wani abu me kama da tsoro ya kama shi a kan aikin, tun da yake bai taɓa ja da baya a kan ko wani aikin da ya sa ƙafa ba, bai san tsoro ko koma ba ya kan aikinsa ba, amma a yau sai ga shi ya na jin ɗar-ɗar na karɓarsa sabon assignment. A da shi da kansa yake neman assignment ko ba'a ba shi ba, ko ya karɓi na wani ya ƙarsa, amma a yau sai ya ke jin kamar ba zai iya ba, kuma tsoron da yake ba na komai ba ne, sai na gudun kada wani abu ya zo ya faru da makusantansa. A da sam ba shi da kalar wannan tsoron, ko da rayuwarsa zai salwantar zai a kan aiki sai ya karɓa, bai damu da kowa ba dan ba shi da kowan da ya wuce Anna, tun da ya mallaki hankalinsa be san ya raɗaɗin zafin rasa makusanci yake ba, sai bayan da Abubakar ya mutu ta dalilinsa. Kamar me shirin karɓar zunubansa haka ya kai hannu ya karɓi file ɗin, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga sannan ya kalli Chideran da ya fara masa bayani a kan aikin. “Case ne a kan kisa da kuma fyaɗen da aka ma wata yarinya a Life Camp” _“Dama na san wata rana dole za ku so ku san waye mahaifinku... A zahirin gaskiya Aliyu da Zaid ban san mahaifinku ba. An gayyace ni zuwa wurin bikin wata ƙawarmu ne.... Kuma a wurin aka zuba min abun gusar da hayyaci a cikin abun shana. Har aka samu wani ya haike min!. Kuma a lokacin ne na samu cikinku!...”_ Kalaman mahaifiyarsu kenan garesu, a ranar da Zaid ya tambayeta labarin mahafinsu, kuma tun bayan lokacin ya tsani wannan kalmar ta fyaɗe, a duk sanda zai jita, sai ya ji kamar an watsa masa maɗaci a kan zuciyarsa, ko da wasa ba ya son sauraron kalmar. Don shi ko aiki aka ba shi wanda ya danganci fyaɗe hukuncin da yakewa me laifin ma da ban ne. A hankali ya gyaɗa kansa ya ba buɗe file ɗin. * Sharon, Kamis, Sani, Mubarak da Symon su ne zaune kan kujeru, yayin da suka kasa kunne suna sauraronsa. “...Gaba ɗaya akwai tarin bayanai game da kisan, akwai hujjojin da 'yan sanda suka samo a wurin da aka yi kisan. Na farko, wuƙar da aka yi amfani da ita wurin kisan. Wuƙar na ɗauke da jinin victim ɗin, sannan akwai shatin yatsun me lefin a jiki. Hujja ta biyu kuma ita ce; autopsy report, bayanan da likitan da ya bincika gawar ya bayar sune; farko sai da aka mata...” Kamar kullum, yau ma sai da ya tauna maganar kafin ya faɗeta, kallonsu ya yi gaba ɗaya, amma su ba shi suke kallo ba, ko wanne a cikinsu da takardar da yake dubawa, wadda ta ƙunshi bayanan case ɗin, hakan ya ba shi damar yin gyaran murya, ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba. “...Fyaɗe, kafin ya kasheta, kamar yanda na faɗa muku tun farko, ya yi amfani da wuƙa ne wurin yanka wuyanta, sannan kuma rahoton ya bayyana cewa makashin ba hagume ne, ma'ana yana amfani da hannun hagu!” “Amma ni sai nake ganin... Kamar waɗanan hujjojjin ba su isa susa mu gano wanda ake zargi ba, muna buƙatar ƙarin wasu hujjojjin” Cewar Sani, bayan da Kuliyan ya gam zayyano musu kaf bayanan cikin file ɗin. A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa ya na kurɓar coffen dake hannunsa. “Kai ma ka ce wani abu” “So what are we gonna do next?” Sharon ta tambaya. “Zan yi magan da Ram, sannan zan yi magan da ɗansandan da ya kula da case ɗin kafin ya zo nan, na san za'a iya samun wasu bayanan” Kuliya ya bata amsa. “Amma ya kamata mu yi magana da iyayen yarinyar” Cewar Kamis yana aje takardar hannunsa. “Ƙwarai wannan ma babbar makamace, wata ƙila za su iya bamu wani hint” “But babu wani wanda zargi ya hau kansa?, i mean ko da ɗaya daga cikin mutanen gidansu ita yarinyar ne?” Cewar Symon. “A bayanan cikin file ɗin dai babu, amma idan muka nitsa cikin binciken ba za mu rasa ba” Kuliya ya amsa masa yana sosa kansa. “Gaskiya makashin nan ba shi da imani, kalli yanda aka yanka wuyan yarinyar, kuma a profile ɗin yarinyar na ga ba ta wuci 18 years ba” Cewar Mubarak, sanda yake kallon hotunan da aka wa gawar. Sai da Kuliya ya ɗan yi jim, tunowa da ita da ya yi, ita ɗin da a yanzu zai iya kira da matarsa, ita ɗin da zai iya cewa zuciyarsa ta raurawa a kanta, ita ɗin da ta zama sanadiyyar haɗuwarsa da wata wanda yake ganin kamar ta jiɓanci rayuwarsa ta baya. Haka dai suka yi ta tattaunawa a kan case ɗin, kafin kowa ya tashi ya fita, ya rage daga Kuliya sai Sharon, wadda suke ƙara tattaunawa kan yanda za su ɓullowa batun. “Ya kwanan amarya?” Sharon ɗin ta faɗi tana harhaɗa kan papers ɗin da suka barbaza, sai da Kuliya ya ɗan kalleta, sannan ya amsa mata da. “Tana lafiya” Sharon ta ɗan yi murmushi tana rufe file ɗin dabta gama haɗawa. “Na san yarinyar, ba ta da wasu shekaru masu yawa, na san ba lalle ma a ce tasan menene ɗaukar nauyin miji da na gida ba... Amma idan ka daure, ka yi haƙuri komai zai zo maka da sauƙi, ka yi ta ɗorata a kan hanya, za ta dawo dai-dai. hmmm?” Sai ya aje mug ɗin hannunsa ya na gyaɗa mata kai, kaf abokansa ita ce mutum ta biyu da yake iya sauraron maganarta. “Thanks for the advice” “Not at all” Ta faɗi da wani guntun murmushi a kan fuskarta, ta haɗa abin da za ta haɗa ta fice daga office ɗin. Kuliya ya shafo kansa yana fitar da iska daga bakisa. Da alama wannan assignment ɗin zafin kai kawai zai ƙara masa, bayan wani ɗumin da kan nasa ya ɗauka. *Unguwar Madalla, Suleja, Niger state* RABI'A POV. “To yanzu Rabi gurin wa zan tura su?” Cewar Antu Saratu, bayan da saurayinta Fu'ad ya zo zance ya shaida mata da ya kamata ta sa masa ranar da zai turo magabatansa. Yayin da suke zaune ne a ɗakinsu, kan katifar Anti Saratun. Rabi ta ɗan yi shiru tana nazari, can kuma tace. “To me zai hana ki turasu wurin kawu Habu, ki ga shi ne kawai wanda za'a iya nemar aurenki a wurinsa” “Kuma fa haka ne, kai amma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112