Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Labarinsu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

siyo miki, ba inda za su fita” Habiba ta faɗi a dake. Saratu ta sunkuya tana kallon Rabi'a cikin murmushi, da ido kawai ta mata alamu da ta tafi. Rabi ta miƙe har da murmushinta ta fita, dan dama da hijabinta a jikinta. “Mama ta shi ki ƙarasa suyar nan...” “Wallahi Umma ba zan iya ba, ga Saratu nan, sai ki sa ta ta soya” “Eh kuma haka ne, Saratu, tun da kin tashi ita me suyar, ke sai ki ƙarasa” Saratu ba ta ce mata komai ba, ta girgiza kanta tana takaicin halin mahaifiyar tasu da ƙanwarta, ta zauna ta ci gaba da suyar. “Na yi zaton ba za ki fito ɗin ba ai...” Sassanyar muryar Yaya ta faɗi, yayin da yake kallon fuskar Rabi'a. Ta ɗan yi murmushi kaɗan tana sinnekai. “Umma ce ta sa ni aiki, shi yasa” Ya langwaɓe kai gefe yana faɗin. “Allah ya bani kuɗin da zan aureki Rabi'ata, dan na gaji da ganinki kina wahala a banza, Gwara na aureki ki je can gidana ki yi bautar me lada!...” Ƙwalla ta taru a idon Rabi'a, amma sai ta shanyeta, don ko kaɗan bata so ta zubo. “Gobe sallah, me kika tana da min ?” Ta ƙara sunkuyar da kanta. Warin wannan bolar na cika hancinta, don Allah ya sani bata san zama a ƙofar gidansu. “Babu komai” “Na sani ai, shi yasa ni na samu na ɗan ɗinka miki kala ɗaya da hijabi, ki yi haƙuri ba yawa Honeyna!” Abubuwa biyu ne suka karya zuciyar Rabi'a lokaci guda, ɗinkin da yace ya mata, da kuma sunan Honeynsa da ya kirata da shi, wannan ƙwallar da take ta ƙoƙarin riƙeta ta sauƙo mata. Ta ɗago da kanta ta kalli fuskar Yayan, sannan ta kalli kedar da yake miƙa mata. * Tsabar murnar samun sabon kayan da take ranar kasa bacci ta yi, daga ta ɗan jima a kwance sai ta miƙe zaune ta janyo ledar kayan ta duba su, ta kuma mayar wa. Allah ne kaɗai yasan yanda ta yi farin cikin samun kayan, shi yasa a har kullum take taya Yayyan da addu'a kan Allah ya buɗa masa, har ya samu kuɗin da zai kawo a aura masa ita. Duk lalacewr auren yafi zaman gidansu. “Ka zo?!...” Kamar daga sama ta ji muryar Mama, hakan yasa ta buɗe idonta dake a lumshe, ta cikin net ɗinta ta hangi fuskar Maman, wadda ta yi kwalliya a cikin daren Allah ta ala. Wasu tsukakkun riga da wando ne a jikinta, ga kitson attachment ɗin da takanas ta tashi ta je aka mata shi, ta zube shi a bayanta, ta caɓa wata uw*r kwalliaya, kamar me shirin zuwa gidan bikin, gidan bikin ma irin na kece rainin nan. “Ka ɗan ƙara matsawa gaba... kasan ni bana san sa ido, kar ka ga dare ya tsala, akwai munafukai masu bacci da ido ɗaya” Ta kuma faɗi ta cikin wayar da take. “Ok to bari na fito...” Kuma daga haka Maman ta sauƙe wayar da ke riƙe a hannunta, ta gyagyyara jikinta, sannan ta kashe wutar ɗakin ta fita. Rabi ta ƙara dunƙuƙunewa a cikin bargonta, don bata ma so Maman ta san cewa ta farka. Abin da ake zarginta da shi, shi ne 'yar mai zargin nata ke yi. *No.181, Guzape, Abuja....* *10:00pm* KULIYA POV. A hankali ƙafafunsa suka taka cikin falon gidan. Abu na farko da ya yi shi ne kunna wutar gidan gaba ɗaya. Kafin ya ƙaraso cikin falon, ya sauƙe ledojin da ya shigo da sua kan sofa. Sabbin kayan da ya siya zai saka idan zai je idi. Kuma kafin ya taho gidan nasa sai da ya biya ta gidan Anna, ya kai mata nata kayan idin. Sai ledar da Annan ta saka masa abinci a ciki, don haka tace yana buƙatar ya riƙa cin abincin gida, ba na kanti ba. Kuma haka ɗin ne, bayan farin ruwan sanyi da ya sha a office lokacin da aka yi buɗa baki bai saka komai a cikinsa ba. Dan shi ba iya girka abinci ya yi ba, idan har ba gidan Annan ya je ba to sai dai ya yi order a wani restaurant da ya saba siyan abinci. Idan kuma aiki ya sha masa kaibama ya samun damar cin abincin. Dan bai damu da shi ba, shi yasa ulcer tai masa kamun kazar kuku. “Ayra!, Ayra!....” Muryarsa ta shiga kiran sunan a hankali, kamar ba shi ba, yana yi yana dudduba ƙasan kujeru. Da gudu kuliyar tasa ta fito daga ƙasan wata kujera, sannan ta iyo kansa. Wata hallita ɗaya a duniya bayan Anna da take iya ganin farin haƙorinsa cikin murmushi ko dariya. Shi kansa yaan cewa ba kasafai yake murmushi ba ma balle a je ga dariya. Murmushin ma baya yi sai idan ya yi nasara a aikinsa. A ƙasa ya zauna, sannan ya kamo kuliyar tasa yana shafa kanta. “Kina jin yinwa ko ?” Ya tambaya kamar yana magana da mutum, don shi ɗaukarta yake kamar ƙawa, saboda bayan me gadin gidan, sai wata tsohuwa dake zuwa tana masa shara a gidan duk sati, babu wani abu mai rai dake rayuwa a gidan sai ita. Ledar da Annan ta saka masa abinci ya janyo, sannan ya fiddo da abincin da Annan ta zuba masa. Ya buɗe flask ɗin, ya zubawa Kuliyarq a murfin flask ɗin, ya tura mata gabanta, nan take ta hau ci. Shi ma gefe ya koma ya zauna ya fara cin nasa abincin. Yana tunanin yanda ayyuka za su masa yawa a satin nan, dan abokinsa kuma abokin aikinsa ya ɗauki hutun bikin sallah. Saboda haka duka ayyukan Abubakar ɗin shi ne zai ƙarasa. A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Yana kai lomar abincin bakinsa, idonsa a kan Ayra, yadda take ta famar cin abincin ne kaɗai zai nuna maka cewar a matse take da abincin. Bayan sun gama cin abincin, ya ɗauki Ayra tare da ɗorata a kan kafaɗarsa, sannan ya ɗauki sauran kayan nasa na ledar, ya shiga ɗakinsa. A kan gado ya zube ledojin, kafin ya aje Ayra kusa da ledojin, Ya juya zuwa walk-in closet ɗinsa. Bayan ɗan wani lokaci ya fito, ya shiga banɗaki. Wanka ya yi, ya fito bayan ya sauya kaya. Daga suit ɗin da ya shigo da ita zuwa wasu baƙaƙen shirt da wando na pyjams. Ya dawo ya zauna a kan gadon yana fitar da kayan idin nasa. Kamar yanda ya saba duk shekara, baƙar shaddace guda ɗaya, sai wani baƙin voil, hulunan ma baƙaƙe ne babu ratsin wata kala ko guda a jikinsu. Haka takalman ma baƙaƙe ne guda biyu, dan shi ba wasu manyan kaya yake sawa ba, sai lokaci irin wannan idan ya zo, hatta da sallar juma'a ba da manyan kaya yake zuwa ba. Miƙewa ya yi ya koma closet ɗin. Wani abun mamaki shi ne, gaba ɗaya kayan cikin closet ɗin baƙaƙe ne, kamar na mai shirin zuwa jana'iza. A rayuwarsa ba ya saka wani kaya mai kala, duka kayansa a duniya baƙi ne, motarsa baƙa, kayan sakawarsa baƙaƙe, hatta da case ɗin wayarsa baƙi ne. Bayan ya aje kayan, ya fito ya zauna a kan work table ɗinsa, ya shiga yin sauran aikin da ya dawo gida da shi. *Dambuwa road, Maiduguri...*

Table of Contents

Chapters

112 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112